Skip to content

Matiyu 21:23 – 23:39

Tambaya Game da Mulkin Yesu

23Ya shiga Haikali yana cikin koyarwa, sai manyan firistoci da shugabannin jama’a suka zo wurinsa, suka ce, “Da wane izini kake yin abubuwan nan, wa ya ba ka izinin?” 24Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. In kun ba ni amsa, ni ma sai in gaya muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan. 25To, baftismar da Yahaya ya yi, daga ina take? Daga Sama take, ko kuwa ta mutum ce?” Sai suka yi ta muhawwara da juna, suna cewa, “In muka ce, ‘Daga Sama take,’ sai ya ce mana, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’ 26In kuwa muka ce, ‘Ta mutum ce,’ ai, muna jin tsoron jama’a, don duk kowa ya ɗauki Yahaya a kan annabi ne.” 27Sai suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Shi kuma ya ce musu, “Haka ni kuma ba zan faɗa muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan ba.”
Misali na Mai ‘Ya’ya Biyu Maza
28“To, me kuka gani? An yi wani mutun mai ‘ya’ya biyu maza. Ya je wurin na farkon, ya ce, ‘Ɗana, yau je ka ka yi aiki a garkar inabi.’ 29Sai ya ce, ‘Na ƙi.’ Amma daga baya sai ya tuba, ya tafi. 30Sai ya je gun na biyun ya faɗa masa haka. Shi kuwa ya amsa ya ce, ‘To, za ni, baba,’ amma bai je ba. 31To, wane ne a cikin su biyun ya yi abin da ubansu yake so?” Sai suka ce, “Na farkon.” Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga Mulkin Allah. 32 Ga shi, Yahaya ya zo ya bayyana muku hanyar adalci, ba ku gaskata shi ba. Amma masu karɓar haraji da karuwai sun gaskata shi, duk da ganin haka kuma, daga baya ba ku tuba kun gaskata shi ba.”
Misali na Manoman da Suka Yi Sufurin Garkar Inabi
33  “To, ga kuma wani misali. An yi wani maigida da ya yi garkar inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabi a ciki, ya kuma gina wata ‘yar hasumiyar tsaro. Ya ba waɗansu manoma sufurin garkar, sa’an nan ya tafi wata ƙasa. 34Da kakar inabi ta kusa, sai ya aiki bayinsa wurin manoman nan su karɓo masa gallar garkar. 35Manoman kuwa suka kama bayinsa, suka yi wa ɗaya dūka, suka kashe ɗaya, suka kuma jajjefi ɗaya. 36Har wa yau ya sāke aiken waɗansu bayi fiye da na dā, suka kuma yi musu haka. 37Daga baya sai ya aiki ɗansa gare su, yana cewa, ‘Sā ga girman ɗana.’ 38Amma da manoman suka ga ɗan, suka ce wa juna, ‘Ai, wannan shi ne magajin, ku zo mu kashe shi, gādonsa ya zama namu.’ 39Sai suka kama shi, suka jefa shi bayan shinge, suka kashe shi. 40To, sa’ad da ubangijin garkar nan ya zo, me zai yi wa manoman nan?” 41Sai suka ce masa, “Zai yi wa mutanen banzan nan mugun kisa, ya ba waɗansu manoma sufurinta, waɗanda za su riƙa ba shi gallar garkar a lokacin nunanta.”
42  Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karantawa a Littattafai ba? cewa,
“ ‘Dutsen da magina suka ƙi,
Shi ne ya zama mafificin dutsen gini.
Wannan aikin Ubangiji ne,
A gare mu kuwa abin al’ajabi ne.’
43“Domin haka ina gaya muku, za a karɓe Mulkin Allah daga gare ku, a bai wa wata al’umma wadda za ta ba da amfani nagari. 44Kowa ya faɗo a kan dutsen nan, sai ya ragargaje. Amma wanda dutsen nan ya faɗa wa, niƙe shi zai yi kamar gari.”
45Da manyan firistoci da Farisiyawa suka ji misalan nan da ya yi, sai suka gane, ashe, da su yake. 46Amma da suka nemi kama shi, suka ji tsoron jama’a, don su sun ɗauke shi shi annabi ne
Misali na Bikin Aure
1Yesu ya sāke yi musu magana da misalai ya ce, 2“Za a kwatanta Mulkin Sama da wani sarki, wanda ya yi wa ɗansa biki. 3Sai ya aiki bayinsa su kirawo waɗanda aka gayyata bikin, amma waɗanda aka gayyatar suka ƙi zuwa. 4Har wa yau ya sāke aiken waɗansu bayi, ya ce, ‘Ku gaya wa waɗanda aka gayyata, “Ga shi, na shisshirya abinci, an yanka shanuna da kiwatattun maruƙana, duk an shirya kome, ku zo bikin mana!” ’ 5Amma suka ƙi kula, suka tafi abinsu, wani ya tafi gona tasa, wani kuma cinikinsa. 6Sauran kuwa suka kame bayinsa, suka wulaƙanta su, suka kashe su. 7Sarki ya yi fushi, ya tura sojansa, suka hallaka masu kisankan nan, suka ƙone garinsu ƙurmus. 8Sa’an nan ya ce wa bayinsa, ‘Bikin fa ya shiryu sosai, amma waɗanda aka gayyata ba su cancanta ba. 9Saboda haka ku tafi ƙofofin gari, ku gayyato duk waɗanda kuka samu, su zo bikin.’ 10Sai bayin suka yi ta bin titi titi, suka tattaro duk waɗanda suka samu, mugaye da nagargaru duka, har wurin bikin ya cika maƙil da baƙi.
11“Da sarki ya shigo ganin baƙin sai ya ga wani mutum a can wanda bai sa riga irin ta biki ba. 12Sai ya ce masa, ‘Malam, ta yaya ka shigo nan ba tare da sa riga irin ta biki ba?’ Mutumin kuwa ya rasa ta cewa. 13 Sai sarki ya ce wa barorinsa, ‘Ku ɗaure shi ƙafa da hannu, ku jefa shi cikin matsanancin duhu. Nan za a yi kuka da cizon baƙi.’ 14Gama da yawa ake kira, amma kaɗan ne zaɓaɓɓu.”
Biyan Haraji ga Kaisar
15Sai Farisiyawa suka je suka yi shawara yadda za su burma shi cikin maganarsa. 16Suka aiko almajiransu wurinsa tare da waɗansu mutanen Hirudus, suka ce, “Malam, ai, mun sani kai mai gaskiya ne, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi, ba ka kuma zaɓen kowa, don ka ɗauki kowa da kowa daidai. 17To, faɗa mana abin da ka gani. Shin, daidai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa?” 18Yesu kuwa domin ya gane muguntarsu, sai ya ce musu, “Don me kuke jarraba ni? Ku munafukai! 19Ku nuna mini kuɗin harajin.” Sai suka kawo masa dinari. 20Yesu ya ce musu, “Surar nan da sunan nan na wane ne?” 21Suka ce, “Na Kaisar ne.” Sa’an nan ya ce musu, “To, sai ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.” 22Da suka ji haka, sai suka yi mamaki, suka rabu da shi, suka yi tafiyarsu.
Tambaya a kan Tashin Matattu
23  A ran nan sai waɗansu Sadukiyawa (su da suke cewa, ba tashin matattu) suka zo wurinsa, suka yi masa tambaya, 24 suka ce, “Malam, Musa dai ya ce, ‘In mutum ya mutu, bai bar na baya ba, sai lalle ɗan’uwansa ya auri matar, ya haifa wa ɗan’uwansa ‘ya’ya.’ 25To, an yi waɗansu ‘yan’uwa maza bakwai a cikinmu. Na farkon ya yi aure, da ya rasu, da yake bai haifu kuma ba, sai ya bar wa ɗan’uwansa matarsa. 26Haka ya faru ga na biyun da na ukun, har ya kai kan na bakwai ɗin. 27Bayansu duka sai matar ta rasu. 28To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu, su bakwai ɗin? Don duk sun aure ta.”
29Amma Yesu ya amsa musu ya ce, “Kun ɓăta ne, domin ba ku san Littattafai ba, ba ku kuma san ikon Allah ba. 30Domin a tashin matattu, ba a aure, ba a aurarwa, sai dai kamar mala’ikun da suke Sama ake. 31Game da tashin matattu, ashe, ba ku taɓa karanta abin da Allah ya ce muku ba? cewa, 32 ‘Ni ne Allahn Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.’ Ai, waɗanda Allah shi ne Allahnsu rayayyu ne, ba matattu ba.” 33Da jama’a suka ji haka, sai suka yi mamakin koyarwarsa.
Umarni Mafi Girma
34Amma da Farisiyawa suka ji ya ƙure Sadukiyawa, suka taru. 35Ɗaya daga cikinsu, wani masanin Attaura, ya yi masa tambaya, yana gwada shi, ya ce, 36“Malam, wane umarni ne mafi girma a cikin Attaura?” 37 Ya ce masa, “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka. 38Wannan shi ne babban umarni na farko. 39 Na biyu kuma kamarsa yake, ‘Ka ƙaunaci ɗan’uwanka kamar kanka.’ 40 A kan umarnin nan biyu duk Attaura da koyarwar annabawa suka rataya.”
Tambaya a kan Ɗan Dawuda
41Tun Farisiyawa suna tare gu ɗaya, sai Yesu ya yi musu tambaya, 42ya ce, “Yaya kuka ɗauki Almasihu? Shi ɗan wane ne?” Sai suka ce masa, “Ɗan Dawuda ne.” 43Ya ce musu, “To, yaya kuwa Dawuda, ta ikon Ruhu, ya ce da shi Ubangiji? Har ya ce,
44  “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,
Zauna a damana,
Sai na ɗora ka a kan maƙiyanka.’
45“Tun da Dawuda ya kira shi Ubangiji ne, to, ƙaƙa zai zama ɗansa?” 46Ba kuwa wanda ya iya tanka masa. Daga ran nan kuwa ba wanda ya yi ƙarfin halin sāke tambayarsa wani abu.
Yesu Ya Fallashi Malaman Attaura da Farisiyawa
1Sa’an nan Yesu ya yi wa jama’a da almajiransa magana, ya ce, 2“Malaman Attaura da Farisiyawa suka tsaya a matsayin Musa. 3Don haka, sai ku kiyaye, ku kuma aikata duk abin da suka gaya muku, amma banda aikinsu. Don suna faɗa ne, ba aikatawa. 4Sukan ɗaura kaya masu nauyi, masu wuyar ɗauka, su jibga wa mutane a kafaɗa. Amma su kansu ko tallafa musu da ɗan yatsa ba sa yi. 5 Duk ayyukansu suna yi ne don idon mutane, suna yin layunsu fantam-fantam, lafin rigunansu kuma har gwiwa. 6Suna son mazaunan alfarma a wurin biki, da mafifitan mazaunai a majami’u, 7a gaishe su a kasuwa, a kuma riƙa ce da su ‘Malam’. 8Amma ku kam, kada a ce muku ‘Malam’, domin Malaminku ɗaya ne, ku duka kuwa ‘yan’uwa ne. 9Kada ku kira kowa ‘Uba’ a duniya, domin Uba ɗaya ne yake gare ku, wanda yake cikin Sama. 10Kada kuma a kira ku ‘Shugabanni’, domin Shugaba ɗaya gare ku, wato, Almasihu. 11 Amma wanda yake babba a cikinku shi zai zama baranku. 12 Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.
13“Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kun toshe wa mutane ƙofar Mulkin Sama. Ku kanku ba ku shiga ba, kuna kuwa hana masu niyyar shiga shiga. 14[Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan ci kayan matan da mazansu sun mutu, kukan yi doguwar addu’a don ɓad da sawu. Saboda haka za a yi muku hukunci mafi tsanani.] 15Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan kewaye ƙasashe da tekuna don samun almajiri ɗaya tak, in kuwa kun samu, kukan mai da shi ɗan wuta fiye da ku, ninkin ba ninkin.
16“Kaitonku, makafin jagora, ku da kuke cewa, ‘Kowa ya rantse da Haikalin ba kome, amma duk wanda ya rantse da zinariyar Haikalin, sai rantsuwarsa ta kama shi.’ 17Ku makafi, wawaye! Wanne ya fi girma, zinariyar ce ko kuwa Haikalin da yake tsarkake zinariyar? 18Kukan ce, ‘Kowa ya rantse da bagaden hadaya, ba kome. Amma duk wanda ya rantse da sadakar da aka ɗora a kai, sai rantsuwarsa ta kama shi.’ 19Ku makafi! Wanne ya fi girma, sadakar ko kuwa bagaden hadaya da yake tsarkake sadakar? 20Don haka kowa ya rantse da bagaden hadaya, ya rantse ke nan da shi, da duk abin da yake a kansa. 21Duk kuma wanda ya rantse da Haikalin ya rantse da shi, da kuma wanda yake zaune a cikinsa. 22 Kowa kuma ya rantse da Sama, ya rantse da kursiyin Allah, da kuma wanda yake zaune a kansa.
23  “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan fitar da zakkar na’ana’a, da anise, da lafsur, amma kun yar da muhimman jigajigan Attaura, wato, gaskiya, da jinƙai, da aminci. Waɗannan ne ya kamata ku yi, ba tare da yar da sauran ba. 24Makafin jagora, kukan tace ƙwaro ɗan mitsil, amma kukan haɗiye raƙumi!
25“Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan wanke bayan ƙwarya da akushi, amma a ciki cike suke da zalunci da zari. 26Kai makahon Bafarisiye! Sai ka fara tsarkake cikin ƙwaryar da akushin don bayansu ma ya tsarkaka.
27  “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kamar kaburburan da aka shafa wa farar ƙasa kuke, masu kyan gani daga waje, daga ciki kuwa sai ƙasusuwan matattu da ƙazanta iri iri. 28Haka nan a idon mutane ku adalai ne, amma ciki sai munafunci da mugun aiki.
29“Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan yi gini a kan kaburburan annabawa, kuna ƙawata gubbobin adalai. 30Kuna cewa, ‘Da mun zauna a zamanin kakanninmu, da ba mu taya su zub da jinin annabawa ba.’ 31Ta haka kuka shaidi kanku ku ne ‘ya’yan masu kisan annabawa. 32To, sai ku cikasa ayyukan kakanninku! 33 Ku macizai! Yaya za ku tsere wa hukuncin Gidan Wuta? 34Saboda haka nake aiko muku da annabawa, da masu hikima, da masanan Attaura, za ku kashe waɗansunsu, ku gicciye waɗansu, ku kuma yi wa waɗansu bulala a majami’unku, kuna binsu gari gari kuna gwada musu azaba. 35 Don alhakin jinin dukan adalai da aka zubar a duniya yă komo a kanku, tun daga jinin Habila adali, har ya zuwa na Zakariya ɗan Berikiya, wanda kuka kashe a tsakanin Haikalin da bagaden hadaya. 36Hakika, ina gaya muku, duk wannan zai auko wa mutanen wannan zamani.”
Yesu Ya Ji Juyayin Urushalima
37“Ya mutanen Urushalima! Ya mutanen Urushalima! Masu kisan annabawa, masu jifan waɗanda aka aiko a gare ku! Sau nawa ne na so in tattaro ku kamar yadda kaza take tattara ‘yan tsakinta cikin fikafikanta, amma kun ƙi! 38 Ga shi, an bar muku gidanku a yashe! 39 Ina dai gaya muku, ba za ku ƙara ganina ba, sai ran da kuka ce, ‘Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji.’ ”