Skip to content
Alamar Ibrahim (Kashi Na 2) – Qur’an Alamar Ibrahim (Kashi Na 2) – Taurat

Suratut 37: 83-84,99-101 (AL-ṢAFFĀT).

83. Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake.

84. A lõkacin da ya je wa dangijinsa da zũciya kuɓutacciya.

99. Kuma (Ibrahĩm] ya ce: “Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni.”

100. “Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne.”

101. Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro mai haƙuri.

Farawa 15:1-6

1Bayan waɗannan al’amura, maganar Ubangiji ta zo ga Abram cikin wahayi cewa, “Abram, kada ka ji tsoro, ni ne garkuwarka, kana da lada mai yawa.”
2Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, me za ka ba ni, ga shi kuwa, ba ni da ɗa? Ko kuwa Eliyezer na Dimashƙu ne zai gāje ni?” 3Abram kuma ya ce, “Ga shi, ba ka ba ni zuriya ba, ga shi ma wani yaron gidana ne zai gāje ni.”
4Sai ga maganar Ubangiji ta zo gare shi cewa, “Mutumin nan, ba shi zai gāje ka ba, ɗan cikinka shi zai gāje ka.” 5 Sai Ubangiji ya fito da shi waje ya ce, “Ina so ka dubi sararin sama, ka kuma ƙidaya taurari, in kana iya ƙidaya su.” Sai kuma ya ce masa, “Haka zuriyarka za ta zama.” 6 Ya amince da Ubangiji, Ubangiji kuwa ya lasafta wannan adalci ne a gare shi.