Skip to content

Kubawar Shari’a 28:1 – 31:29

1  “Idan kun yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, kuna aikata dukan umarnansa waɗanda nake umartarku da su yau, to, Ubangiji Allahnku zai fifita ku fiye da dukan sauran al’umma. 2Idan kun yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, dukan albarkun nan za su sauko muku, su zama naku.
3“Za ku zama masu albarka, ko kuna cikin gari, ko kuna cikin karkara.
4“’Ya’yanku za su zama masu albarka, haka nan kuma amfanin gonakinku, da ‘ya’yan dabbobinku, da ‘ya’yan shanunku, da ‘ya’yan tumakinku da awakinku.
5“Kwandunanku da makwaɓan za su yalwata ƙullunku.
6“Da albarka za ku shiga, da albarka kuma za ku fita.
7“Ubangiji zai sa ku fatattaki abokan gābanku a gabanku waɗanda suke tasar muku. Ta hanya guda za su auka muku, amma ta hanyoyi bakwai za su gudu daga gabanku.
8“Ubangiji zai sa wa abin da yake cikin rumbunanku albarka da dukan aikin hannuwanku. Zai sa muku albarka a ƙasar da yake ba ku.
9“Ubangiji zai sa ku zama tsattsarkar jama’arsa kamar yadda ya rantse muku, idan za ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin tafarkunsa. 10Dukan mutanen duniya za su gane ku na Ubangiji ne, za su ji tsoronku. 11Ubangiji zai arzuta ku ƙwarai da ‘ya’ya, da ‘ya’yan dabbobi, da amfanin gona, a ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninku zai ba ku. 12Ubangiji zai buɗe muku taskarsa ta sammai, don ya ba ƙasarku ruwa a kan kari, zai kuma sa albarka a kan dukan aikin hannuwanku. Al’ummai da yawa za su karɓi rance a wurinku, amma ku, ba za ku karɓi rance ba. 13Ubangiji zai sa ku zama kai, ba wutsiya ba. Kullum ci gaba za ku yi, ba baya ba, idan kuka yi biyayya da umarnan Ubangiji Allahnku waɗanda nake umartarku da su yau, in kun lura, kun yi aiki da su, 14idan kuma ba ku kauce zuwa dama ko hagu daga maganar da na umarce ku da ita yau ba, wato don ku bi waɗansu gumaka, ku bauta musu.”
Sakamakon Rashin Biyayya
(L.Fir 26.14-46)
15“Amma idan ba za ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku ba, ko kuwa ba ku lura kuka aikata umarnansa da dokokinsa waɗanda nake umartar da su yau ba, to, dukan waɗannan la’ana za su auko muku, su same ku.
16“La’anannu za ku zama a gari da karkara.
17“La’anannu ne kwandunanku da makwaɓan ƙullunku.
18“La’anannu ne ‘ya’yanku, da amfanin gonakinku, da ‘ya’yan shanunku, da ‘ya’yan tumakinku da na awakinku.
19“Da la’ana za ku shiga, da la’ana kuma za ku fita.
20“Ubangiji zai aiko muku da la’ana, da ruɗewa, da damuwa cikin dukan abin da za ku yi, har ya hallaka ku, ku lalace da sauri saboda mugayen ayyukanku, domin kuma kuka rabu da ni. 21Ubangiji zai aiko muku da annoba wadda za ta manne muku, ta cinye ku cikin ƙasar da za ku shiga, ku mallake ta. 22Ubangiji zai buge ku da ciwon fuka, da zazzaɓi, da ciwon kumburi, da zafi mai tsanani, da fari, da burtuntuna, da fumfuna. Waɗannan za su yi ta damunku har ku lalace. 23Samaniya da take bisa kanku za ta zama tagulla, ƙasar kuma da kuke a bisa kanta ta zama baƙin ƙarfe. 24Ubangiji zai mai da ruwan sama na ƙasarku gāri da ƙura, zai zubo muku da shi daga sama har ku hallaka.
25“Ubangiji zai sa abokan gabanku su rinjaye ku cikin yaƙi. Ta hanya guda za ku auka musu, amma ta hanyoyi bakwai za ku gudu daga gabansu. Za ku zama abin ƙi ga dukan mulkokin duniya. 26Gawawwakinku za su zama abinci ga dukan tsuntsayen sama, da namomin duniya. Ba wanda zai kore su. 27Ubangiji zai buge ku da marurai irin na Masar, da basur, da ƙazwa, da ƙaiƙayi waɗanda ba za su warke ba. 28Ubangiji kuma zai buge ku da ciwon hauka, da makanta, da rikicewar hankali. 29Da tsakar rana za ku riƙa lalubawa kamar makaho, ba za ku yi arziki cikin ayyukanku ba. Za a riƙa zaluntarku, ana yi muku ƙwace kullum, ba wanda zai cece ku.
30“Za ku yi tashin yarinya, wani ne zai kwana da ita. Za ku gina gida, wani ne zai zauna a ciki. Za ku dasa inabinku, wani ne zai girbe amfanin. 31Za a yanka sanku a idonku, amma ba za ku ci ba. Za a ƙwace jakinku ƙiri ƙiri a idonku, ba za a mayar muku da shi ba. Za a ba magabtanku tumakinku, ba wanda zai cece ku. 32A idonku za a ba da ‘ya’yanku mata da maza ga wata al’umma dabam, za ku yi ta jin kewarsu, amma a banza, gama ba ku da ikon yin kome. 33Mutanen da ba ku sani ba, su za su ci amfanin gonakinku da dukan amfanin wahalarku. Za a zalunce ku, a murƙushe ku kullum. 34Abubuwan da idanunku za su gani za su sa ku zama mahaukata. 35Ubangiji zai bugi gwiwoyinku da ƙafafunku da marurai tun daga tafin ƙafarku har zuwa ƙoƙwan kanku.
36“Ubangiji zai bashe ku, ku da sarkin da kuka naɗa wa kanku ga wata al’ummar da ku da kakanninku ba ku sani ba. Can za ku bauta wa gumakan itace da na duwatsu. 37Za ku zama abin ƙi, da abin karin magana, da abin habaici a cikin dukan mutane inda Ubangiji zai kora ku.
38“Za ku shuka iri da yawa a gonakinku, amma kaɗan za ku girbe gama fara za su cinye. 39Za ku dasa gonakin inabi, ku nome su, amma ba za ku sha ruwan inabin, ko ku tsinke ‘ya’yan inabin ba, gama tsutsa za ta cinye shi. 40Za ku sami itatuwan zaitun ko’ina cikin ƙasarku, amma ba za ku sami man da za ku shafa ba, gama ‘ya’yan za su kakkaɓe. 41Za ku haifi ‘ya’ya mata da maza, amma ba za su zama naku ba, gama za a kai su bauta. 42Ƙwari za su cinye dukan itatuwanku da dukan amfanin ƙasarku.
43“Baƙin da suke tare da ku za su yi ta ƙaruwa, ku kuwa za ku yi ta komawa baya baya. 44Za ku karɓi rance a wurinsu, su ba za su karɓi rance a wurinku ba. Su za su zama kai, ku kuwa za ku zama wutsiya.
45“Dukan waɗannan la’anoni za su auko muku, su bi ku, su same ku, har ku hallaka, domin ba ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku ba, ba ku kiyaye umarnai da dokoki da ya umarce ku da su ba. 46Za su zama alama da abin mamaki a kanku da zuriyarku har abada. 47Ba ku bauta wa Ubangiji Allahnku da murna da farin ciki ba, saboda dukan abin da ya ba ku a yalwace, 48domin haka za ku bauta wa magabtanku waɗanda Ubangiji zai turo muku. Za ku bauta musu da yunwa, da ƙishirwa, da tsiraici, da talauci. Za su sa karkiyar ƙarfe a wuyanka har su hallaka ku. 49Ubangiji zai kawo wata al’umma daga nesa, wato daga bangon duniya, mai kai sura kamar gaggafa, wadda za ta yi gāba da ku. Al’ummar da ba ku san harshenta ba, 50al’umma mai zafin hali, wadda ba ta kula da tsofaffi, ba ta kuma jin tausayin yara. 51Za ta ci shanunku da amfanin ƙasarku har ku hallaka. Ba za ta bar muku hatsi ko ruwan inabi, ko mai, ko ‘ya’yan shanunku, ko na tumaki da na awakinku ba, har ta lalatar da ku. 52Za su kewaye garuruwanku da yaƙi, har dogayen garukanku, da kagaranku waɗanda kuke dogara gare su, su rurrushe. Za su kewaye garuruwan ƙasarku da yaƙi a ƙasar da Ubangiji Allahnku ya ba ku. 53Za ku ci naman ‘ya’yanku, mata da maza, waɗanda Ubangiji Allahnku ya ba ku, saboda irin tsananin kewayewar da magabtanku suka yi muku da yaƙi. 54Nagarin mutum mai taushin zuciya wanda yake tare da ku, zai ƙi ɗan’uwansa, da matarsa, da ‘ya’yansa da suka ragu, 55domin kada ya ba wani daga cikinsu naman ‘ya’yansa wanda yake ci, gama ba abin da ya rage masa saboda irin tsananin kewayewar garuruwanku da yaƙi wanda abokan gabanku suka kawo muku. 56 Matar kirki mai taushin zuciya wadda take tare da ku wadda ba za ta sa tafin ƙafarta a ƙasa ba saboda taushin zuciyarta da kyakkyawan halinta, za ta ƙi ƙaunataccen mijinta, da ɗanta, da ‘yarta. 57A ɓoye za ta ci mahaifar da take biyo bayan ta haihu, da ‘ya’yan da za ta haifa, saboda ba ta da wani abinci lokacin da magabtanku za su kewaye garuruwanku da yaƙi mai tsanani.
58“Idan ba ku lura, ku aikata dukan maganar dokokin nan da aka rubuta a wannan littafi ba, domin ku ji tsoron sunan nan mai ɗaukaka, mai kwarjini, wato sunan Ubangiji Allahnku, 59to, Ubangiji zai aukar muku, ku da zuriyarku, da munanan masifu waɗanda ba su kawuwa, da mugayen cuce-cuce marasa warkewa. 60Sai ya sāke kawo muku cuce-cuce irin na Masar, waɗanda kuka ji tsoronsu, za su kuwa manne muku. 61Har yanzu kuma Ubangiji zai kawo muku kowace irin cuta, da kowace irin annoba, waɗanda ba a ambace su a littafin dokokin nan ba, har ku hallaka. 62Ko da yake kuna da yawa kamar taurarin sama, za ku zama ‘yan kaɗan, domin ba ku yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku ba. 63Kamar yadda Ubangiji ya ji daɗi ya arzuta ku, ya riɓaɓɓanya ku, haka nan kuma zai ji daɗi ya lalatar da ku, ya hallaka ku. Za a fitar da ku daga ƙasar da za ku shiga, ku mallaka.
64“Ubangiji zai warwatsa ku cikin dukan al’ummai daga wannan bangon duniya zuwa wancan. Can za ku bauta wa gumakan itace da na dutse waɗanda ku da kakanninku ba ku san su ba. 65Ba za ku sami zaman lafiya wurin waɗannan al’ummai ba, ko tafin ƙafarku ma ba zai sami wurin hutawa ba. Ubangiji kuma zai sa fargaba a zuciyarku, ya sa idanunku su lalace, ranku zai yi suwu. 66Kullum ranku zai kasance da damuwa, za ku zauna da tsoro dare da rana, kuna tsoron abin da zai sami ranku. 67Da safe za ku ce, ‘Da ma maraice ne.’ Da maraice kuma za ku ce, ‘Da ma safiya ce,’ saboda tsoron da yake a zuciyarku, da abubuwan da idanunku suke gani. 68Ubangiji zai komar da ku Masar cikin jiragen ruwa, ko da yake na ce ba za ku ƙara tafiya can ba. Can za ku sayar da kanku bayi mata da maza, amma ba wanda zai saye ku.
1Waɗannan ne zantuttukan alkawari da Ubangiji ya umarci Musa ya faɗa wa Isra’ilawa a ƙasar Mowab, wato banda alkawarin da ya yi da su a bisa Dutsen Horeb.
2Sai Musa ya kira dukan Isra’ilawa ya ce musu, “Ai, kun ga dukan abin da Ubangiji ya yi wa Fir’auna da barorinsa a dukan ƙasar Masar. 3Idanunku sun ga manyan wahalai, da alamu, da mu’ujizai masu girma. 4Duk da haka har wa yau Ubangiji bai ba ku zuciyar ganewa, ko idanun gani, ko kunnuwan ji ba. 5Shekara arba’in na bi da ku cikin jeji. Rigunanku da takalmanku ba su tsufa ba. 6Ba ku ci hatsi ba, ba ku kuma sha ruwan inabi ba, ko barasa, don ku sani shi ne Ubangiji Allahnku. 7 Sa’ad da kuka isa wannan wuri, sai Sihon Sarkin Heshbon, da Og, Sarkin Bashan, suka fito su yi yaƙi da mu, amma muka ci su. 8 Muku ƙwace ƙasarsu, muka ba Ra’ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa, su gāda. 9Saboda haka sai ku kiyaye, ku aikata dukan zantuttukan wannan alkawari don ku arzuta a cikin dukan abin da za ku yi.
10“Yau, ga ku nan tsaye, dukanku a gaban Ubangiji Allahnku, shugabannin kabilanku, da dattawanku, da shugabannin sojojinku, da dukan mazajen Isra’ila, 11da ‘ya’yanku, da matanku, da baƙin da suke a zangonku, da mai yi muku faskare ko mai ɗebo muku ruwa. 12Don ku ƙulla alkawari da Ubangiji Allahnku, alkawarin da Ubangiji Allahnku yake yi da ku yau. 13Don ya mai da ku jama’arsa yau, shi kuma ya zama Allahnku kamar yadda ya yi muku magana, da yadda kuma ya rantse wa kakanninku, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu. 14Ba da ku kaɗai nake yin wannan alkawari ba, 15amma da wanda ba ya nan tare da mu yau, da shi wanda yake tare da mu a nan yau, a gaban Ubangiji Allahnmu.
16“Kun sani dai yadda muka zauna a ƙasar Masar, da yadda muka yi ta ratsawa ta tsakiyar al’ummai muka wuce. 17Kun ga abubuwan da suke da su masu banƙyama, wato gumakansu na itace, da na dutse, da na azurfa, da na zinariya. 18 Kada zuciyar wani mutum, ko ta wata mata ko na wani iyali, ko wata kabila cikinku yau, ta bar bin Ubangiji Allahnku, ta koma ga bauta wa gumakan al’umman nan. Kada a iske wani tushe a cikinku mai ba da ‘ya’ya masu dafi, masu ɗaci. 19Idan wani mutum ya ji zantuttukan la’anan nan sa’an nan ya sa wa kansa albarka a zuciyarsa, yana cewa, ‘Ba abin da zai same ni ko na bi taurin zuciyata,’ wannan zai haddasa lalacewar ɗanye da busasshe gaba ɗaya. 20Ubangiji ba zai gafarce shi ba, amma fushin Ubangiji da kishinsa za su auko a kan wannan mutum, dukan la’anar kuma da aka rubuta a littafin nan za ta bi ta kansa, Ubangiji kuma zai shafe sunansa daga duniya. 21Ubangiji zai ware mutumin nan daga dukan kabilan Isra’ila, don ya hukunta shi bisa ga dukan la’anar da aka rubuta a wannan littafin dokoki.
22“Tsararraki masu zuwa nan gaba, wato ‘ya’yan da za su gaje ku, da baƙon da ya zo daga ƙasa mai nisa, za su ga annobar ƙasar, da cuce-cucen da Ubangiji zai ɗora mata. 23 Dukan ƙasa za ta zama kibritu da gishiri, ba shuka, ba amfani, ciyawa kuma ba ta tsirowa, kamar yadda Ubangiji ya kabantar da Saduma da Gwamrata, da Adam da Zeboyim, da zafin fushinsa. 24Dukan al’ummai za su ce, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi haka da wannan ƙasa? Me ya sa ya yi fushi mai tsanani haka?’ 25Sa’an nan jama’a za su ce, ‘Saboda sun yi watsi da alkawarin Ubangiji Allah na kakanninsu, wato alkawarin da ya yi da su sa’ad da ya fisshe su daga ƙasar Masar. 26Suka tafi suka bauta wa gumaka, suka yi musu sujada, gumakan da ba su san su ba, ba Ubangiji ne ya ba su ba. 27Saboda haka Ubangiji ya husata da wannan ƙasa, ya kawo mata kowace irin la’anar da aka rubuta a wannan littafin. 28Ubangiji ya tumɓuke su da zafin fushinsa, da babbar hasala, daga ƙasarsu, ya watsa su cikin wata ƙasa dabam kamar yadda suke a yau.’
29“Sanin gaibu na Ubangiji Allahnmu ne, amma abubuwan da aka bayyana namu ne, mu da ‘ya’yanmu har abada, don mu kiyaye dukan maganar dokokin nan.
1“Sa’ad da duk waɗannan abubuwa suka same ku, wato albarka da la’ana waɗanda na sa a gabanku, in kun tuna da su a zuciyarku a duk inda kuke cikin al’ummai inda Ubangiji Allahnku ya kora ku, 2kuka sāke komowa wurin Ubangiji Allahnku, ku da ‘ya’yanku kuka yi biyayya da maganarsa da zuciya ɗaya, da dukan ranku, bisa ga yadda na umarce ku yau, 3sa’an nan Ubangiji Allahnku zai komo da ku daga bauta, ya yi muku jinƙai. Zai tattaro ku daga cikin al’ummai inda ya warwatsa ku. 4Idan korarrunku suna can ƙurewar duniya, Ubangiji Allahnku zai tattaro ku daga can, ya dawo da ku. 5Ubangiji Allahnku kuma zai komo da ku cikin ƙasar da kakanninku suka mallaka, za ku mallake ta. Ubangiji zai arzuta ku, ya riɓaɓɓanya ku fiye da kakanninku. 6Ubangiji Allahnku kuma zai tausasa zuciyarku da ta ‘ya’yanku domin ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da zuciya ɗaya da dukan ranku, domin ku rayu. 7Ubangiji Allahnku kuwa zai ɗora wa magabtanku da maƙiyanku waɗanda suka tsananta muku waɗannan la’ana. 8Sa’an nan za ku yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, ku kiyaye dukan umarnan nan waɗanda na umarce ku da su yau. 9Ubangiji Allahnku zai arzuta dukan aikin hannuwanku ƙwarai, ya kuma arzutar da ‘ya’yanku da ‘ya’yan shanu, da amfanin gona, gama Ubangiji zai ji daɗi ya arzuta ku kuma yadda ya ji daɗin kakanninku, 10idan za ku yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, ku kiyaye umarnansa da dokokinsa waɗanda suke rubuce a littafin dokokin nan, idan kuma kun juyo wurin Ubangiji Allahnku da zuciya ɗaya da dukan ranku.
11“Gama wannan umarni da na yi muku yau, bai fi ƙarfinku ba, bai kuma yi nisa da ku ba. 12 Ba cikin Sama yake ba, balle ku ce, ‘Wa zai hau zuwa sama, ya sauko mana da shi don mu ji, mu kiyaye?’ 13Ba kuma a hayin teku yake ba, balle ku ce, ‘Wa zai haye mana wannan teku don ya kawo mana shi don mu ji, mu kiyaye?’ 14Amma umarnin yana kurkusa da ku, yana cikin bakinku da zuciyarku don ku kiyaye shi.
15“Ga shi yau, na sa rai da nagarta a gabanku, da mutuwa da mugunta. 16Idan kuka kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku waɗanda nake umartarku da su yau, idan kuma kun ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kuna yin tafiya cikin tafarkunsa, kuna kiyaye umarnansa, da dokokinsa, da farillansa, to, za ku rayu, ku riɓaɓɓanya, Ubangiji Allahnku kuwa zai sa muku albarka cikin ƙasar da za ku shiga, ku mallake ta. 17Amma idan zuciyarku ta kangare kun ƙi ku saurara, amma zuciyarku ta janye ku kun yi wa gumaka sujada, kuka bauta musu, 18to, ina faɗa muku yau, lalle za ku hallaka. Ba za ku yi tsawon rai a ƙasar da za ku haye Urdun ku shiga ciki don ku mallake ta ba. 19Ina kiran sama da duniya su zama shaidu a kanku yau, cewa na sa rai da mutuwa a gabanku, da albarka da la’ana. Ku zaɓi rai fa, don ku rayu, ku da zuriyarku. 20 Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi biyayya da maganarsa, ku manne masa, gama wannan shi ne ranku da tsawon kwanakinku, don ku zauna a ƙasar da Ubangiji Allahnku ya rantse zai ba kakanninku, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.”
1Sai Musa ya ci gaba da yi wa dukan Isra’ilawa magana. 2 Ya ce, “Yau shekarata ɗari da ashirin ne, ba na iya kaiwa da komowa. Ubangiji kuwa ya ce mini, ‘Ba za ka haye wannan Urdun ba.’ 3Ubangiji Allahnku shi ne zai yi gaba ya haye, ya hallaka al’umman da take gabanku don ku ci su. Joshuwa ne zai shugabance ku, ya haye kamar yadda Ubangiji ya faɗa. 4Ubangiji zai yi musu kamar yadda ya yi wa Sihon da Og, sarakunan Amoriyawa, da ƙasarsu, sa’ad da ya hallaka su. 5Ubangiji zai bashe su a gare ku. Za ku yi musu kamar yadda dā na umarce ku. 6Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tare da ku. Ba zai kunyatar da ku ba, ba kuwa zai yashe ku ba.”
7Sai Musa ya kira Joshuwa, ya yi masa magana a gaban dukan jama’ar Isra’ila, ya ce, “Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali, gama kai ne za ka kai wannan jama’a cikin ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba kakanninsu. Kai ne za ka ba su ita gādo. 8 Ubangiji kansa zai bi da kai, ba zai kunyatar da kai ba, ba kuwa zai yashe ka ba. Kada ka ji tsoro, kada kuma ka karai.”
A Karanta Dokokin Kowace Shekara ta Bakwai
9Sai Musa ya rubuta waɗannan dokoki, ya ba firistoci, ‘ya’yan Lawiyawa, waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawari na Ubangiji, da dukan dattawan Isra’ila. 10 Sai Musa ya umarce su, ya ce, “A ƙarshen kowace shekara bakwai, a lokacin da aka ƙayyade na shekarar yafewa, a lokacin Idin Bukkoki, 11sa’ad da dukan Isra’ilawa za su hallara a gaban Ubangiji Allahnku a inda zai zaɓa, to, sai ku karanta musu waɗannan dokoki su ji da kunnuwansu. 12Ku tara dukan jama’a wuri ɗaya, mata da maza, da yara, da baƙin da suke zaune tare da ku a garuruwanku domin su ji, su koyi tsoron Ubangiji Allahnku, su kuma lura su aikata dukan dokokin nan, 13domin ‘ya’yansu, waɗanda ba su sani ba, su ji, su koyi tsoron Ubangiji Allahnku dukan kwanakinku cikin ƙasar da za ku haye Urdun, ku mallaka.”
Umarnin Ƙarshe da Ubangiji Ya Yi wa Musa
14Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Lokacin rasuwarka ya yi, sai ka kira Joshuwa, ku shigo alfarwa ta sujada, don in ba shi ragamar mulki.” Sai Musa da Joshuwa suka tafi, suka shiga alfarwa ta sujada. 15Ubangiji kuwa ya bayyana a cikin alfarwar a al’amudin girgije. Al’amudin girgijen kuwa ya tsaya a ƙofar alfarwar.
16Ubangiji ya ce wa Musa, “Ga shi, za ka rasu ka tarar da kakanninka. Wannan jama’a kuwa za ta fara kaucewa daga hanya, su bi gumakan ƙasar da za su shiga, su zauna. Za su rabu da ni, su ta da alkawarina wanda na yi da su. 17A wannan rana zan husata da su ƙwarai, in rabu da su, in ɓoye musu fuskata, za a cinye su. Masifu da wahalai za su same su. Za su kuwa ce a ranar, ‘Masifun nan sun same mu domin Allahnmu ba ya tare da mu.’ 18Hakika kuwa, zan ɓoye musu fuskata sabili da muguntar da suka aikata, suka kuma bi gumaka.
19“Don haka, sai ka rubuta wannan waƙa, ka koya wa Isra’ilawa. Ka sa ta a bakinsu don waƙan nan ta zama shaida a gare ni game da Isra’ilawa. 20Sa’ad da na kawo su a ƙasar da take da yalwar abinci, wadda na rantse zan ba kakanninsu, har suka ci, suka ƙoshi, suka yi ƙiba, za su juya, su bi gumaka, su bauta musu. Za su raina ni, su tā da alkawarina. 21Sa’ad da yawan masifun nan da wahalan nan suka same su, to, waƙar nan za ta ba da shaida a kansu, gama zuriyarsu ba za ta manta da wannan waƙa ba, gama na san ƙudurin da suke yi kafin in kawo su ƙasar da na rantse zan bayar.”
22Saboda wannan sai Musa ya rubuta wannan waƙa a ranar, ya koya wa jama’ar Isra’ila.
23  Sai Ubangiji ya umarci Joshuwa ɗan Nun ya ce, “Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali, gama kai ne za ka kai jama’ar Isra’ila a ƙasar da na rantse zan ba su, ni kuma da kaina zan tafi tare da kai.”
24Sa’ad da Musa ya gama rubuta maganar dokokin nan sarai a littafin, 25sai ya umarci Lawiyawa waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, ya ce, 26“Ku ɗauki littafin dokokin nan, ku ajiye shi tare da akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku domin ya zama shaida a kanku, 27gama na san tayarwarku da taurinkanku. Tun ma ina da rai ke nan tare da ku kuka tayar wa Ubangiji, balle bayan rasuwata. 28Ku tattaro mini dattawan kabilanku da manyanku don in faɗa musu wannan magana a kunnensu, in kuma kira sama da duniya su zama shaida a kansu. 29Gama na sani bayan rasuwata za ku aikata mugunta, ku kauce daga hanyar da na umarce ku. Masifa za ta auko muku a kwanaki masu zuwa saboda za ku aikata mugunta a gaban Ubangiji, za ku tsokani fushinsa da aikin hannuwanku.”