Alamar Ibrahim – Qur’an | Alamar Ibrahim – Taurat (Farawa 12: 1-7) |
Surat 3:84
Ka ce: “Mun yi ĩmãni da Allah kuma da abin da aka saukar mana da abin da aka saukar wa Ibrãhĩma da Isma’ĩla da Is’hãƙa da Yãƙũba da jĩkõki, da abin da aka bai wa Mũsã da ĩsã da annabãwa daga Ubangijinsu, bã mu bambantãwa a tsakãnin kõwa daga gare su. Kuma mũ, zuwa gare Shi mãsu sallamãwa ne.” Surat 4:54 (The Women) Ko suna hãsadar mutãne ne a kan abin da Allah Ya bã su daga falalarSa? To, lalle ne, Mun bai wa gidan Ibrãhĩm Littãfida hikima kuma Mun bã su mulki mai girma. |
1 Ana nan sai Ubangiji ya ce wa Abram, “Ka fita daga ƙasarka, da danginka, da gidan mahaifinka zuwa ƙasar da zan nuna maka. 2Zan kuwa maishe ka al’umma mai girma, zan sa maka albarka, in sa ka ka yi suna, domin ka zama sanadin albarka. 3 Waɗanda suka sa maka albarka zan sa musu albarka, amma zan la’anta waɗanda suka la’anta ka. Dukan al’umman duniya za su roƙe ni in sa musu albarka kamar yadda na sa maka.”
4Abram kuwa ya kama hanya bisa ga faɗar Ubangiji, Lutu kuma ya tafi tare da shi, Abram yana da shekara saba’in da biyar sa’ad da ya yi ƙaura daga Haran. 5Abram kuwa ya ɗauki matarsa Saraya da Lutu, ɗan ɗan’uwansa, da dukan dukiyarsu, da dukan mallakarsu waɗanda suka tattara a Haran.
Sa’ad da suka kai ƙasar Kan’ana, 6Abram ya ratsa ƙasar zuwa Shekem, wurin itacen oak na More. A lokacin nan Kan’aniyawa suke a ƙasar. 7 Sai Ubangiji ya bayyana ga Abram, ya ce, “Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa.” Sai ya gina bagade gagina bagade ga Ubangiji, wanda ya bayyana gare shi
|