Skip to content

Ayyukan Manzanni 2

.

Zuwan Ruhu Mai Tsarki
1  Da ranar Fentikos ta yi, duk suna tare a wuri ɗaya, 2farat ɗaya, sai aka ji wani amo daga sama, kamar na busowar gawurtacciyar iska, ya cika duk gidan da suke zaune. 3Sai waɗansu harsuna kamar na wuta suka bayyana a gare su, suna rarrabuwa, suna sassauka a kan ko wannensu. 4Sai duk, aka cika su da Ruhu Mai Tsarki, suka kuma fara magana da waɗansu harsuna dabam dabam, gwargwadon yadda Ruhun ya yi musu baiwar yin magana.
5To, a Urushalima a lokacin, akwai waɗansu Yahudawa masu bautar Allah daga ko’ina cikin ƙasashen duniya. 6Da jin dirin nan kuwa, taron ya haɗe, ya ruɗe, domin ko wannensu ya ji suna magana da bakin garinsu. 7Sai suka yi al’ajabi suka yi mamaki, suna cewa, “Ashe, duk masu maganar nan ba Galilawa ba ne? 8Ƙaƙa kuwa ko wannenmu yake ji da bakin garinsu ake magana? 9Ga mu kuwa, Fartiyawa, da Madayanawa, da Elamawa, da mutanen ƙasar Bagadaza, da na Yahudiya, da na Kafadokiya, da na Fantas, da na Asiya, 10da na Firijiya, da na Bamfiliya, da na Masar, da kuma na kewayen Kurane ta ƙasar Libiya, har ma da baƙi daga Roma, wato Yahudawa, da kuma waɗanda suka shiga Yahudanci, 11da kuma Karitawa, da Larabawa, duk muna ji suna maganar manyan al’amuran Allah da bakunan garuruwanmu.” 12Duk kuwa suka yi mamaki, suka ruɗe, suna ce wa juna, “Me ke nan kuma?” 13Amma waɗansu suka yi ba’a suka ce, “Ruwan inabi suka sha suka yi tatul!”
Jawabin Bitrus a Ranar Fentikos
14Amma Bitrus ya miƙe tare da sha ɗayan nan, ya ɗaga murya ya yi musu jawabi, ya ce, “Ya ku ‘yan’uwana Yahudawa da dukan mazaunan Urushalima, ku kula da wannan, ku kuma saurari maganata. 15Ai, mutanen nan ba bugaggu ba ne yadda kuke zato, tun da yake yanzu ƙarfe tare na safe ne kawai. 16Wannan, ai, shi ne abin da Annabi Yowel ya faɗa cewa,
17  “ ‘Allah ya ce,
A zamanin karshe zai zamanto zan zubo wa dukan ‘yan adam Ruhuna.
‘Ya’yanku mata da maza za su yi annabci,
Wahayi zai zo wa samarinku,
Dattawanku kuma za su yi mafarkai.
18Hakika, har ma a kwanakin nan zan zubo Ruhuna a kan bayina mata da maza,
Za su kuma yi annabci.
19Zan nuna abubuwan al’ajabi a sararin sama,
Da mu’ujizai a nan ƙasa,
Wato jini, da wuta, da kuma, hauhawan hayaƙi.
20Za a mai da rana duhu,
Wata kuma jini,
Kafin Ranar Ubangiji ta zo,
Babbar ranar nan mai girma.
21A sa’an nan ne zai zamanto kowa ya yi addu’a da sunan Ubangiji zai sami ceto.’
22“Ya ku ‘yan’uwa, Isra’ilawa, ku ji wannan magana. Yesu Banazare, mutumin da Allah ya tabbatar muku cewa shi yardajjensa ne, ta mu’ujizai, da abubuwan al’ajabi, da alamu waɗanda ya yi ta wurinsa a cikinku, kamar yadda ku kanku kuka sani, 23 shi Yesun nan fa, an ba da shi bisa ƙaddarar Allah da rigyasaninsa, ku kuwa kuka gicciye shi, kuka kashe shi, ta hannun masu zunubi. 24 Amma Allah ya tashe shi bayan ya ɓalle masa ƙangin mutuwa, domin ba shi yiwuwa mutuwa ta riƙe shi. 25Dawuda kuma ya yi faɗi a game da shi ya ce,
“ ‘Kullum hankalina yana kan Ubangiji,
Yana damana, domin kada in jijjigu.
26Saboda haka, zuciyata ta yi fari, ina farin ciki matuƙa.
Ko da yake kuma ni jiki ne, zan zauna ina sa zuciya,
27Domin ba za ka yar da raina a Hades ba,
Ba kuwa za ka yarda Mai Tsarkinka ya ruɓa ba.
28Kā sanar da ni hanyoyin rai.
Za ka cika ni da farin ciki ta zamana a zatinka.’
29“Ya ‘yan’uwa, na iya yi muku magana da amincewa a game da kakanmu Dawuda, cewa ya mutu, an binne shi, kabarinsa kuma yana nan gare mu har ya zuwa yau. 30 To, da yake shi annabi ne, ya kuma san Allah ya rantse masa, cewa zai ɗora wani daga cikin zuriya tasa kan kursiyinsa, 31sai ya hango, ya kuma yi faɗi a kan tashin Almasihu daga matattu, cewa ba za a yashe shi a Hades ba, jikinsa kuwa ba zai ruɓa ba. 32Yesun nan kam, Allah ya tashe shi daga matattu, mu kuwa duk shaidu ne ga haka. 33Da yake an ɗaukaka shi a dama ga Allah, ya kuma sami cikar alkawarin nan na baiwar Ruhu Mai Tsarki daga wurin Uba, sai ya zubo da wannan da kuke gani, kuke kuma ji. 34Ai, ba Dawuda ne ya hau Sama ba, amma shi kansa ya ce,
“ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,
Zauna a damana,
35Sai na sa ka take maƙiyanka.’
36“Don haka sai duk jama’ar Isra’ila su sakankance, cewa shi Yesun na da kuka gicciye, Allah ya mai da shi Ubangiji, da kuma Almasihu.”
37To, da suka ji haka, maganar ta soke su a zuci, suka ce wa Bitrus da sauran manzannin, “’Yan’uwa, me za mu yi?” 38Sai Bitrus ya ce musu, “Sai ku tuba, a yi wa ko wannenku baftisma, a kan kun yarda da sunan Yesu Almasihu, domin a gafarta zunubanku, za ku kuwa sami baiwar Ruhu Mai Tsarki, 39domin alkawarin nan ku aka yi wa, ku da ‘ya’yanku, da kuma dukan manisanta, wato duk waɗanda Ubangiji Allahnmu ya kira.” 40Sai ya yi ta tabbatar musu da maganganu masu yawa, yana ta yi musu gargaɗi, yana cewa, “Ku tsirar da kanku daga wannan karkataccen zamani.” 41Waɗanda suka ya na’am da maganarsa kuwa aka yi musu baftisma. A ran nan kuma suka ƙaru da mutum wajen dubu uku. 42Sai suka himmantu ga koyarwar manzanni da tarayya da juna, da gutsuttsura gurasa, da kuma yin addu’a.
Yadda Zaman Masu Bi Yake
43Sai tsoro ya kama kowa, aka kuma yi abubuwan al’ajabi da mu’ujizai da yawa ta wurin manzannin. 44 Dukan masu ba da gaskiya suna tare, suna mallakar kome nasu gaba ɗaya. 45Suka sayar da mallakarsu da kayansu, suka rarraba wa kowa kuɗin, gwargwadon bukatarsa. 46Kowace rana kuma sukan riƙa zuwa Haikali da nufi ɗaya, suna gutsuttsura gurasa a gidajensu, suna cin abinci da farin ciki ƙwarai, rai kwance, 47suna yabon Allah, suna da farin jini a wurin dukan mutane. Kowace rana kuma Ubangiji yana ƙara masu waɗanda ake ceta.

(Ayyukan Manzanni 2 2:1-47)