Skip to content

From Books

A. L̃.R. Waɗancan ãyoyin Littãfi mai bayyanãwa ne.

Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi, yanã abin karantãwa na Lãrabci; tsammãninkũ, kunã hankalta.

Mũ, Munã bãyar da lãbãri a gare ka, mafi kyãwon lãbãri ga abin da Muka yi wahayin wannan Alƙur’ãni zuwa gare ka. Kuma lalle ne kã kasance a gabãninsa, haƙĩƙa, daga gafalallu.

A lõkacin da Yũsufu ya ce wa ubansa, “Yã bãba! Lalle ne nĩ, nã ga taurãri gõma shã ɗaya, da rãnã da watã. Na gan su sunã mãsu sujada a gare ni.”

Ya ce: “Ya ƙaramin ɗãna! Kada ka faɗi mafarkinka ga ‘yan’uwanka, har su ƙulla maka wani kaidi. Lalle ne Shaidan ga mutum, haƙĩƙa, maƙiyi ne bayyanãnne.

“Kuma kãmar wancan ne, Ubangijinka Yake zãɓen ka, kuma Ya sanar da kai daga fassarar lãbãrai, kuma ya cika ni’imõminSa a kanka, kuma a kan gidan Yãƙũba kãmar yadda ya cika su a kan ubanninka biyu, a gabãni, Ibrãhĩm da Is’hãƙa. Lalle Ubangijinka ne Masani, Mai hikima.”

Lalle ne, haƙĩƙa, ãyõyi sun kasance ga Yũsufu da ‘yan’uwansa dõmin mãsu tambaya.

A lõkacin da suka ce: lalle ne Yũsufu da ɗan’uwansa ne mafiya sõyuwa ga ubanmu daga gare mu, alhãli kuwa mũ jama’a guda ne. Lalle ubanmu, haƙĩƙa, yanã cikin ɓata bayyananniya.

Ku kashe Yũsufu, kõ kuwa ku jẽfa shi a wata ƙasa, fuskar ubanku ta wõfinta sabõda ku, kuma ku kasance a bãyansa mutãne sãlihai.

Wani mai magana daga cikinsu ya ce: “Kada ku kashe Yũsufu. Ku jẽfa shi a cikin duhun rĩjiya, wasu matafiya su tsince shi, idan kun kasance mãsu aikatãwa ne.”

Suka ce: “Yã bãbanmu! Mẽne ne a gare ka ba ka amince mana ba a kan Yũsufu, alhãlikuwa lalle ne mũ, haƙãƙa mãsu nashĩha muke a gare shi?”

“Ka bar shi tãre da mu a gõbe, ya ji dãɗi, kuma ya yi wãsa. Kuma lalle ne mu, a gare shi, mãsu tsaro ne.”

Ya ce: “Lalle ne ni, haƙãƙa yanã ɓãta mini rai ku tafii da shi, Kuma inã tsõron kerkẽci ya cinye shi, alhãli ku kuwa kunã mãsu shagala daga gare shi.”

Suka ce: “Haƙĩƙa idan kerkẽci ya cinye shi, alhãli kuwa munã dangin jũna, lalle ne mũ, a sa’an nan, hakĩka, mun zama mãsu hasãra.”

To, a lõkacin da suka tafi da shi, kuma suka yi niyyar su sanya shi a cikin duhun rĩjiya, Muka yi wahayi zuwa gare shi, “Lalle ne, kanã bã su lãbari game da wannan al’amari nãsu, kuma sũ ba su sani ba.”

Kuma suka je wa ubansu da dare sunã kũka.

Suka ce: “Yã bãbanmu! Lalle ne, mun tafi munã tsẽre, kuma muka bar Yusufu a wurin kãyanmu, sai kerkẽci ya cinye shi, kuma kai, bã mai amincẽwa da mu ba ne, kuma kõ dã mun kasance mãsu gaskiya!”_

Kuma suka je, a jikin rigarsa akwai wani jinin ƙarya. Ya ce: “Ã’a, zukatanku suka ƙawãta muku wani al’amari. Sai haƙuri mai kyau! Kuma Allah ne wanda ake nẽman taimako (a gunSa) a kan abin da kuke siffantãwa.”

Kuma wani ãyari ya je, sai suka aika mai nẽman musu rũwa, sai ya zura gugansa, ya ce: “Yã bushãrata! Wannan yãro ne.” Kuma suka ɓõye shi yanã abin sayarwa. Kuma Allah ne Masani ga abin da suke aikatãwa.

Kuma suka sayar da shi da ‘yan kuɗi kaɗan, dirhamõmi ƙidãyayyu, Kuma sun kasance, a wurinsa, daga mãsu isuwa da abu kaɗan.

Kuma wanda ya saye shi daga Masar ya ce wa mãtarsa, “Ki girmama mazauninsa, akwai tsammãnin ya amfãne mu, kõ kuwa mu riƙe shi ɗã.”Kuma kamar wancan ne Muka tabbatar ga Yũsufu, a cikin ƙasa kuma dõmin Mu sanar da shi daia fassarar lũbũru, kuma Allah ne Marinjãyi a kan al’amarinSa, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.”

Kuma a lõkacin da ya isa mafi ƙarfinsa, Muka bã shi hukunci da ilmi. Kuma kamar wancan ne Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

Kuma wadda yake a cikin ɗãkinta, ta nẽme shi ga kansa, kuma ta kukkulle ƙõfõfi, kuma ta ce, “Yã rage a gare ka!” ya ce: “Ina neman tsarin Allah! Lalle shĩne Ubangijina. Yã kyautata mazaunina. Lalle ne shĩ, mãsu zãlunci ba su cin nasara!”

Kuma lalle ne, tã himmantu da shi. Kuma yã himmantu da ita in bã dõmin ya ga dalĩlin Ubangijinsa ba. Kãmar haka dai, dõmin Mu karkatar da mummũnan aiki da alfãsha daga gare shi. Lalle ne shi, daga bãyinMu zaɓaɓɓu yake.

Kuma suka yi tsẽre zuwa ga ƙõfa. Sai ta tsãge rigarsa daga bãya, kuma suka iske mijinta a wurin ƙõfar. Ta ce: “Mẽnene sakamakon wanda ya yi nufin cũta game da iyãlinka? Fãce a ɗaure shi, ko kuwa a yi masa wata azãba mai raɗaɗi.”

Ya ce: “Ita ce ta nẽme ni a kaina.”Kuma wani mai shaida daga mutãnenta ya bãyar da shaida: “Idan rigarsa ta kasance an tsage ta daga gaba, to, tã yi gaskiya, kuma shĩ ne daga maƙaryata.”

“Kuma idan rigarsa ta kasance an tsãge ta daga bãya, to, tã yi ƙarya, kuma shĩ ne daga mãsu gaskiya.”

Sa’an nan a lõkacin da ya ga rĩgarsa an tsãge ta daga bãya, ya ce: “Lalle ne shi, daga kaidinku ne, mata! Lalle ne kaidinku mai girma ne!”

“Yusufu! Ka kau da kai daga wannan. Kuma ki nẽmi gãfara dõmin laifinki. Lalle ne ke, kin kasance daga mãsu kuskure.”

Kuma waɗansu mãtã a cikin Birnin suka ce: “Matar Azĩz tanã nẽman hãdiminta daga kansa! Haƙĩƙa, yã rufe zũciyarta da so. Lalle ne mũ, Munã ganin taa cikin ɓata bayyanãnna.”

Sa’an nan a lõkacin da ta ji lãbãri game da mãkircinsu, sai ta aika kiran liyafa zuwa gare su, kuma ta yi tattalin abincin da ake dõgara wajen cinsa, kuma ta bai wa kõwace ɗaya daga cikinsu wuƙa, kuma ta ce: “Ka fito a kansu.” To, a lõkacin da, suka gan shi, suka girmamã shi, kuma suka yanyanke hannãyensu, kuma suka ce: “Tsarki yanã ga Allah! Wannan bã mutum ba ne! Wannan bai zama ba fãce Malã’ika ne mai daraja!”

Ta ce: “To wannan ne fa wanda kuka, zarge ni a cikinsa! Kuma lalle ne, haƙẽƙa na nẽme shi daga kansa, sai ya tsare gida, kuma nĩ inã rantsuwa, idan bai aikata abin da nake umurnin sa ba, haƙẽƙa anã ɗaure shi. Haƙĩƙa, yanã kasan, cewa daga ƙasƙantattu.”

Ya ce: “Yã Ubangijina! Kurkuku ne mafi sõyuwa a gare ni daga abin da suke kirã na zuwa gare shi. Kuma idan ba Ka karkatar da kaidinsu daga gare ni ba, zan karkata zuwa gare su, kuma in kasance daga jãhilai.”

Sai Ubangijinsa Ya karɓa masa sabõda haka Ya karkatar da kaidinsu daga gare shi. Lalle Shĩ ne Mai jĩ, Masani.

Sa’an nan kuma ya bayyana a gare su a bãyan sun ga alãmõmin, lalle ne dai su ɗaure shi har zuwa wani lõkaci.

Kuma waɗansu samãri biyu suka shiga kurkuku tãre da shi. ¦ayansu ya ce: “Lalle ne nĩ, nã yi mafarkin gã ni inã mãtsar giya.” Kuma ɗayan ya ce: “Lalle ne nĩ, nã yi Mafarkin gã ni inã ɗauke da waina a bisa kaina, tsuntsãye sunã ci daga gare ta. Ka bã mu lãbãri game da fassararsu. Lalle ne mũ, Munã ganin ka daga mãsu kyautatãwa.”

Ya ce: “Wani abinci bã zai zo muku ba wanda ake azurtã ku da shi fãce nã bã ku lãbãrin fassararsa, kãfin ya zo muku. Wannan kuwa yanã daga abin da Ubangijĩna Ya sanar da ni. Lalle ne nĩ nã bar addinin mutãne waɗanda ba su yi ĩmãni da Allah ba, kuma game da lãhira, sũ kãfirai ne.”

“Kuma na bi addinin iyayẽna, Ibrãhĩm da Is’hãka da Yãƙũba. Bã ya yiwuwa a gare mu mu yi shirka da Allah da kõme. Wannan yana daga falalar Allah a kanmu da mutãne, amma mafi yawan mutãne bã su gõdewa.”

“Yã abõkaina biyu na kurkuku! Shin iyãyen giji dabam-dabam ne mafiya alhẽri kõ kuwa Allah Makaɗaici Mai tanƙwasãwa?”

“Ba ku bauta wa kõme, baicinSa, fãce waɗansu sũnãye waɗanda kuka ambace su, kũ da ubanninku. Allah bai saukar da wani dalĩli ba game da su. Bãbu hukunci fãce na Allah. Ya yi umurnin kada ku bauta wa kõwa fãce Shi. Wancan ne addini madaidaici, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.”

“Yã abõkaina biyu, na kurkuku! Amma ɗayanku, to, zai shãyar da uban gidansa giya, kuma gudan, to, zã a tsĩrẽ shi, sa’an nan tsuntsãye su ci daga kansa. An hukunta al’amarin, wanda a cikinsa kuke yin fatawa.”

Kuma ya ce da wanda ya tabbatar da cẽwa shi mai kuɓuta ne daga gare su, “Ka ambacẽ ni a wurin uban gidanka.” Sai Shaiɗan ya mantar da shi tunãwar Ubangijinsa, sabõda haka ya zauna a cikin kurkuku ‘yan shekaru.

Kuma sarki ya ce: “Lalle ne, nã yi mafarki; nã ga shãnu bakwai mãsu ƙiba, waɗansu bakwai rãmammu, sunã cin su, da zangarku bakwai kõre-kõre da waɗansu ƙeƙasassu. Yã kũ jama’a! Ku yi mini fatawa a cikin mafarkĩna, idan kun kasance ga mafarki kunã fassarawa.”

Suka ce: “Yãye-yãyen mafarki ne, kuma ba mu zamo masana ga fassarar yãye-yãyen mafarki ba.”

Kuma wannan da ya kuɓuta daga cikinsu ya ce: a bãyan yã yi tunãni a lõkaci mai tsawo, “Nĩ, inã bã ku lãbãri game da fassararsa. Sai ku aike ni.”

“Yã Yũsufu! Yã kai mai yawan gaskiya! Ka yi mana fatawa a cikin shãnu bakwai mãsu ƙiba, waɗansu bakwai rãmammu sunã cin su, da zangarku bakwai kõrãye da waɗansu ƙẽƙasassu, tsammãnĩna in kõma ga mutãne, tsammãninsu zã su sani.”

Ya ce: “Kunã shũka, shẽkara bakwai tutur, sa’an nan abin da kuka girbe, sai ku bar shi, a cikin zanganniyarsa, sai kaɗan daga abin da kuke ci.”

“Sa’an nan kuma waɗansu bakwai mãsu tsanani su zo daga hãyan wancan, su cinye abin da kuka gabãtar dõminsu, fãce kaɗan daga abin da kuke ãdanãwa.”

“Sa’an nan kuma wata shẽkara ta zo daga bãyan wancan, a cikinta ake yi wa mutãne ruwa mai albarka, kuma a cikinta suke mãtsar abin sha.”

Kuma sarkin ya ce: “Ku zo mini da shi.” To, a lõkacin da manzo ya je masa (Yũsufu), ya ce: “Ka kõma zuwa ga uban gidanka, sa’ an nan ka tambaye shi; Mẽnene hãlin mãtãyen nan waɗanda suka yanyanke hannãyensu? Lalle ne Ubangijĩna ne Masani game da kaidinsu.”

Ya ce: “Mẽne ne babban al’amarinku, a lõkacin da kaka nẽmi Yũsufu daga kansa?” Suka ce: “Tsarki ga Allah yake! Ba mu san wani mummũnan aiki a kansaba.” Mãtar Azĩz ta ce: “Yanzu fagaskiya ta bayyana. Nĩ ce nã nẽme shi daga kansa. Kuma lalle ne shĩ, haƙĩƙa, yanã daga mãsu gaskiya.

“Wancan ne, dõmin ya san cẽwa lalle ne ni ban yaudareshi ba a ɓõye, kuma lalle Allah bã Ya shiryar da kaidin mayaudara.”

“Kuma bã ni kuɓutar da kaina. Lalle ne rai, haƙĩƙa, mai yawan umurni ne da mummũnan aiki, fãce abin da Ubangjina Ya yi na; rahama. Lalle Ubangjina Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.”

Kuma sarkin ya ce: “Ku zo mini da shi in kẽɓe shi ga kaina.” To, a lõkacin da Yũsufu ya yi masa magana sai ya ce: “Lalle ne kai a yau, a gunmu, mai daraja ne, amintacce.”

Ya ce: “Ka sanya ni a kan taskõkin ƙasa. Lalle ne nĩ, mai tsarẽwa ne, kuma masani.”

Kuma kamar wancan ne Muka bãyar da ĩko ga Yũsufu a cikin ƙasa yanã sauka a inda duk yake so. Munã sãmun wanda Muke so da rahamar Mu, kuma bã Mu tõzartar da lãdar mãsu kyautatawa.

Kuma lalle lãdar Lãhira ce mafi alhẽri ga waɗandasuka yi ĩmãni, kuma suka kasance mãsu taƙawa.

Kuma ‘yan’uwan Yũsufu suka jẽ, sa’an nan suka shiga a gare shi, sai ya gãne su, alhãli kuwa su, sunã mãsu musunsa.

Kuma a lõkacin da ya yi musu tattali da tattalinsu, ya ce: “Ku zo mini da wani ɗan’uwa nãku daga ubanku. Ba ku gani ba cẽwa lalle ne nĩ, inã cika ma’auni, kuma nĩ ne mafi alhẽrin mãsu saukarwa?”

“Sa’an nan idan ba ku zo mini da shĩ ba, to, bãbu awoa gare ku a wurĩna, kuma kada ku, kasance ni.”

Suka ce: “Zã mu nẽme shi daga ubansa. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu aikatãwa ne.”

Kuma ya ce wa yaransa, “Ku sanya hajjarsu a cikin kãyansu, tsammãninsu sunã gãne ta idan sun jũya zuwa ga mutãnensu, tsammã ninsu, zã su kõmo.”

To, a lõkacin da suka kõma zuwa ga ubansu, suka ce: “Yã bãbanmu! An hana mu awo sai ka aika ɗan’uwanmu tãre da mu. Zã mu yi awo. Kuma lalle ne, haƙĩƙa mũ, mãsu lũra da Shi ne.”

Ya ce: “Ashe, zã ni amince muku a kansa? Fãce dai kamar yadda na amince muku a kan ɗan’uwansa daga gabãni, sai dai Allah ne Mafĩfĩcin mãsu tsari, kuma Shĩ ne Mafi rahamar mãsu rahama.”

Kuma a lõkacin da suka bũɗe kãyansu, suka sãmi hajjarsu an mayar musu da ita, suka ce: “Yã bãbanmu! Ba mu zãlunci! Wannan hajjarmu ce an mayar mana da ita, kuma mu nẽmo wa iyalinmu abinci, kuma mu kiyãye ɗan’uwanmu, kuma mu ƙãra awon kãyan rãƙumi guda, wancan awo ne mai sauki.”

Ya ce: “Bã zan sake shi tãre da kũ ba, sai kun kawo mini alkawarinku baga Allah, haƙĩƙa, kunã dawo mini da shi, sai fa idan an kẽwaye ku.” To, a, lõkacinda suka yi mãsa alkawari, ya ce: “Allah ne wakĩli a kan abin da muke faɗa.”

Kuma ya ce: “Yã ɗiyana! Kada ku shiga ta ƙõfa guda, ku shiga ta ƙõfõfi dabam-dabam, kuma bã na wadãtar muku kõme daga Allah. Bãbu hukunci fãce daga Allah, a gare Shi na dõgara, kuma a gare Shi mãsu dõgara sai su dõgara.”

Kuma a lõkacin da suka shiga daga inda ubansu ya umurce su wani abu bai kasance yanã wadãtarwa ga barinsu daga Allah ba fãce wata bukata ce a ran Yãƙũbu, ya bayyana ta. Kuma lalle ne shĩ, haƙĩƙa, ma’abũcin wani ilmi ne ga abin da Muka sanar da shi, kuma mafi yawan mutãne ba su sani ba.

Kuma a lõkacin da suka shiga wajen Yũsufu, ya tattara ɗan’uwansa zuwa gare shi, ya ce: “Lalle nĩ ne ɗan’uwanka, sabõda haka kada ka yi baƙin ciki da abin da suka kasance sunã aikatãwa.”

Sa’an nan a lõkacin da ya yi musu tattali da tattalinsu, sai ya sanya ma’auni a cikin kãyan ɗan’uwansa sa’an nan kuma mai yẽkuwa ya yi yẽkuwa,” Yã kũ ãyari! lalle ne, haƙĩƙa kũ ɓarãyi ne.”

Suka ce: kuma suka fuskanta zuwa gare su: “Mẽne ne kuke nẽma?”

Suka ce: “Munã nẽman ma’aunin sarki. Kuma wanda ya zo da shi, yanã da kãyan rãkumi ɗaya, kuma ni ne lãmuni game da shi.”

Suka ce: “Tallahi! Lalle ne, haƙĩƙa, kun sani, ba mu zodon mu yi ɓarna a cikin ƙasa ba, kuma ba mu kasance ɓarãyi ba.”

Suka ce: “To mẽne ne sakamakonsa idan, kun kasance maƙaryata?”

Suka ce: “Sakamakonsa, wanda aka same shi a cikin kãyansa, to, shi ne sakamakonsa, kamar wancan ne muke sãka wa azzãlumai.”

To, sai ya fãra (bincike) da jikunansu a gabãnin jakar ɗan’uwansa. Sa’an nan ya fitar da ita daga jakar ɗan’uwansa. Kamar wancan muka shirya wa Yũsufu. Bai kasance ya kãma ɗan’uwansa a cikin addinin (dõkõkin) sarki ba, fãce idan Allah Ya so. Munã ɗaukaka darajõji ga wanda Muka so, kuma a saman kõwane ma’abũcin ilmi akwai wani masani.

Suka ce: “Idan ya yi sãta, to, lalle ne wani ɗan’uwansa yã taɓa yin sãta a gabãninsa.” Sai Yũsufu ya bõye ta a cikin ransa. Kuma bai bayyana ta ba a gare su, ya ce: “Kũ ne mafi sharri ga wuri. Kuma Allah ne Mafi sani daga abin da kuke siffantãwa.”

Suka ce: “Yã kai Azĩzu! Lalle ne yanã da wani ubã, tsoho mai daraja, sabõda haka ka kãma ɗayanmu amatsayinsa. Lalle ne mũ, muna ganin ka daga mãsu kyautatãwa.”

Ya ce: “Allah Ya tsare mu daga mu kãma wani fãce wanda muka sãmi kãyanmu a wurinsa. Lalle ne mũ, a lõkacin nan, haƙĩƙa, azzãlumai ne.”

Sabõda haka, a lõkacin da suka yanke tsammãni daga gare shi, sai suka fita sunã mãsu gãnãwa. Babbansu ya ce: “Shin, ba ku sani ba cẽwa lalle ne ubanku yariƙi alkawari daga Allah a kanku, kuma daga gabanin haka akwai abin da kuka yi na sakaci game da Yũsufu? Sabõda haka, bã zan gushe daga ƙasar nan ba fãce ubana yã yi mini izni, kõ kuwa Allah Ya yi hukunci a gare ni, kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mahukunta.”

“Ku kõma zuwa ga ubanku, ku gaya masa: Yã bãbanmu, lalle ne ɗanka yã yi sãta, kuma ba mu yi shaida ba fãce da abin da muka sani, kuma ba mu kasance mun san gaibu ba.”

“Kuma ka tambayi alƙarya wadda muka kasance a cikinta da ãyari wanda muka gabãto acikinsa, kuma lalle ne haƙĩƙa, mũ mãsu gaskiya ne.”

Ya ce: “Ã’a, zukatanku sun ƙawãta wani al’amari a gare ku. Sai haƙuri mai kyãwo, akwai tsammãnin Allah Ya zo mini da su gabã ɗaya (Yũsufu da ‘yan’uwansa). Lalle ne Shĩ ne Masani, Mai hikima.”

Kuma ya jũya daga gare su, kuma ya ce: “Yã baƙin cikina a kan Yũsufu!” Kuma idãnunsa suka yi fari sabõda huznu sa’an nan yanã ta haɗẽwar haushi.

Suka ce: “Tallahi! Bã zã ka gushe ba, kanã ambaton Yũsufu, har ka kasance Mai rauni ƙwarai, kõ kuwa ka kasance daga mãsu halaka.”

Ya ce: “Abin sani kawai, inã kai ƙarar baƙin cikĩna da sunõna zuwa ga Allah, kuma na san abin da ba ku sani ba daga Allah.”

“Yã ɗiyãna! Sai ku tafi ku nẽmo lãbãrin Yũsufu da ɗan’uwansa. Kada ku yanke tsammãni daga rahamar Allah. Lalle ne, bãbu Mai yanke tsammãni daga rahamar Allah fãce mutãne kãfirai.”

Sa’an nan a lõkacin da suka shiga gare shi suka ce: “Yã kai Azĩzu! Cũta ta shãfe mu, mũ da iyãlinmu, kuma mun zo da wata hãja maras kuma. Sai ka cika mana ma’auni, kuma ka yi sadaka a gare mu. Lalle ne Allah Yanã sãka wa mãsu yin sadaka. “

Ya ce: “Shin, kan san abin da kuka aikata ga Yũsufu da ɗan’uwansa a lõkacin da kuke jãhilai?”

Saka ce: “Shin kõ, lalle ne, kai ne Yũsufu?” Ya ce: “Nĩ ne Yũsufu, kuma wamian shĩ ne ɗan’uwãna. Hƙĩƙa Allah Yã yi falala a gare mu. Lalle ne, shi wanda ya bi Allah da taƙawa, kuma ya yi haƙuri, to, Lalle ne Allah bã Ya tõzarta lãdar mãsu kyautatãwa.”

Suka ce: “Tallahi! Lalle ne haƙĩƙa, Allah Yã zãɓe ka akannmu, kuma lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, mãsu kuskure.”

Ya ce: “Bãbu zargi akanku a yau, Allah Yanã gãfartã muku, kuma Shĩ ne Mafi rahamar mãsu rahama.”

“Ku tafi da rĩgãta wannan, sa’an nan ku jẽfa ta a kan fuskar mahaifina, zai kõma mai gani. Kuma ku zo mini da iyãlinku bãki ɗaya.”

Kuma, a lõkacin da ãyari ya bar (Masar) ubansa ya ce: “Lalle ne nĩ inã shãƙar iskar Yũsufu, bã dõmin kanã ƙaryata ni ba.”

Suka ce: “Tallahi lalle ne, kai, haƙĩƙa, kanã a cikin ɓatarka daɗaɗɗa.”

Sa’an nan a lõkacin da mai bãyar da bushãra ya je, sai ya jẽfa ta a kan fuskarsa, sai ya kõma mai gani. Ya ce: “Shin, ban gaya muku ba, lalle ne, ni inã sanin abin da ba ku sani ba, daga Allah?”

Suka ce: “Yã ubanmu! ka nẽma mana gãfara ga zunubanmu, lalle ne mũ, mun kasance mãsu kuskure.”

Ya ce: “Da sannu zã ni nẽma muku gãfara daga Ubangijina. Shi ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.”

Sa’an nan a lõkacin da suka shiga gun Yũsufu, yã tattara mahaifansa biyu a gare shi, kuma ya ce: “Ku shiga Masar in Allah Ya so, kuna amintattu.”

Kuma ya ɗaukaka iyãyensa biyu a kan karaga, sa’an nan suka fãɗi a gare shi, suna mãsu sujada. Kuma ya ce: “Ya bãbãna! Wannan ita ce fassarar mafarkin nan nãwa. Lalle ne Ubangijina Ya sanya shi ya tabbata sõsai, kuma lalle ne Ya kyautata game da ni a lõkacin da Ya fitar da ni daga kurkuku. Kuma Ya zo da ku daga ƙauye, a bãyan Shaiɗan yã yi fisgar ɓarna a tsakãnĩna da tsakãnin ‘yan’uwana, Lalle ne Ubangijina Mai tausasawa ne ga abin da Yake so. Lalle ne Shĩ, Shĩ ne Masani, Mai hikima.”

“Yã Ubangijina lalle ne Kã bã ni daga mulki, kuma Kã sanar da ni daga fassarar lãbaru. Ya Mahaliccin sammai da ƙasa! Kai ne Majiɓincĩna a dũniya da Lãhira Ka karɓi raina inã Musulmi, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai.”

Wannan daga lãbarun gaibi ne, Munã yin wahayinsa zuwa gare ka, kuma ba ka kasance a wurinsu ba a lõkacin da suke yin niyyar zartar da al’amarinsu, alhãli sunã yin mãkirci.

1Yakubu ya zauna a ƙasar Kan’ana inda mahaifinsa ya yi baƙunci. 2Wannan shi ne tarihin zuriyar Yakubu.Yusufu da ‘Yan’uwansaYusufu yana da shekara goma sha bakwai sa’ad da ya zama makiyayin garke tare da ‘yan’uwansa, ɗan ƙanƙanen yaro ne a tsakanin ‘ya’ya maza na Bilha da Zilfa matan mahaifinsa. Sai Yusufu ya kawo labarin munanan abubuwa da ‘yan’uwansa suke yi a wurin mahaifinsa.3Isra’ila kuwa ya fi ƙaunar Yusufu da kowannensu, domin shi ɗan tsufansa ne. Sai ya yi masa riga mai ado. 4Amma sa’ad da ‘yan’uwansa suka gane mahaifinsu yana ƙaunarsa fiye da dukansu, suka ƙi jininsa, ba su iya maganar alheri da shi.5Yusufu ya yi mafarki. Sa’ad da ya faɗa wa ‘yan’uwansa, suka ƙara ƙin jininsa. 6Ya ce musu, “Ku ji irin mafarkin da na yi. 7Ga shi, muna ɗaurin dammuna cikin gona, ga kuwa damina ya tashi tsaye kyam, ga kuma dammunanku suka taru kewaye da shi, suka sunkuya wa damina.”8’Yan’uwansa suka ce masa, “Ashe, lalle ne kai za ka sarauce mu? Ko kuwa, ashe lalle ne kai za ka mallake mu?” Sai suka daɗa ƙin jininsa domin mafarkansa da maganganunsa.9Shi kuwa sai ya sāke yin wani mafarki, ya faɗa wa ‘yan’uwansa, ya ce, “Ga shi kuma na sāke yin wani mafarki, na ga rana, da wata, da taurari goma sha ɗaya suna sunkuya mini.”10Amma sa’ad da ya faɗa wa mahaifinsa da ‘yan’uwansa, sai mahaifinsa ya tsauta masa, ya ce, “Wane irin mafarki ne wannan da ka yi? Lalle ne, da ni da mahaifiyarka da ‘yan’uwanka za mu sunkuya a gabanka har ƙasa?” 11 ‘Yan’uwansa suka ji kishinsa, amma mahaifinsa ya riƙe al’amarin cikin zuciyarsa.An Sayar da Yusufu zuwa Masar12Wata rana, da ‘yan’uwansa suka tafi kiwon garken mahaifinsu a Shekem, 13Isra’ila ya ce wa Yusufu, “Ashe, ba ‘yan’uwanka suna kiwon garken a Shekem ba? Zo in aike ka wurinsu.”Sai ya ce masa, “Ga ni.”14Mahaifinsa ya ce, “Tafi yanzu, ka dubo lafiyar ‘yan’uwanka da ta garken, ka kawo mini labarinsu.” Saboda haka, ya aike shi daga kwarin Hebron.Da Yusufu ya isa Shekem, 15wani mutum ya same shi yana hange-hange cikin karkara. Sai mutumin ya tambaye shi ya ce, “Me kake nema?”16Yusufu ya ce, “Ina neman ‘yan’uwana ne. Ina roƙonka ka faɗa mini idan ka san inda suke kiwon garkuna.”17Mutumin ya ce, “Sun riga sun tashi daga nan, gama na ji sun ce, ‘Bari mu tafi Dotan.’ ” Saboda haka, Yusufu ya bi sawun ‘yan’uwansa, ya kuwa same su a Dotan.18Da suka hango shi daga nesa, kafin ya zo kusa da su, sai suka ƙulla su kashe shi. 19Suka ce wa juna, “Ga mai mafarkin nan can yana zuwa. 20Ku zo mu kashe shi yanzu, mu jefa shi cikin ɗaya daga cikin rijiyoyin nan, sa’an nan mu ce, wata muguwar dabbar jeji ce ta kashe shi, sa’an nan mu ga yadda mafarkinsa zai zama.”21Amma sa’ad da Ra’ubainu ya ji, ya yi ƙoƙari ya cece shi daga hannunsu, yana cewa, “Kada mu raba shi da ransa. 22Kada mu kashe shi, mu dai jefa shi cikin rijiyan nan a jeji, amma kada mu yi masa lahani.” Ya yi haka da nufin ya cece shi daga hannunsu, ya mayar da shi ga mahaifinsu. 23Don haka, sa’ad da Yusufu ya zo wurin ‘yan’uwansa, suka tuɓe masa rigarsa, rigan nan mai ado wadda take wuyansa. 24Suka ɗauke shi suka jefa shi cikin rijiyar. Rijiyar kuwa wofi ce, ba ruwa a ciki.25Suka zauna su ci abinci, da suka ɗaga ido suka duba, sai ga ayarin Isma’ilawa suna zuwa daga Gileyad, da raƙumansu ɗauke da ƙāro, da man ƙanshi na wartsakewa, da mur, suna gangarawa kan hanyarsu zuwa Masar. 26Yahuza ya ce wa ‘yan’uwansa, “Wace riba ke nan, in mun kashe ɗan’uwanmu, muka ɓoye jininsa? 27Ku zo mu sayar da shi ga Isma’ilawa, kada mu bar hannunmu ya taɓa shi, gama shi ɗan’uwanmu ne, shi kuma jikinmu ne.” ‘Yan’uwansa suka yarda da shi. 28 Da Madayanawa, fatake, suna wucewa, sai suka jawo Yusufu suka fitar da shi daga cikin rijiyar suka sayar wa Isma’ilawa a bakin azurfa ashirin, aka kuwa tafi da Yusufu zuwa Masar.29Sa’ad da Ra’ubainu ya koma a wajen rijiya, da bai ga Yusufu a cikin rijiyar ba, sai ya kyakkece tufafinsa, 30ya koma wurin ‘yan’uwansa, ya ce, “Saurayin ba ya nan, ni kuwa, ina zan sa kaina?”31Suka ɗauki rigar Yusufu, suka yanka akuya, suka tsoma rigar cikin jinin. 32Suka kuma ɗauki rigan nan mai ado, suka kawo ta ga mahaifinsu, suka ce, “Ga abar da muka samu, duba ka gani, ta ɗanka ce, ko kuwa?”33Da ya gane ita ce, ya ce, “Rigar ɗana ce, wani mugun naman jeji ne ya cinye shi, ba shakka an yayyage Yusufu.” 34Sai Yakubu ya kyakkece rigunansa, ya yi ɗamara da majayi, ya yi kukan ɗansa har kwanaki masu yawa. 35Dukan ‘ya’yansa mata da maza suka tashi domin su ta’azantar da shi, amma ya ƙi ta’azantuwa, yana cewa, “A’a, a Lahira zan tafi wurin ɗana, ina baƙin ciki.” Haka mahaifinsu ya yi kuka dominsa. 36A lokacin kuwa, ashe, Madayanawa sun riga sun sayar da shi a Masar ga Fotifar, sarkin yaƙin Fir’auna, shugaba na masu tsaron fādar Fir’auna.

Yahuza da Tamar

1Ya zama fa a wannan lokaci, Yahuza ya bar ‘yan’uwansa ya gangara, ya zauna wurin wani Ba’adullame mai suna Hira. 2A can, sai Yahuza ya ga ‘yar wani Bakan’ane mai suna Shuwa. Ya aure ta, ya shiga wurinta, 3ta yi ciki, ta haifi ɗa namiji, ya kuwa raɗa masa suna Er. 4Sai ta sāke yin ciki, ta kuma haifi ɗa, ta raɗa masa suna Onan. 5Har yanzu kuma ta sāke haihuwar ɗa, ta raɗa masa suna Shela. A Kezib ta haifi Shela.6Yahuza kuwa ya auro wa ɗan farinsa, Er, mata, sunanta Tamar. 7Amma Er, ɗan farin Yahuza mugu ne a gaban Ubangiji. Sai Ubangiji ya kashe shi. 8Sa’an nan Yahuza ya ce wa, Onan, “Shiga wurin matar ɗan’uwanka, ka yi mata wajibin ɗan’uwan miji, ka samar wa ɗan’uwanka zuriya.” 9Amma Onan ya sani zuriyar ba za ta zama tasa ba, saboda haka duk lokacin da ya shiga wurin matar ɗan’uwansa, sai ya zubar da maniyyi a ƙasa don kada ya ba ɗan’uwansa zuriya. 10Amma abin nan da ya yi, mugun abu ne a gaban Ubangiji, shi ma Ubangiji ya kashe shi. 11Yahuza kuwa ya ce wa Tamar surukarsa, “Yi zaman gwauranci a gidan mahaifinki, har ɗana Shela ya yi girma,” gama yana jin tsoro kada shi kuma ya mutu kamar ‘yan’uwansa. Saboda haka Tamar ta tafi ta zauna a gidan mahaifinta.12A kwana a tashi, ga matar Yahuza, ‘yar Shuwa ta rasu. Da Yahuza ya gama karɓar ta’aziyya, sai ya haura Timna wurin masu sausayar tumakinsa, da shi da abokinsa Hira Ba’adullame. 13Sa’ad da aka faɗa wa Tamar, aka ce, “Surukinki zai haura zuwa Timna ya yi wa tumakinsa sausaya,” 14sai ta tuɓe tufafinta na takaba, ta yi lulluɓi ta lulluɓe kanta, ta zauna a ƙofar Enayim a hanyar Timna, gama ta ga Shela ya yi girma, amma ba a ba da ita gare shi ba.15Da Yahuza ya gan ta, ya yi tsammani wata karuwa ce, gama ta rufe fuskarta. 16Sai ya je wurinta a gefen hanyar, ya ce, “Zo, mu kwana mana,” gama bai san ita surukarsa ba ce.Sai ta ce, “Me za ka ba ni, da za ka kwana da ni?”17Ya amsa, ya ce, “Zan aiko miki da ɗan akuya daga cikin garken.”Ta ce, “Ko ka ba ni jingina, kafin ka aiko?”18Ya ce, “Wane alkawari zan yi miki?”Ta amsa, ta ce, “Ba ni hatiminka da ɗamararka da sandan da yake a hannunka.” Ya kuwa ba ta su, ya kwana da ita. Sai ta yi ciki. 19Ta tashi ta yi tafiyarta. Da ta cire lulluɓinta ta sa tufafinta na takaba.20Sa’ad da Yahuza ya aika da ɗan akuya ta hannun abokinsa Ba’adullame don ya karɓi jinginar daga hannun matar, bai same ta ba. 21Ya tambayi mutanen wurin, ya ce, “Ina karuwan nan wadda take zaune a Enayim a bakin hanya?”Sai suka ce, “Ba wata karuwar da ta taɓa zama nan.”22Ya koma wurin Yahuza ya ce, “Ban same ta ba, mutanen wurin kuma suka ce, ‘Ba wata karuwa da ta zo nan.’ ”23Yahuza ya amsa, ya ce, “Bari ta riƙe abubuwan su zama nata, don kada a yi mana dariya, gama ga shi, na aike da ɗan akuya, amma ba ka same ta ba.”24Bayan misalin wata uku, aka faɗa wa Yahuza, “Tamar surukarka ta yi lalata, har ma tana da ciki.”Sai Yahuza ya ce, “A fito da ita, a ƙone ta.”25Za a fito da ita ke nan sai ta aika wa surukinta, ta ce, “Wanda yake da waɗannan kaya shi ya yi mini ciki.” Ta kuma ce, “Ka shaida, ina roƙonka, ko na wane ne wannan hatimi, da abin ɗamarar, da sanda.”26Sai Yahuza ya shaida su, ya ce, “Ta fi ni gaskiya, tun da yake ban ba da ita ga ɗana Shela ba.” Daga nan bai ƙara kwana da ita ba.27Sa’ad da lokaci ya yi da za ta haihu, ashe, cikin tagwaye ne. 28Da tana cikin naƙuda, sai hannun wani ya fara fitowa, ungozoma kuwa ta ɗauki jan zare ta ɗaura a hannun, tana cewa, “Wannan shi ya fara fitowa.” 29Amma da ya janye hannunsa, ga ɗan’uwansa ya fito, sai ta ce, “A’a, ta haka za ka keta ka fito!” Saboda haka aka raɗa masa suna Feresa. 30Daga baya ɗan’uwansa ya fito da jan zare a hannunsa, aka kuwa sa masa suna Zera.

Yusufu da Matar Fotifar

1Aka kuwa gangara da Yusufu zuwa Masar. Sai Fotifar Bamasare sarkin yaƙin Fir’auna, shugaban masu tsaron fāda ya saye shi daga hannun Isma’ilawa, waɗanda suka gangaro da shi zuwa can. 2 Ubangiji yana tare da Yusufu, har ya zama mutum ne mai galaba a gidan maigidansa Fotifar, Bamasaren. 3Maigidansa kuwa ya ga Ubangiji yana tare da shi, Ubangiji kuma yakan sa albarka ga aikin hannuwansa duka. 4Don haka Yusufu ya sami tagomashi a wurinsa, ya zama mai yi masa hidima. Fotifar kuma ya shugabantar da shi a bisa gidansa, da bisa dukan abin da yake da shi. 5Ubangiji ya sa wa gidan Bamasaren albarka sabili da Yusufu tun daga lokacin da Fotifar Bamasaren ya shugabatar da shi a bisa gidansa da dukan dukiyarsa. Albarkar Ubangiji na bisa dukan abin da yake da shi, na gida da na jeji. 6Ya bar dukan abin da yake da shi a hannun Yusufu. Tun da ya same shi, ba ruwansa da kome, sai dai abincin da zai ci.Yusufu fa kyakkyawa ne mai kyan gani. 7Ya zamana fa, wata rana, sai matar maigidansa ta sa idonta kan Yusufu, ta ce, “Ka kwana da ni.” 8Amma ya ƙi, ya kuwa faɗa wa matar maigidansa, ya ce, “Ga shi, tun da maigida ya same ni, maigidana ba ruwansa da kome na cikin gida, ya kuwa riga ya sa dukan abin da yake da shi cikin hannuna. 9Bai fi ni iko cikin gidan nan ba, ba kuma abin da ya hana mini sai ke kaɗai, domin ke matarsa ce. Ƙaƙa fa zan aikata wannan babbar mugunta, in yi wa Allah zunubi?” 10Ko da yake ta yi ta yi wa Yusufu magana yau da gobe, amma bai biye mata ya kwana da ita ko su zauna tare ba.11Amma wata rana, sa’ad da ya shiga cikin gida ya yi aikinsa, mazajen gidan kuma ba wanda yake gidan, 12sai ta kama rigarsa, tana cewa, “Ka kwana da ni.” Amma ya bar rigarsa a hannunta ya gudu ya fita. 13Da ta ga ya bar rigarsa a hannunta ya gudu, ya fita waje, 14sai ta yi kira ga mutanen gidan, ta ce musu, “Ku duba ku gani, ya kawo mana Ba’ibrane ya ci mutuncinmu. Ya zo wurina don ya kwana da ni, sai na yi ihu da ƙarfi. 15Da ya ji na ta da murya na yi ihu, ya kuwa gudu ya bar rigarsa, ya fita waje.”16Ta ajiye rigar a wurinta har maigidansa ya komo. 17Sai ta mayar masa da magana, ta ce, “Baran nan, Ba’ibrane wanda ka kawo cikinmu, ya shigo wurina don ya ci mutuncina, 18amma nan da nan da na ta da murya na yi ihu, sai ya gudu ya bar rigarsa a hannuna, ya gudu zuwa waje.”19Sa’ad da maigidan Yusufu ya ji abin da matarsa ta faɗa masa, “Ka ji yadda baranka ya yi da ni ke nan,” sai ya husata. 20Maigidan Yusufu ya ɗauke shi ya māka shi a kurkuku, inda ‘yan sarƙa na sarki suke tsare, can ya zauna a kurkuku. 21 Amma Ubangiji yana tare da Yusufu, ya kuwa nuna masa madawwamiyar ƙauna, ya sa ya sami farin jini a wurin yarin kurkukun. 22Yarin kurkuku ya shugabantar da Yusufu bisa dukan ‘yan sarƙa da suke a kurkuku, dukan abin da ake yi a wurin kuma shi yake yi. 23Yarin kurkukun, ba ruwansa da dukan abin da Yusufu yake kula da shi, domin Ubangiji yana tare da shi, dukan abin da ya yi kuwa Ubangiji yakan sa wa abin albarka.

Yusufu Ya Fassara Mafarkan ‘Yan Kurkuku

1Bayan waɗannan al’amura, sai mai shayarwa da mai tuya na Sarkin Masar suka yi wa maigidansu Sarkin Masar laifi. 2Fir’auna ya yi fushi da ma’aikatan nan nasa biyu, wato shugaban masu shayarwa da shugaban masu tuya. 3Ya ba da su a sa su kurkuku, cikin gidan shugaban masu tsaron fāda, wato kurkuku inda Yusufu yake a tsare. 4Shugaban ‘yan tsaron ya danƙa su ga Yusufu don ya hidimta musu, sun kuwa jima a kurkukun har an daɗe.5Suka yi mafarki, su biyu ɗin, a dare ɗaya, da shi mai shayarwar da mai tuyar na gidan Sarkin Masar, waɗanda aka sa a kurkuku, kowanne kuwa da nasa mafarkin da kuma tasa irin fassarar mafarkin. 6Da Yusufu ya zo wurinsu da safe, ya ga sun damu. 7Sai ya tambaye su ya ce, “Me ya sa fuskokinku suke a yamutse yau?”8Suka ce masa, “Mafarkai muka yi, ba kuma wanda zai fassara mana su.”Sai Yusufu ya ce musu, “Ashe, ba a wurin Allah fassarori suke ba? Ku faɗa mini su, ina roƙonku.”9Saboda haka, shugaban masu shayarwa ya faɗa wa Yusufu mafarkinsa, ya ce masa, “A mafarkina ga kurangar inabi a gabana. 10A kurangar akwai rassa uku. Sai ta yi toho, ta huda nan da nan, ta kuma yi nonna, har suka nuna suka zama inabi. 11Finjalin Fir’auna na hannuna, sai na ɗauki ‘ya’yan inabi na matse su cikin finjalin Fir’auna, na sa finjalin a hannun Fir’auna.”12Yusufu ya ce masa, “Wannan ita ce fassararsa, rassan nan uku, kwana uku ne, 13bayan kwana uku Fir’auna zai ɗaukaka ka, ya komar da kai matsayinka, za ka kuma sa finjalin Fir’auna a hannunsa kamar dā lokacin da kake mai hidimar shayarwarsa. 14Amma ka tuna da ni sa’ad da abin ya tabbata gare ka, sai ka yi mini alheri, ka ambace ni a wurin Fir’auna, har da za a fisshe ni daga wannan gida. 15Gama ni, hakika sato ni aka yi daga ƙasar Ibraniyawa. A nan kuma ban yi wani abin da zai isa a sa ni a kurkuku ba.”16Sa’ad da shugaban masu tuya ya ga fassarar tana da kyau, sai ya ce wa Yusufu, “Ni ma cikin nawa mafarki, na ga kwanduna uku na waina a bisa kaina. 17A kwandon da yake bisa ɗin akwai toye-toye iri iri domin Fir’auna, amma ga tsuntsaye suna ta ci daga cikin kwandon da yake bisa duka, wato wanda yake bisa kaina ɗin.”18Yusufu ya amsa, “Wannan ita ce fassararsa, kwandunan uku, kwana uku ne, 19bayan kwana uku Fir’auna zai falle kanka ya rataye ka a bisa itace, tsuntsaye kuwa za su ci naman jikinka.”20A rana ta uku, wadda take ranar haihuwar Fir’auna, Fir’auna ya yi wa dukan bayinsa biki, sai ya kawo shugaban masu shayarwa da shugaban masu tuya a gaban fādawansa. 21Ya komar da shugaban masu shayarwa a matsayinsa na shayarwa, ya kuwa miƙa finjali a hannun Fir’auna, 22amma ya rataye shugaban masu tuya kamar yadda Yusufu ya fassara musu. 23Duk da haka shugaban masu shayarwar bai tuna da Yusufu ba, amma ya manta da shi.

Yusufu Ya Fassara wa Fir’auna Mafarkansa

1Bayan shekaru biyu cif, Fir’auna ma ya yi mafarki, ga shi, yana tsaye a bakin kogin Nilu, 2sai ga shanu bakwai masu ƙiba mulmul suka fito daga Nilu, suka yi kiwo cikin iwa. 3Ga kuma waɗansu shanu bakwai munana ramammu suka fito daga cikin Nilu a bayansu, suka tsaya kusa da waɗancan shanu a bakin Nilu. 4Sai shanun nan munana ramammu suka cinye shanun nan bakwai masu sheƙi, masu ƙibar. Sai Fir’auna ya farka. 5Barci kuma ya kwashe shi, ya sāke yin mafarki a karo na biyu, sai zangarku bakwai masu kauri kyawawa suna girma a kara gudu. 6Ga shi kuma, a bayansu waɗansu zangarku bakwai suka fito sirara waɗanda iskar gabas ta ƙeƙasar. 7Sai siraran zangarkun suka haɗiye zangarkun nan bakwai masu kauri kyawawa. Sai Fir’auna ya farka, ashe, mafarki ne. 8 Saboda haka da safe, hankalinsa ya tashi, sai ya aika aka kirawo dukan bokayen Masar da dukan masu hikimar Masar, Fir’auna kuwa ya faɗa musu mafarkansa, amma ba wanda ya iya fassara masa su.9Sai shugaban masu shayarwa ya ce wa Fir’auna, “Yau, na tuna da laifofina. 10Sa’ad da ka yi fushi da barorinka, ka sa ni da shugaban masu tuya cikin kurkukun da yake a cikin gidan shugaban masu tsaron fāda, 11muka yi mafarki dare ɗaya, ni da shi, kowane mutum da irin tasa fassarar mafarkin. 12Akwai wani Ba’ibrane, ɗan saurayi, tare da mu, bawan shugaban masu tsaron fāda, sa’ad da muka faɗa masa sai ya fassara mana mafarkanmu, ya yi wa kowannenmu fassara bisa kan mafarkinsa. 13Yadda ya fassara mana haka kuwa ya zama, aka komar da ni matsayina, mai tuya kuwa aka rataye shi.”14Sai Fir’auna ya aika a kirawo Yusufu, da gaggawa suka fito da shi daga cikin kurkuku. Da Yusufu ya yi aski, ya sāke tufafinsa ya zo gaban Fir’auna. 15Fir’auna kuwa ya ce wa Yusufu, “Na yi mafarkin da ba wanda ya san fassararsa, amma na ji an ce, wai kai, in ka ji mafarkin kana iya fassara shi.”16Yusufu ya amsa wa Fir’auna ya ce, “Ba a gare ni ba, Allah zai amsa wa Fir’auna da kyakkyawar amsa.”17Fir’auna ya ce wa Yusufu, “Ga shi, a cikin mafarkina ina tsaye a bakin Kogin Nilu, 18ga shanu bakwai, masu sheƙi masu ƙiba suka fito daga cikin Nilu suna kiwo cikin iwa. 19Sai waɗansu shanu bakwai ƙanjamammu, munana, ramammu, irin waɗanda ban taɓa ganinsu a ƙasar Masar ba, suka fito bayansu. 20Sai ramammun, munanan shanun suka cinye shanun nan bakwai masu ƙiba na farko, 21amma da suka haɗiye su, ba wanda zai iya sani sun haɗiye su, gama suna nan a ramammunsu kamar yadda suke a dā. Sai na farka. 22Har yanzu kuma, a cikin mafarkina ga zangarku masu kauri kyawawa guda bakwai, suna girma a kara guda, 23zangarku bakwai kuma busassu sirara waɗanda iskar gabas ta ƙeƙasar, suka fito a bayansu. 24Siraran zangarkun kuwa suka haɗiye zangarkun nan bakwai kyawawa masu kauri. Na faɗa wa bokaye, amma ba wanda ya iya yi mini fassararsa.”25Yusufu ya ce wa Fir’auna, “Mafarkin Fir’auna ɗaya ne, Allah ya bayyana wa Fir’auna abin da yake shirin aikatawa. 26Waɗannan shanu bakwai, shekaru bakwai ne, kyawawan zangarkun nan bakwai kuma shekaru bakwai ne, mafarkin ɗaya ne. 27Ramammun shanun nan bakwai da suka fito a bayansu shekaru bakwai ne, busassun zangarkun nan bakwai waɗanda iskar gabas ta ƙeƙasar kuwa, shekaru bakwai ne na yunwa. 28Haka yake kamar yadda na faɗa wa Fir’auna, Allah ya nuna wa Fir’auna abin da yake shirin aikatawa. 29Za a yi shekara bakwai cike da ƙoshi a ƙasar Masar duka, 30amma a bayansu za a yi shekara bakwai na yunwa, amma za a manta da dukan ƙoshin nan a ƙasar Masar, yunwar kuwa za ta game dukan ƙasar. 31Zai kuwa zama kamar ba a taɓa yin ƙoshi a ƙasar ba, saboda tsananin yunwar. 32Maimaitawar mafarkin nan na Fir’auna kuwa, ya nuna cewa Allah ya riga ya ƙaddara al’amarin, hakika kuwa Allah zai tabbatar da shi ba da jimawa ba.33“Yanzu fa bari Fir’auna ya zaɓi mutum mai basira, mai hikima, ya sa shi bisa ƙasar Masar. 34Bari Fir’auna ya ci gaba da naɗa shugabanni bisa ƙasa, don su tattara humushin amfanin ƙasar Masar na shekarun nan bakwai na ƙoshi. 35Bari kuma su tattara dukan abinci a shekarun nan bakwai masu zuwa na albarka, su tsiba a ƙarƙashin ikon Fir’auna saboda abinci cikin birane, su kuma lura da shi. 36Wannan abinci zai zama ajiya domin ƙasar, kariyar shekaru bakwai na yunwa, waɗanda za a yi cikin ƙasar Masar, domin kada ƙasar ta ƙare saboda yunwar.”An Naɗa Yusufu Mai Mulki a Masar37Fir’auna da fādawansa duka sun yarda da wannan shawara. 38Sai Fir’auna ya ce wa fādawansa, “Mā iya samun mutum irin wannan, wanda Ruhun Allah yake cikinsa?” 39Domin haka Fir’auna ya ce wa Yusufu, “Tun da yake Allah ya nuna maka waɗannan abu duka, ba wani mai basira da hikima kamarka, 40 za ka shugabanci gidana, bisa ga cewarka za a mallaki jama’ata, sai dai da sarauta kaɗai nake gaba da kai.” 41Fir’auna ya ce wa Yusufu, “Ga shi, na sa ka bisa dukan ƙasar Masar.” 42 Sai Fir’auna ya cire zobensa mai hatimi daga hannunsa ya sa a hannun Yusufu, ya sa masa rigunan lilin masu kyau, ya rataya masa sarƙar zinariya a wuya, 43ya kuma sa shi ya hau karusarsa ta biyu, suka yi ta shela a gabansa, “Ku ba da hanya.” Ta haka fa ya sa ya zama mai mulki bisa dukan ƙasar Masar. 44Har yanzu dai Fir’auna ya ce wa Yusufu, “Ni ne Fir’auna, ba mutumin da zai ɗaga hannu ko ƙafa cikin dukan ƙasar Masar idan ba da izninka ba.” 45Fir’auna kuwa ya sa wa Yusufu suna, Zafenat-faneya. Ya kuma aurar masa da Asenat ‘yar Fotifera, firist na On. Yusufu kuwa ya fita rangadin ƙasar Masar.46Yusufu yana da shekara talatin lokacin da ya kama aiki a wurin Fir’auna, Sarkin Masar. Yusufu kuwa ya fita daga gaban Fir’auna ya ratsa dukan ƙasar Masar. 47A cikin shekaru bakwai ɗin nan na ƙoshi, ƙasa ta ba da amfani mai yawan gaske, 48sai ya tattara dukan abinci na shekarun nan bakwai da aka yi na ƙoshi a ƙasar Masar, ya kuwa tanada abinci cikin birane, a kowane birni ya tanada abinci daga karkarar da take kewaye da shi. 49Sai Yusufu ya tsiba tsaba kamar yashin teku, har ya daina aunawa domin ba ta aunuwa saboda yawa.50Kafin kuwa shekarun nan na yunwa, an haifa wa Yusufu ‘ya’ya biyu maza, waɗanda Asenat ‘yar Fotifera, firist na On ta haifa masa. 51Yusufu ya raɗa wa ɗan farin suna, Manassa, yana cewa, “Gama Allah ya sa ni in manta da dukan wahalata da dukan gidan mahaifina.” 52Na biyun kuma ya raɗa masa suna, Ifraimu, yana cewa, “Gama Allah ya wadata ni a cikin ƙasar wulakancina.”53Shekarun nan bakwai na ƙoshi da aka yi cikin ƙasar Masar sun cika, 54 aka fara shekaru bakwai na yunwa kamar yadda Yusufu ya faɗa. Sai aka yi yunwa cikin sauran ƙasashe duka, amma a ƙasar Masar akwai abinci. 55 Sa’ad da yunwa ta game dukan ƙasar, mutanen suka yi wa Fir’auna kuka domin abinci, sai Fir’auna ya faɗa wa Masarawa duka, ya ce, “Ku tafi wurin Yusufu, abin da duk ya faɗa muku, sai ku yi.” 56Domin haka sa’ad da yunwar ta bazu ko’ina a ƙasar, Yusufu ya buɗe taskokin ajiya, ya yi ta sayar wa Masarawa, gama yunwa ta tsananta a ƙasar. 57Duniya duka kuwa ta zo Masar wurin Yusufu, ta sayi hatsi saboda yunwa ta tsananta a duniya duka.

‘Yan’uwan Yusufu sun Zo Masar Sayen Abinci

1A sa’ad da Yakubu ya ji akwai hatsi a Masar, sai ya ce wa ‘ya’yansa maza, “Me ya sa kuke zuba wa juna ido? 2 Ga shi kuwa, na ji akwai hatsi a Masar, ku gangara ku sayo mana hatsi a can domin mu rayu, kada mu mutu.” 3Don haka ‘yan’uwan Yusufu su goma suka gangara su sayo hatsi a Masar. 4Amma Yakubu bai aiki Biliyaminu ɗan’uwan Yusufu tare da ‘yan’uwansa ba, gama ya ce, “Kada wata ɓarna ta same shi.”5Haka nan ‘ya’yan Isra’ila maza suka zo su sayi hatsi tare da sauran matafiya, gama ana yunwa a ƙasar Kan’ana. 6Yanzu fa, Yusufu shi ne mai mulkin ƙasar, shi ne kuwa mai sayar wa jama’ar ƙasar duka. ‘Yan’uwan Yusufu suka zo suka sunkuya har ƙasa a gabansa. 7Da Yusufu ya ga ‘yan’uwansa, ya gane da su, amma ya mai da su kamar baƙi, ya yi musu magana da gautsi ya ce, “Daga ina kuka fito?”Suka ce, “Daga ƙasar Kan’ana muka zo sayen abinci.”8Yusufu kuwa ya gane da ‘yan’uwansa amma su ba su gane shi ba. 9 Sai Yusufu ya tuna da mafarkan da ya yi a kansu, ya ce musu, “Ku magewaya ne, zuwa kuka yi domin ku leƙi asirin ƙasar.”10Suka ce masa, “A’a, shugabanmu, domin sayen abinci bayinka suka zo. 11Mu duka ‘ya’yan mutum guda ne, amintattu kuma, bayinka ba magewaya ba ne.”12Yusufu ya ce musu, “A’a! Ku dai kun zo ku ga inda ƙasarmu yake da rashin ƙarfi.”13Suka ce, “Mu bayinka, ‘yan’uwan juna ne, mu goma sha biyu muke maza, ‘ya’yan mutum guda a ƙasar Kan’ana, ga shi kuwa autanmu yana tare da mahaifinmu a yanzu, ɗayan kuwa ya rasu.”14Amma Yusufu ya ce musu, “Ai, kamar dai yadda na faɗa muku, magewaya ne ku. 15Ta haka za a jarraba ku, da ran Fir’auna, ba za ku fita daga nan wurin ba, sai autanku ya zo nan. 16Ku aiki ɗaya daga cikinku ya kawo ɗan’uwanku, amma ku, za a tsare ku, don a tabbatar da maganarku, ko akwai gaskiya cikinku, idan ba haka ba kuwa, da ran Fir’auna, lalle ku magewaya ne.” 17Sai ya tura su cikin waƙafi har kwana uku.18A kan rana ta uku, Yusufu ya ce musu, “Abin da za ku yi in bar ku da rai ke nan, gama ina tsoron Allah, 19sai ku bar ɗan’uwanku ɗaya a tsare a inda aka kulle ku. Idan amintattu ne ku, sauran kuwa su tafi su kai hatsi ga iyalanku mayunwata, 20sa’an nan su kawo mini autanku. Ta haka za a tabbatar da maganarku, har a bar ku da rai.” Haka kuwa suka yi.21Sai suka ce wa junansu, “A ainihin gaskiya, muna da laifi dangane da ɗan’uwanmu, da yake mun ga wahalar da yake sha, sa’ad da kuma ya roƙe mu mu taimake shi, amma ba mu saurara ba, domin haka wannan wahala ta sauko mana.”22  Sai Ra’ubainu ya amsa musu, “Ashe, dā ma ban faɗa muku kada ku cuci yaron ba? Amma ba ku saurara ba. To, ga shi fa, ana neman hakkinsa yanzu.” 23Ba su sani ba, ashe, Yusufu yana jinsu, domin akwai tafinta a tsakaninsu. 24Ya juya waje ɗaya ya yi kuka, sai ya sāke komawa wurinsu ya yi magana da su. Ya ɗauki Saminu daga cikinsu ya ɗaure shi a kan idonsu.‘Yan’uwan Yusufu Suka Komo Kan’ana25Yusufu ya umarta a cika tayakan da hatsi, a kuma mayar wa kowa da kuɗinsa cikin taikinsa, a kuma ba su guzuri don hanya. Haka kuwa aka yi musu. 26Suka labta wa jakunansu hatsi, suka tashi. 27Da ɗaya daga cikinsu ya buɗe taikinsa domin ya ba jakinsa tauna a zango, sai ya ga kuɗinsa a bakin taikinsa. 28Ya ce wa ‘yan’uwansa, “An mayar mini da kuɗina, ga shi nan a taiki!”Zuciyarsu ta karai sai suka juya suna duban juna, suna makyarkyata suna cewa, “Me ke nan da Allah ya yi mana?”29Sa’ad da suka zo wurin mahaifinsu Yakubu a ƙasar Kan’ana, suka faɗa masa dukan abin da ya same su, suna cewa, 30“Mutumin, shugaban ƙasar, ya yi mana magana da gautsi, ya ɗauke mu a magewayan ƙasa. 31Amma muka ce masa, ‘Mu amintattu ne, mu ba magewaya ba ne. 32Mu sha biyu ne ‘yan’uwan juna, ‘ya’ya maza na mahaifinmu, ɗayan ya rasu, autan kuwa yana tare da mahaifinmu a yanzu haka a ƙasar Kan’ana.’33“Sai mutumin, shugaban ƙasar, ya ce mana, ‘Ta haka zan sani ko ku amintattu ne, ku bar ɗan’uwanku ɗaya tare da ni, ku ɗauki hatsi domin iyalanku mayunwata, ku yi tafiyarku. 34Ku kawo mini autanku, da haka zan sani ku ba magewaya ba ne, amma amintattu ne, zan kuma ba ku ɗan’uwanku, ku yi ta ciniki a ƙasar.’ ”35Da zazzagewar tayakansu ga ƙunshin kuɗin kowannensu a cikin taikinsa. Sa’ad da su da mahaifinsu suka ga ƙunshin kuɗinsu, suka razana. 36Sai Yakubu mahaifinsu, ya ce musu, “Kun sa ni rashi, ga shi, ba Yusufu, Saminu ba shi, wai kuma yanzu za ku ɗauki Biliyaminu, ga dai irin abubuwan da suka faɗo mini.”37Ra’ubainu kuwa ya ce wa mahaifinsa, “Ka kashe ‘ya’yana biyu maza idan ban komo da shi ba, ka sa shi a hannuna, zan kuwa komo maka da shi.”38Amma ya ce, “Ɗana ba zai gangara tare da ku ba, ga ɗan’uwansa ya rasu, shi kaɗai kuwa ya ragu. Zai yiwu a kashe shi a hanya. Na tsufa ƙwarai ba zan iya ɗaukar wannan baƙin ciki ba, zai kashe ni.”

‘Yan’uwan Yusufu Sun Sāke Komawa Masar da Biliyaminu

1A halin yanzu, yunwa ta tsananta a ƙasar. 2Sa’ad da suka cinye hatsin da suka kawo daga Masar, mahaifinsu ya ce musu, “Ku koma, ku sayo mana ɗan abinci.”3Amma Yahuza ya ce masa, “Mutumin fa, ya yi mana faɗakarwa sosai, ya ce, ‘Idan ba tare da autanku kuka zo ba, ba za ku ga fuskata ba.’ 4In za ka yarda ka aiki ɗan’uwanmu tare da mu, sai mu gangara mu sayo muku abinci. 5Amma idan ba haka ba, ba za mu tafi ba, gama mutumin ya ce mana, ‘Ba za ku ga fuskata ba idan ba ku zo tare da ɗan’uwanku ba.’ ”6Sai Isra’ila ya ce, “Don me kuka cuce ni, da kuka faɗa wa mutumin nan, kuna da wani ɗan’uwa?”7Suka amsa, “Ai, mutumin ne ya yi ta tambayar labarinmu da na danginmu, yana cewa, ‘Mahaifinku yana da rai har yanzu? Kuna kuma da wani ɗan’uwa?’ Abin da muka faɗa masa amsoshi ne na waɗannan tambayoyi. Ta ƙaƙa za mu iya sani zai ce, ‘Ku zo da ɗan’uwanku’?”8Sai Yahuza ya ce wa Isra’ila, mahaifinsu, “Ka sa saurayin a hannuna, mu tashi mu tafi, mu sami abinci mu rayu, kada mu mutu, da mu da kai da ƙanananmu. 9Na ɗauki lamuninsa, a hannuna za ka neme shi. Idan ban komo maka da shi, in kawo shi a gabanka ba, bari alhakin ya zauna a kaina har abada, 10gama da ba don mun yi jinkiri ba, da yanzu, ai, mun yi sawu biyu.”11Mahaifinsu, Isra’ila ya ce musu, “In tilas haka zai zama, sai ku yi wannan, ku ɗiba daga cikin zaɓaɓɓu, mafiya kyau na albarkar ƙasar a cikin tayakanku, ku kai wa mutumin tsaraba, da ɗan man shafawa na ƙanshi da ‘yar zuma, da kayan yaji, da ƙaro, da tsabar citta, da ɓaure. 12Ku ɗauki kuɗi riɓi biyu a hannunku, ku kuma ɗauki kuɗin da aka mayar muku a tayakanku, kila kuskure ne aka yi. 13Ku kuma ɗauki ɗan’uwanku, ku tashi ku sāke komawa wurin mutumin. 14Allah Maɗaukaki ya ba ku tagomashi a gun mutumin, har da zai sakar muku da ɗaya ɗan’uwan nan naku tare da Biliyaminu kuma. Ni kuwa idan na yi rashi, na rasa ke nan.”15Sai mutane suka ɗauki tsarabar, suka kuma ɗauki riɓin kuɗin a hannunsu tare da Biliyaminu. Suka tashi suka gangara zuwa Masar, suka shiga wurin Yusufu. 16Sa’ad da Yusufu ya ga Biliyaminu tare da su, ya faɗa wa mai hidimar gidansa, ya ce, “Ka shigar da mutanen cikin gida, ka yanka dabba ka shirya, gama mutanen za su ci abincin rana tare da ni.” 17Mutumin kuwa ya yi kamar yadda Yusufu ya faɗa masa, ya shigo da mutanen a gidan Yusufu.18Mutanen suka tsorata sabili da an kawo su a cikin gidan Yusufu, sai suka ce, “Ai, saboda kuɗin da aka mayar mana cikin tayakanmu a zuwanmu na farko, shi ya sa aka shigar da mu, domin ya nemi hujja a kanmu, ya fāɗa mana, ya maishe mu bayi, ya kuma ƙwace jakunanmu.” 19Sai suka hau wurin mai hidimar gidan Yusufu, suka yi magana da shi a ƙofar gida, 20suka ce, “Ya shugaba, mun zo a karo na farko sayen abinci, 21amma da muka isa zango muka buɗe tayakanmu sai ga kuɗin kowannenmu cif cif bakin taikinsa, don haka ga su a hannunmu, mun sāke komowa da su, 22ga waɗansu kuɗin kuma mun riƙo a hannunmu, mun gangaro mu ƙara sayen abinci. Ba mu san wanda ya sa kuɗin nan namu a tayakanmu ba.”23Ya amsa ya ce, “Salama na tare da ku, kada ku ji tsoro, Allahnku da Allah na mahaifinku ne kaɗai ya sa muku dukiyar cikin tayakanku. Na karɓi kuɗinku.” Sai ya fito musu da Saminu.24Da mutumin ya kawo su gidan Yusufu, ya ba su ruwa, suka kuwa wanke ƙafafunsu, sa’an nan kuma ya bai wa jakunansu tauna, 25sai suka shirya tsarabar, domin Yusufu yana zuwa da tsakar rana, saboda sun ji, wai zai ci abinci a nan. 26Sa’ad da Yusufu ya koma gida, suka kawo tsarabar da suka riƙo masa cikin gida, suka sunkuya har ƙasa a gabansa. 27Ya tambayi lafiyarsu ya ce, “Mahaifinku yana lafiya, tsohon nan da kuka yi magana a kansa? Yana nan da rai?”28Sai suka amsa, “Bawanka, mahaifinmu yana lafiya, har yanzu yana da rai.” Suka sunkuya suka yi masa mubaya’a.29Sai ya ɗaga idanunsa, ya ga ɗan’uwansa Biliyaminu, ɗan da mahaifiyarsa ta haifa, ya ce, “Wannan shi ne auta naku, wanda kuka yi mini magana a kansa? Allah ya yi maka alheri ɗana!” 30Da Yusufu ya ji kamar zai yi kuka sabili da zuciyarsa tana begen ɗan’uwansa, sai ya gaggauta ya nemi wurin yin kuka. Ya shiga ɗakinsa, a can ya yi kuka. 31Sa’an nan ya wanke fuskarsa, ya fito ya ɗaure, ya umarta a kawo abinci. 32Aka hidimta masa shi kaɗai, su kuma su kaɗai, domin Masarawa ba sukan ci abinci tare da Ibraniyawa ba, gama wannan abin ƙyama ne ga Masarawa. 33Aka zaunar da ‘yan’uwan Yusufu a gaban Yusufu bisa ga shekarunsu na haihuwa, daga babba zuwa ƙarami. ‘Yan’uwan kuwa suka duddubi juna suna mamaki. 34Daga teburin da yake a gabansa aka riƙa ɗibar rabonsu ana kai musu, amma rabon Biliyaminu ya yi biyar ɗin na kowannensu. Suka kuwa sha, suka yi murna tare da shi.

Finjalin Yusufu a Taikin Biliyaminu

1Yusufu ya umarci mai hidimar gidansa, ya ce, “Cika tayakan mutanen nan da abinci iyakar yadda za su iya ɗauka, ka kuma sa kuɗin kowanne a bakin taikinsa, 2ka sa finjalina na azurfa a bakin taikin autan, tare da kuɗinsa na hatsin.” Sai ya yi kamar yadda Yusufu ya faɗa masa. 3Gari na wayewa aka sallami mutanen da jakunansu. 4Tun ba su riga suka yi nisa da garin ba, Yusufu ya ce wa mai hidimar gidansa, “Tashi, ka bi mutanen, in ka iske su ka ce musu, 5‘Don me kuka rama alheri da mugunta? Don me kuka sace mini finjalina na azurfa? Da shi ne mai gidana yake sha, da shi ne kuma yake yin istihara. Kun yi kuskure da kuka yi haka.’ ”6Lokacin da ya iske su sai ya yi musu waɗannan maganganu. 7Suka ce masa, “Don me shugabana zai faɗi irin waɗannan maganganu? Allah ya sawwaƙe da bayinka za su aikata irin wannan! 8Ga shi, kuɗin da muka samu a bakin tayakanmu, mun komo maka da su tun daga ƙasar Kan’ana, ta yaya fa, za mu saci azurfa ko zinariya daga gidan maigidanka? 9Daga cikinmu barorinka, duk wanda aka sami abin a wurinsa, bari ya mutu, mu kuwa mu zama bayinka, ranka ya daɗe.” 10Ya ce, “Bari ya zama kamar yadda kuka faɗa, shi wanda aka sami abin a wurinsa zai zama bawana, sauranku kuwa za ku tafi lafiya.” 11Nan da nan kowa ya saukar da taikinsa ƙasa, kowa kuwa ya buɗe taikinsa. 12Ya bincika, ya fara daga babba zuwa ƙarami, sai aka iske finjalin a cikin taikin Biliyaminu. 13Suka kyakkece rigunansu, kowannensu kuwa ya yi wa jakinsa labtu suka koma birnin.14Sa’ad da Yahuza da ‘yan’uwansa suka zo gidan Yusufu, suka iske yana nan har yanzu, sai suka fāɗi ƙasa a gabansa. 15Yusufu ya ce musu, “Wane abu ke nan kuka aikata? Ba ku sani ba, mutum kamata yakan yi istihara?”16Sai Yahuza ya amsa, “Me za mu ce wa shugabana? Wace magana za mu yi? Ko kuwa, ta yaya za mu baratar da kanmu? Allah ne ya tona laifin bayinka, ga mu, mu bayin shugabana ne, da mu da shi wanda aka sami finjalin a wurinsa.”17Amma Yusufu ya ce, “Allah ya sawwaƙe mini da in yi haka! Sai shi wanda aka sami finjalin a hannunsa, shi zai zama bawana, amma ku, ku yi tafiyarku lafiya zuwa wurin mahaifinku.”Yahuza Ya Yi Gōdō domin Biliyaminu18Yahuza ya je wurin Yusufu ya ce, “Ya shugabana, ina roƙonka, ka bar bawanka ya yi magana a kunnuwanka, kada kuma ka bar fushinka ya yi ƙuna bisa bawanka, gama daidai da Fir’auna kake. 19Ranka ya daɗe, ka tambaye mu, ka ce, ‘Kuna da mahaifi ko ɗan’uwa?’ 20Sai muka amsa, ranka ya daɗe, muka ce, ‘Muna da mahaifi, tsoho, da ɗan tsufansa, auta, wanda ɗan’uwansa ya rasu, shi kaɗai ya ragu daga cikin mahaifiyarsa, mahaifinsa kuwa yana ƙaunarsa.’ 21Sai ka ce wa barorinka, ‘Ku kawo shi wurina, don in gan shi.’ 22Ranka ya daɗe, muka kuwa ce, ‘Saurayin ba zai iya rabuwa da mahaifinsa ba, gama in ya rabu da mahaifinsa, mahaifinsa zai mutu.’ 23Sai ka amsa wa barorinka, ka ce, ‘In ba autanku ya zo tare da ku ba, ba za ku ƙara ganin fuskata ba.’24“Sa’ad da muka koma a wurin baranka, mahaifinmu, muka mayar masa da dukan abin da ka ce. 25Don haka sa’ad da mahaifinmu ya ce, ‘Koma, ku sayo mana ɗan abinci,’ 26sai muka ce, ‘Ba za mu iya gangarawa ba, amma idan autanmu zai tafi tare da mu, za mu gangara, gama ba dama mu ga fuskar mutumin sai ko autanmu yana tare da mu.’ 27Sa’an nan baranka, mahaifinmu, ya ce mana, ‘Kun sani ‘ya’ya biyu matata ta haifa mini, 28ɗayan ya bar ni, na kuwa ɗauka, hakika an yayyage shi kaca kaca, gama ban ƙara ganinsa ba. 29In kuka ɗauke wannan kuma daga gare ni, mai yiwuwa ne a kashe shi, to, za ku sa baƙin ciki ya ishe ni, da tsufana, har ya kashe ni.’30-31“Domin haka kuwa, yanzu, idan na koma wurin baranka, mahaifina, ba tare da saurayin ba, in har bai ga yaron tare da ni ba, zai mutu, gama ransa ya shaƙu da saurayin, barorinka kuwa za su sa baranka, mahaifinmu, ya mutu cikin baƙin ciki, da tsufansa. 32Gama ni baranka na ɗauki lamunin saurayin wurin mahaifinsa da cewa, ‘In ban komo maka da shi ba, sai alhakinsa ya zauna a kaina a gaban mahaifina duka raina.’ 33Domin haka fa, ina roƙonka, bari ni baranka in zama bawa gare ka, shugabana, a maimakon saurayin a bar saurayin ya koma tare da ‘yan’uwansa. 34Gama yaya zan iya komawa wurin mahaifina, in saurayin ba ya tare da ni? Ina jin tsoron ganin ɓarnar da za ta auko wa mahaifina.”

Yusufu ya Bayyana Kansa ga ‘Yan’uwansa

1  Yusufu ya kasa daurewa a gaban dukan waɗanda suke a tsaye kusa da shi, sai ya ta da murya ya ce, “Kowa ya ba mu wuri.” Saboda haka ba mutumin da ya tsaya a wurin sa’ad da Yusufu ya bayyana kansa ga ‘yan’uwansa. 2Ya yi kuka da ƙarfi, har Masarawa suka ji, labarin kuwa ya kai gidan Fir’auna. 3Yusufu kuwa ya ce wa ‘yan’uwansa, “Ni ne Yusufu. Mahaifina yana da rai har yanzu?” Amma ‘yan’uwansa ba su iya ba shi amsa ba, gama sun firgita a gabansa. 4Yusufu ya ce wa ‘yan’uwansa. “Ku matso kusa da ni, ina roƙonku.” Suka matso kusa. Sai ya ce, “Ni ne ɗan’uwanku, Yusufu, wanda kuka sayar zuwa Masar. 5Yanzu fa, kada ku damu ko kuwa ku ji haushin kanku domin kun sayar da ni a nan, gama Allah ne ya aike ni a gabanku don in ceci rai. 6Gama shekara biyu ke nan da ake yunwa a ƙasar, amma da sauran shekara biyar masu zuwa da ba za a yi noma ko girbi ba. 7Allah kuwa ya aike ni a gabanku, domin in cetar muku da ringi a duniya, in kuma rayar muku kuɓutattu masu yawa. 8Don haka, ba ku kuka aiko ni nan ba, amma Allah ne, shi ne kuwa ya sa in zama uba ga Fir’auna, da shugaban gidansa duka, mai mulki kuma bisa ƙasar Masar duka.9  “Ku gaggauta, ku hau zuwa wurin mahaifina ku ce masa, ‘Ga abin da Yusufu ɗanka ya ce, “Allah ya maishe ni shugaban Masar duka, ka gangaro wurina kada ka yi wata wata. 10Za ka zauna a ƙasar Goshen, za ka zauna kusa da ni, kai da ‘ya’yanka da jikokinka, da garkunan awaki da na tumaki, da garkunanka na shanu, da dukan abin da kake da shi. 11A nan zan cishe ka, gama akwai sauran shekara biyar masu zuwa na yunwa, don kada ka tsiyace, kai da iyalinka, da duk wanda yake tare da kai.” ’ 12Yanzu, da idanunku kun gani, idanun ɗan’uwana Biliyaminu kuma sun gani, cewa bakina ne yake magana da ku. 13Ku faɗa wa mahaifina dukan darajar da nake da ita a Masar da dukan abin da kuka gani. Ku gaggauta ku gangaro mini da mahaifina a nan.”14Sai Yusufu ya rungumi ɗan’uwansa Biliyaminu ya yi ta kuka, Biliyaminu ma ya yi kuka a bisa kafaɗun Yusufu. 15Ya sumbaci ‘yan’uwansa duka, ya yi kuka bisansu, bayan wannan sai ‘yan’uwansa suka yi taɗi da shi.16Sa’ad da labari ya kai gidan Fir’auna cewa, “’Yan’uwan Yusufu sun zo,” abin ya yi wa Fir’auna da fādawansa daɗi ƙwarai.17Sai Fir’auna ya ce wa Yusufu, “Ka faɗa wa ‘yan’uwanka su yi wannan, ‘Ku yi wa dabbobinku laftu ku koma a ƙasar Kan’ana. 18Ku ɗauko mahaifinku da iyalanku, ku zo wurina, ni kuwa zan ba ku yankin ƙasa mafificiya a Masar, za ku ci moriyar ƙasar.’ 19Ka kuma umarce su ka ce, ‘Ku ɗauki kekunan shanu daga ƙasar Masar domin ‘yan ƙanananku da matanku, ku ɗauko mahaifinku, ku zo. 20Kada ku damu da kayayyakinku, gama abin da yake mafi kyau duka a ƙasar Masar naku ne.’ ”21Haka kuwa ‘ya’yan Isra’ila suka yi. Yusufu kuma ya ba su kekunan shanu bisa ga umarnin Fir’auna, ya ba su guzuri don hanya. 22Ga kowane ɗayansu ya ba da rigar ado, amma ga Biliyaminu ya ba da azurfa ɗari uku, da rigunan ado biyar. 23Ga mahaifinsa kuwa ya aika da jakai goma ɗauke da kyawawan abubuwa na Masar, da jakai mata goma ɗauke da tsaba, da kuma abinci da guzurin hanya saboda mahaifinsa. 24Ya sallami ‘yan’uwansa. Da suna shirin tashi, sai ya ce musu, “Kada ku yi faɗa a hanya.”25Suka haura daga Masar, suka zo ƙasar Kan’ana zuwa wurin Yakubu mahaifinsu. 26Suka ce masa, “Har yanzu Yusufu yana nan da rai, shi ne kuwa mai mulki bisa ƙasar Masar duka.” Sai gabansa ya fāɗi, domin bai gaskata su ba.27Amma sa’ad da suka faɗa masa jawaban Yusufu duka, waɗanda ya faɗa musu, sa’ad da kuma ya ga kekunan shanun da Yusufu ya aiko don a ɗauke shi, sai ruhun mahaifinsu Yakubu ya farfaɗo. 28Isra’ila ya ce, “I, ya isa, ɗana Yusufu yana da rai har yanzu. Zan tafi in gan shi kafin in mutu.”

Yakubu da Iyalinsa suka Tafi Masar

1Isra’ila ya kama tafiyarsa da dukan abin da yake da shi. Ya zo Biyer-sheba, ya kuwa ba da hadayu ga Allah na mahaifinsa Ishaku. 2Sai Allah ya yi magana cikin wahayin dare, ya ce, “Yakubu.”Ya amsa ya ce, “Na’am.”3Sai ya ce, “Ni ne Allah, Allah na mahaifinka, kada ka ji tsoron zuwa Masar, gama a can zan maishe ka babbar al’umma. 4Ni kuwa zan gangara tare da kai zuwa Masar, ni kuma zan sāke haurowa tare da kai. Lokacin mutuwarka za ka mutu a hannun Yusufu.”5Sai Yakubu ya tashi daga Biyer-sheba, ‘ya’yan Isra’ila maza kuwa suka ɗauki mahaifinsu Yakubu, da ‘yan ƙananansu da matansu a cikin kekunan shanun da Fir’auna ya aika a ɗauko su. 6 Suka kuma kora shanunsu, suka ɗauki kayayyakinsu waɗanda suka samu a ƙasar Kan’ana, suka iso Masar, Yakubu da zuriyarsa duka, 7’ya’yansa maza da jikokinsa maza tare da shi, ‘ya’yansa mata, da jikokinsa mata, ya kawo zuriyarsa dukka zuwa ƙasar Masar.8Waɗannan su ne sunayen ‘ya’ya maza na Isra’ila, wato Yakubu, waɗanda suka iso Masar. Ra’ubainu, ɗan farin Yakubu. 9’Ya’yan Ra’ubainu, maza kuwa, su ne Hanok, da Fallu, da Hesruna, da Karmi. 10’Ya’yan Saminu, maza, su ne Yemuwel, da Yamin, da Ohad, da Yakin, da Zohar, da Shawul ɗan wata Bakan’aniya. 11’Ya’yan Lawi, maza, su ne Gershon, da Kohat, da Merari. 12’Ya’yan Yahuza, maza, su ne Er, da Onan, da Shela, da Feresa, da Zera, (amma Er da Onan suka rasu a ƙasar Kan’ana). ‘Ya’yan Feresa, maza kuwa, su ne Hesruna da Hamul. 13’Ya’yan Issaka, maza, su ne Tola, da Fuwa, da Yashub, da Shimron. 14’Ya’yan Zabaluna, maza, su ne Sered, da Elon, da Yaleyel, 15(waɗannan su ne ‘ya’yan Lai’atu, maza, waɗanda ta haifa wa Yakubu cikin Fadan-aram, da ‘ya tasa kuma Dinatu, ‘ya’yansa mata da maza duka, mutum talatin da uku ne).16’Ya’yan Gad, maza, su ne Zifiyon, da Haggi, da Shuni, da Ezbon, da Eri, da Arodi, da Areli. 17’Ya’yan Ashiru, maza, su ne Yimna, da Yishuwa, da Yishwi, da Beriya, da Sera, ‘yar’uwarsu. ‘Ya’yan Beriya, maza kuma, su ne Eber da Malkiyel. 18Waɗannan su goma sha shida, su ne zuriyar Yakubu, maza, na wajen Zilfa, wadda Laban ya bai wa Lai’atu, ‘yarsa.19’Ya’ya maza, na Rahila, matar Yakubu, su ne Yusufu da Biliyaminu. 20 Asenat ‘yar Fotifera, firist na On, ta haifa wa Yusufu Manassa da Ifraimu a ƙasar Masar. 21’Ya’yan Biliyaminu, maza, su ne Bela, da Beker, da Ashbel, da Gera, da Na’aman, da Ahiram, da Rosh, da Muffim, da Huffim, da Adar. 22Waɗannan su goma sha huɗu su ne zuriyar Yakubu, maza, na wajen Rahila.23Hushim shi ne ɗan Dan. 24’Ya’yan Naftali, maza, su ne Yazeyel, da Guni, da Yezer, da Shallum. 25Waɗannan su bakwai, su ne zuriyar Yakubu, maza, na wajen Bilha, wadda Laban ya bai wa ‘yarsa Rahila.26Mutanen Yakubu dukka da suka shiga Masar, waɗanda suke zuriyarsa ne, banda matan ‘ya’yansa, su mutum sittin da shida ne. 27 ‘Ya’yan Yusufu, maza, waɗanda aka haifa masa a Masar su biyu ne. Dukkan mutane na gidan Yakubu da suka zo Masar su saba’in.Yakubu da Iyalinsa a Masar28Isra’ila kuwa ya aiki Yahuza ya yi gaba zuwa wurin Yusufu ya faɗa masa ya sadu da shi a nuna masa Goshen. Da suka zo ƙasar Goshen, 29sai Yusufu ya kintsa karusarsa ya haura zuwa Goshen don ya taryi Isra’ila, mahaifinsa. Nan da nan da isowarsa wurinsa, ya rungume shi, ya jima yana ta kuka a kafaɗarsa. 30Isra’ila ya ce wa Yusufu, “To, bari in mutu yanzu, tun da na ga fuskarka na sani kuma kana da rai har yanzu.”31Yusufu ya ce wa ‘yan’uwansa da iyalin gidan mahaifinsa, “Zan tafi in faɗa wa Fir’auna, in ce masa, ‘’yan’uwana da iyalin gidan mahaifina, waɗanda dā yake a ƙasar Kan’ana, sun zo wurina, 32mutanen kuwa makiyaya ne, sun kuwa zo da garkunansu na awaki da na tumaki, da garkunansu na shanu, da dukkan abin da suke da shi.’ 33To, sa’ad da Fir’auna zai kira ku, ya tambaye ku, ‘Mece ce sana’arku?’ 34Sai ku ce, ‘Ranka ya daɗe, mu makiyayan shanu ne tun muna ‘yan yara har zuwa yau, da mu da kakanninmu,’ don ku sami wurin zama a ƙasar Goshen, gama kowane makiyayi abin ƙyama ne ga Masarawa.”

1Yusufu ya shiga ya yi magana da Fir’auna, ya ce

, “Mahaifina da ‘yan’uwana, da garkunansu na awaki da na tumaki, da garkunan shanu, da dukan abin da suka mallaka, sun zo daga ƙasar Kan’ana, yanzu suna ƙasar Goshen.” 2Daga cikin ‘yan’uwansa kuma ya ɗauki mutum biyar ya gabatar da su a gaban Fir’auna.3Sai Fir’auna ya ce wa ‘yan’uwan nan nasa, “Mece ce sana’arku?”Suka amsa wa Fir’auna, suka ce, “Ranka ya daɗe, mu makiyaya ne, kamar yadda iyayenmu suke.” 4Suka kuma ce wa Fir’auna, “Ranka ya daɗe, mun zo baƙunci ne cikin ƙasar, gama ba wurin kiwo domin garkunan bayinka, gama yunwa ta tsananta a ƙasar Kan’ana. Yanzu muna roƙonka, ka yarda wa bayinka su zauna a ƙasar Goshen.”5Fir’auna ya ce wa Yusufu, “Mahaifinka da ‘yan’uwanka sun zo wurinka. 6Ƙasar Masar tana gabanka. Ka zaunar da mahaifinka da ‘yan’uwanka a ƙasa mai kyau, bari su zauna a ƙasar Goshen. In kuma ka san da waɗansu waɗanda suka dace a cikinsu, ka sa su su lura da shanuna.”7Yusufu kuwa ya shigo da Yakubu mahaifinsa, ya tsai da shi a gaban Fir’auna, Yakubu kuwa ya sa wa Fir’auna albarka. 8Fir’auna kuma ya ce wa Yakubu, “Nawa ne shekarun haihuwarka?”9Yakubu ya ce wa Fir’auna, “Shekaruna na zaman baƙuncina, shekara ce ɗari da talatin, shekaruna kima ne cike kuma da wahala, ba su kuwa kai yawan shekarun kakannina ba, cikin baƙuncinsu.” 10Yakubu kuwa ya sa wa Fir’auna albarka, sa’an nan ya fita daga gaban Fir’auna. 11Sai Yusufu ya zaunar da mahaifinsa da ‘yan’uwansa, ya kuwa ba su mahalli a ƙasar Masar, cikin ƙasa mafi kyau a ƙasar Remesse, kamar yadda Fir’auna ya umarta. 12Yusufu ya bai wa mahaifinsa da ‘yan’uwansa da dukan iyalin gidan mahaifinsa abinci, bisa ga yawan ‘ya’yansu.Hidimar Yusufu a Lokacin Yunwa13A yanzu cikin ƙasar duka, ba abinci, gama yunwar ta tsananta ƙwarai, har ƙasar Masar da ƙasar Kan’ana suka matsu saboda yunwar. 14Yusufu kuwa ya ƙwalƙwale dukan kuɗin da yake akwai a ƙasar Masar da a ƙasar Kan’ana, domin hatsin da suka saya. Yusufu kuma ya kawo kuɗin cikin gidan Fir’auna. 15Sa’ad da aka kashe kuɗin da yake a Masar duka da na ƙasar Kan’ana, Masarawa duka suka zo wurin Yusufu, suka ce, “Ka ba mu abinci, don me za mu mutu a kan idonka? Gama kuɗinmu sun ƙare.”16Yusufu ya amsa, ya ce, “Ku ba da shanunku, ni kuwa zan ba ku abinci a madadin shanunku in kuɗinku sun ƙare.” 17Saboda haka suka kai wa Yusufu dabbobinsu, sai Yusufu ya ba su abinci madadin dawakai da garkunan awaki da na tumaki, da garkunan shanu da na jakai, ya tallafe su da abinci a madadin dabbobinsu duka a wannan shekara.18Sa’ad da wannan shekara ta ƙare, sai suka zo wurinsa a shekara ta biyu, suka ce masa, “Ranka ya daɗe. Ba za mu ɓoye wa shugabanmu ba cewa kuɗinmu duka mun kashe, garkunan dabbobin kuma sun zama naka. Banda jikunanmu da gonakunmu, ba kuwa abin da ya rage mana. 19Kada ka bar mu mu mutu, ka yi wata dabara! Kada ka bari mu rasa gonakinmu. Ka musaye mu da abinci, mu da gonakunmu. Mu kuwa za mu zama bayin Fir’auna, ka kuma ba mu iri domin mu rayu, kada mu mutu don kuma kada ƙasar ta zama kango.”20Ta haka Yusufu ya saya wa Fir’auna ƙasar Masar duka, gama Masarawa duka sun sayar da saurukansu, saboda yunwa ta tsananta musu. Ƙasar ta zama halaliyar Fir’auna. 21Yusufu ya mai da jama’ar bayi daga wannan kan iyaka na Masar zuwa wancan. 22Sai gonakin firistoci ne kaɗai bai saya ba, gama firistocin suna da rabo wanda Fir’auna ya yanka musu, da rabon da Fir’auna yake ba su suke zaman gari, sabili da haka ba su sayar da gonakinsu ba. 23Yusufu ya ce wa jama’ar, “Ga shi, a yau na saya wa Fir’auna ku da gonakinku. Yanzu fa, ga iri dominku, za ku shuka gonakin. 24Da haka za ku ba da kashi ɗaya cikin biyar ga Fir’auna, kashi huɗu cikin biyar kuwa ya zama naku din iri na shuka a gonakinku, don kuma abincinku, da na iyalan gidanku, da na ‘yan ƙanananku.”25Suka ce, “Ka ceci rayukanmu, in ko ya gamshe ka, ya shugaba, mā zama bayin Fir’auna.” 26Sai Yusufu ya kafa doka daga wannan rana har wa yau game da ƙasar Masar wadda ta ce, Fir’auna zai sami kashi ɗaya daga cikin biyar, sai dai gonakin firistoci kaɗai ne ba su zama na Fir’auna ba.Wasiyyar Yakubu27Ta haka fa Isra’ila ya yi zamansa a ƙasar Masar a ƙasar Goshen, suka kuwa sami mahalli a cikinta suka hayayyafa suka riɓaɓɓanya ƙwarai. 28Yakubu kuma ya zauna a ƙasar Masar shekara goma sha bakwai, don haka kwanakin Yakubu, wato shekarun ransa, shekara ce ɗari da arba’in da bakwai. 29 A sa’ad da lokaci ya gabato da Isra’ila zai mutu, ya kira ɗansa Yusufu ya ce masa, “Idan zan sami tagomashi a idonka, ka sa hannunka a ƙarƙashin cinyata, ka ɗau alkawari za ka aikata mini aminci da gaskiya. Kada ka binne ni a Masar, 30amma bari in kwanta tare da kakannina, ka ɗauke ni daga Masar, ka binne ni a makabartarsu.”Ya amsa ya ce, “Zan aikata yadda ka faɗa.”31Sai Yakubu ya ce, “Rantse mini.” Sai Yusufu ya rantse masa. Sa’an nan sai Isra’ila ya mai da kai bisa kan gadonsa.

Ayyukan Manzanni 2

.

Zuwan Ruhu Mai Tsarki
1  Da ranar Fentikos ta yi, duk suna tare a wuri ɗaya, 2farat ɗaya, sai aka ji wani amo daga sama, kamar na busowar gawurtacciyar iska, ya cika duk gidan da suke zaune. 3Sai waɗansu harsuna kamar na wuta suka bayyana a gare su, suna rarrabuwa, suna sassauka a kan ko wannensu. 4Sai duk, aka cika su da Ruhu Mai Tsarki, suka kuma fara magana da waɗansu harsuna dabam dabam, gwargwadon yadda Ruhun ya yi musu baiwar yin magana.
5To, a Urushalima a lokacin, akwai waɗansu Yahudawa masu bautar Allah daga ko’ina cikin ƙasashen duniya. 6Da jin dirin nan kuwa, taron ya haɗe, ya ruɗe, domin ko wannensu ya ji suna magana da bakin garinsu. 7Sai suka yi al’ajabi suka yi mamaki, suna cewa, “Ashe, duk masu maganar nan ba Galilawa ba ne? 8Ƙaƙa kuwa ko wannenmu yake ji da bakin garinsu ake magana? 9Ga mu kuwa, Fartiyawa, da Madayanawa, da Elamawa, da mutanen ƙasar Bagadaza, da na Yahudiya, da na Kafadokiya, da na Fantas, da na Asiya, 10da na Firijiya, da na Bamfiliya, da na Masar, da kuma na kewayen Kurane ta ƙasar Libiya, har ma da baƙi daga Roma, wato Yahudawa, da kuma waɗanda suka shiga Yahudanci, 11da kuma Karitawa, da Larabawa, duk muna ji suna maganar manyan al’amuran Allah da bakunan garuruwanmu.” 12Duk kuwa suka yi mamaki, suka ruɗe, suna ce wa juna, “Me ke nan kuma?” 13Amma waɗansu suka yi ba’a suka ce, “Ruwan inabi suka sha suka yi tatul!”
Jawabin Bitrus a Ranar Fentikos
14Amma Bitrus ya miƙe tare da sha ɗayan nan, ya ɗaga murya ya yi musu jawabi, ya ce, “Ya ku ‘yan’uwana Yahudawa da dukan mazaunan Urushalima, ku kula da wannan, ku kuma saurari maganata. 15Ai, mutanen nan ba bugaggu ba ne yadda kuke zato, tun da yake yanzu ƙarfe tare na safe ne kawai. 16Wannan, ai, shi ne abin da Annabi Yowel ya faɗa cewa,
17  “ ‘Allah ya ce,
A zamanin karshe zai zamanto zan zubo wa dukan ‘yan adam Ruhuna.
‘Ya’yanku mata da maza za su yi annabci,
Wahayi zai zo wa samarinku,
Dattawanku kuma za su yi mafarkai.
18Hakika, har ma a kwanakin nan zan zubo Ruhuna a kan bayina mata da maza,
Za su kuma yi annabci.
19Zan nuna abubuwan al’ajabi a sararin sama,
Da mu’ujizai a nan ƙasa,
Wato jini, da wuta, da kuma, hauhawan hayaƙi.
20Za a mai da rana duhu,
Wata kuma jini,
Kafin Ranar Ubangiji ta zo,
Babbar ranar nan mai girma.
21A sa’an nan ne zai zamanto kowa ya yi addu’a da sunan Ubangiji zai sami ceto.’
22“Ya ku ‘yan’uwa, Isra’ilawa, ku ji wannan magana. Yesu Banazare, mutumin da Allah ya tabbatar muku cewa shi yardajjensa ne, ta mu’ujizai, da abubuwan al’ajabi, da alamu waɗanda ya yi ta wurinsa a cikinku, kamar yadda ku kanku kuka sani, 23 shi Yesun nan fa, an ba da shi bisa ƙaddarar Allah da rigyasaninsa, ku kuwa kuka gicciye shi, kuka kashe shi, ta hannun masu zunubi. 24 Amma Allah ya tashe shi bayan ya ɓalle masa ƙangin mutuwa, domin ba shi yiwuwa mutuwa ta riƙe shi. 25Dawuda kuma ya yi faɗi a game da shi ya ce,
“ ‘Kullum hankalina yana kan Ubangiji,
Yana damana, domin kada in jijjigu.
26Saboda haka, zuciyata ta yi fari, ina farin ciki matuƙa.
Ko da yake kuma ni jiki ne, zan zauna ina sa zuciya,
27Domin ba za ka yar da raina a Hades ba,
Ba kuwa za ka yarda Mai Tsarkinka ya ruɓa ba.
28Kā sanar da ni hanyoyin rai.
Za ka cika ni da farin ciki ta zamana a zatinka.’
29“Ya ‘yan’uwa, na iya yi muku magana da amincewa a game da kakanmu Dawuda, cewa ya mutu, an binne shi, kabarinsa kuma yana nan gare mu har ya zuwa yau. 30 To, da yake shi annabi ne, ya kuma san Allah ya rantse masa, cewa zai ɗora wani daga cikin zuriya tasa kan kursiyinsa, 31sai ya hango, ya kuma yi faɗi a kan tashin Almasihu daga matattu, cewa ba za a yashe shi a Hades ba, jikinsa kuwa ba zai ruɓa ba. 32Yesun nan kam, Allah ya tashe shi daga matattu, mu kuwa duk shaidu ne ga haka. 33Da yake an ɗaukaka shi a dama ga Allah, ya kuma sami cikar alkawarin nan na baiwar Ruhu Mai Tsarki daga wurin Uba, sai ya zubo da wannan da kuke gani, kuke kuma ji. 34Ai, ba Dawuda ne ya hau Sama ba, amma shi kansa ya ce,
“ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,
Zauna a damana,
35Sai na sa ka take maƙiyanka.’
36“Don haka sai duk jama’ar Isra’ila su sakankance, cewa shi Yesun na da kuka gicciye, Allah ya mai da shi Ubangiji, da kuma Almasihu.”
37To, da suka ji haka, maganar ta soke su a zuci, suka ce wa Bitrus da sauran manzannin, “’Yan’uwa, me za mu yi?” 38Sai Bitrus ya ce musu, “Sai ku tuba, a yi wa ko wannenku baftisma, a kan kun yarda da sunan Yesu Almasihu, domin a gafarta zunubanku, za ku kuwa sami baiwar Ruhu Mai Tsarki, 39domin alkawarin nan ku aka yi wa, ku da ‘ya’yanku, da kuma dukan manisanta, wato duk waɗanda Ubangiji Allahnmu ya kira.” 40Sai ya yi ta tabbatar musu da maganganu masu yawa, yana ta yi musu gargaɗi, yana cewa, “Ku tsirar da kanku daga wannan karkataccen zamani.” 41Waɗanda suka ya na’am da maganarsa kuwa aka yi musu baftisma. A ran nan kuma suka ƙaru da mutum wajen dubu uku. 42Sai suka himmantu ga koyarwar manzanni da tarayya da juna, da gutsuttsura gurasa, da kuma yin addu’a.
Yadda Zaman Masu Bi Yake
43Sai tsoro ya kama kowa, aka kuma yi abubuwan al’ajabi da mu’ujizai da yawa ta wurin manzannin. 44 Dukan masu ba da gaskiya suna tare, suna mallakar kome nasu gaba ɗaya. 45Suka sayar da mallakarsu da kayansu, suka rarraba wa kowa kuɗin, gwargwadon bukatarsa. 46Kowace rana kuma sukan riƙa zuwa Haikali da nufi ɗaya, suna gutsuttsura gurasa a gidajensu, suna cin abinci da farin ciki ƙwarai, rai kwance, 47suna yabon Allah, suna da farin jini a wurin dukan mutane. Kowace rana kuma Ubangiji yana ƙara masu waɗanda ake ceta.

(Ayyukan Manzanni 2 2:1-47)