Skip to content
Alamar Ludu – Qur’ani

Alamar Lutu – Taurat

Surat 7:80-83 (AL-AʿRĀF)

80.Da Lũɗu, a lõkacin daya ce wa mutãnensa: “Shin, kunã jẽ wa alfãsha, bãbu kõwa da ya gabãce ku da ita daga halittu?”

81.“Lalle ne ku, haƙĩƙa kunã jẽ wa maza da sha’awa, baicin mata; Ã’a, kũ mutãne ne maɓarnata.”

82.Kuma bãbu abin da ya kasance jawãbin mutãnensa, fãce ɗai suka ce: “Ku fitar da su daga alƙaryarku: lalle ne sũ, wasumutãne ne mãsu da’awar tsarki!”

83.Sai Muka tsĩrar da shi, shĩ da iyãlansa, fãce matarsa, ta kasance daga mãsu wanzuwa.

84.Kuma Muka yi ruwa a kansu da wani irin ruwa; Sai ka dũba yadda ãƙibar mãsu laifi ta kasance!

 Surat 11:77-83 (The HŪD)

77.Kuma a lõkacin da manzanninMu suka je wa Lũɗu aka ɓãta masa rai game da su, ya, ƙuntata rai sabõda su. Ya ce: “Wannan yini ne mai tsananin masĩfa.”

78.Kuma mutãnensa suka je masa sunã gaggãwa zuwa gare shi, kuma a gabãni, sun kasance sunã aikatãwar mũnãnan ayyuka. Ya ce: “Yã mutãnẽna! waɗannan, ‘yã’yã na sũ ne mafiya tsarki a gare ku. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku wulãkantã ni a cikin bãƙĩna. Shin, bãbu wani namiji shiryayye daga gare ku?”

79.Suka ce: “Lalle, haƙĩƙa kã sani, bã mu da wani hakki a cikin ‘ya’yanka, kuma lalle kai haƙĩƙa, kanã sane da abin da muke nufi.”

80.Ya ce: “Dã dai inã da wani ƙarfi game da ku, kõ kuwa inã da gõyon bãya daga wani rukuni mai ƙarfi?”

81.(Manzannin) Suka ce: “Yã Lũɗu! Lalle mũ, manzannin Ubangijinka ne. Bã zã su iya sãduwa zuwa gare ka ba. Sai ka yi tafiyarka a wani yankin dare da iyãlinka, kuma kada wani daga gare ku ya waiwaya fãce mãtarka. Lalle ne abin da ya same su mai sãmunta ne. Lalle wa’adinsu lõkacin sãfiya ne. Shin lõkacin sãfiya bã kusa ba ne?”

82.Sa’an nan a lõkacin da umurninMu ya je, Muka sanya na samanta ya zama na ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu a kanta (ƙasar Lũɗu) daga taɓocũrarre.

83.Alamtacce a wurin Ubangijinka. Kuma ita (ƙasar Lũɗu) ba ta zama mai nĩsa ba daga azzãlumai (kuraishãwa).

Genesis 19

1Mala’ikun nan biyu kuwa suka isa Saduma da maraice, Lutu kuwa yana zaune a ƙofar Saduma. Sa’ad da Lutu ya gan su sai ya miƙe ya tarye su. Sai ya yi ruku’u a gabansu. 2ya ce, “Iyayengijina, ina roƙonku ku ratse zuwa gidan baranku, ku kwana, ku wanke ƙafafunku, da sassafe kuma sai ku kama hanyarku.”
Suka ce, “A’a, a titi za mu kwana.” 3Amma ya nace musu ƙwarai, sai suka ratse suka shiga gidansa, ya shirya musu liyafa, ya toya musu abinci marar yisti, suka ci.
4Amma kafin su shiga barci, mutanen birnin Saduma, samari da tsofaffi, dukan mutane gaba ɗaya suka kewaye gidan. 5 Suka kira Lutu suka ce, “Ina mutanen da suka zo wurinka da daren nan? Fito mana da su waje, don mu yi luɗu da su.”
6Lutu ya fita daga cikin gida ya rufe ƙofar a bayansa ya je wurin mutane, 7ya ce, “Ina roƙonku ‘yan’uwana, kada ku aikata mugunta haka. 8Ga shi, ina da ‘ya’ya mata biyu waɗanda ba su san namiji ba, bari in fito muku da su waje, ku yi yadda kuka ga dama da su, sai dai kada ku taɓa mutanen nan ko kaɗan, gama sun shiga ƙarƙashin inuwata.”
9Amma suka ce, “Ba mu wuri!” Suka kuma ce, “Wannan mutum ya zo baƙunci ne, yanzu kuma zai zama alƙali! Yanzu za mu yi maka fiye da yadda za mu yi musu.” Sai suka tutture Lutu suka matsa kusa don su fasa ƙofar. 10Amma baƙin suka miƙa hannunsu, suka shigar da Lutu cikin gida inda suke, suka rufe ƙofa. 11 Sai suka bugi mutanen da suke ƙofar gidan da makanta, ƙanana da manya duka, har suka gajiyar da kansu suna laluba inda ƙofa take.
Lutu ya Bar Saduma
12Mutanen suka ce wa Lutu, “Kana da wani naka a nan? Ko surukai, ko ‘ya’ya mata da maza, ko dai kome naka da yake cikin birnin? Fito da su daga wurin, 13gama muna gab da hallaka wurin nan, domin kukan da ake yi a kan mutanen ya yi yawa a gaban Ubangiji. Ubangiji kuwa ya aiko mu, mu hallaka birnin.”
14Sai Lutu ya fita ya faɗa wa surukansa waɗanda za su auri ‘ya’yansa mata, “Tashi, ku fita daga wannan wuri, gama Ubangiji yana gab da hallaka birnin.” Amma sai surukansa suka aza wasa yake yi.
15Sa’ad da safiya ta gabato, mala’ikun suka hanzarta Lutu, suna cewa, “Tashi, ka ɗauki matarka da ‘ya’yanka biyu mata da suke nan, don kada a shafe ku saboda zunubin birnin.” 16Amma da ya yi ta ja musu rai, sai mutanen suka kama hannunsa, da na matarsa, da na ‘ya’yansa biyu mata, saboda jinƙan da Ubangiji ya yi masa, suka fitar da shi suka kai shi a bayan birnin. 17Sa’ad da suka fitar da shi, suka ce, “Ka gudu domin ranka, kada ka waiwaya baya, ko ka tsaya ko’ina cikin kwari, gudu zuwa tuddai domin kada a hallaka ka.”
18Sai Lutu ya ce musu, “A’a, ba haka ba ne iyayengijina, 19ga shi, baranka ya sami tagomashi a idonka, ka kuwa nuna mini babban alheri da ka ceci raina, amma ba zan iya in kai tuddan ba, kada hatsarin ya same ni a hanya, in mutu. 20Ga ɗan gari can ya fi kusa inda zan gudu in fake. Bari in gudu zuwa can, in tsirar da raina.”
21Sai ya ce masa, “Na yarda da abin da ka ce, ba zan hallakar da garin da ka ambata ba. 22Gaggauta, ka gudu zuwa can, ba zan yi kome ba sai ka isa wurin.” Domin haka aka kira sunan garin Zowar.
Halakar Saduma da Gwamrata
23Da hantsi Lutu ya isa Zowar. 24 Sai Ubangiji ya yi ta zuba wa Saduma da Gwamrata wutar kibritu daga sama, 25ya hallakar da waɗannan birane, da dukan kwarin, da dukan mazaunan biranen, da tsire-tsire. 26 Amma matar Lutu da take bin bayansa ta waiwaya, sai ta zama surin gishiri.