Skip to content
Kukan Azaba da Waƙar Yabo
1  Ya Allahna, ya Allahna,
Don me ka yashe ni?
Na yi kuka mai tsanani, ina neman taimako,
Amma har yanzu ba ka zo ba!
2Da rana na yi kira a gare ka, ya Allahna,
Amma ba ka amsa ba.
Da dare kuma na yi kira,
Duk da haka ban sami hutawa ba.
3Amma an naɗa ka Mai Tsarki,
Wanda Isra’ila suke yabonsa.
4Kakanninmu suka dogara gare ka,
Sun dogara gare ka, ka kuwa cece su.
5Suka yi kira gare ka, suka tsira daga hatsari,
Suka dogara gare ka, ba su kuwa kunyata ba.
6A yanzu dai ni ba mutum ba ne, tsutsa ne kawai,
Rainanne, abin ba’a ga kowa da kowa!
7  Duk wanda ya gan ni
Sai yă maishe ni abin dariya,
Suna zunɗena da harshensu suna kaɗa kai.
8  Suka ce, “Ka dogara ga Ubangiji,
Me ya sa bai cece ka ba?
Idan Ubangiji na sonka,
Don me bai taimake ka ba?”
9Kai ne ka fito da ni lafiya a lokacin da aka haife ni,
A lokacin da nake jariri ka kiyaye ni.
10Tun daga lokacin da aka haife ni nake dogara gare ka,
Kai ne Allahna tun daga ran da aka haife ni.
11Kada ka yi nisa da ni!
Wahala ta gabato,
Ba kuwa mai taimako.
12Magabta da yawa sun kewaye ni kamar bijimai,
Dukansu suna kewaye da ni,
Kamar bijimai masu faɗa na ƙasar Bashan.
13Sun buɗe bakinsu kamar zakoki,
Suna ruri, suna ta bina a guje.
14Ƙarfina ya ƙare,
Ya rabu da ni kamar ruwan da ya zube ƙasa.
Dukan gaɓoɓina sun guggulle,
Zuciyata ta narke kamar narkakken kakin zuma.
15Maƙogwarona ya bushe kamar ƙura,
Harshena kuma na liƙe wa dasashina na sama.
Ka bar ni matacce cikin ƙura.
16Ƙungiyar mugaye na kewaye da ni,
Suka taso mini kamar garken karnuka,
Suka soke hannuwana da ƙafafuna.
17Ana iya ganin ƙasusuwana duka.
Magabtana suka dube ni, suka zura mini ido.
18  Suka rarraba tufafina a tsakaninsu,
Suka jefa kuri’a a kan babbar rigata.
19Kada ka yi nisa da ni, ya Ubangiji!
Ka gaggauta ka cece ni, ya Mai Cetona!
20Ka cece ni daga takobi,
Ka ceci raina daga waɗannan karnuka.
21Ka kuɓutar da ni daga waɗancan zakoki,
Ba ni da mataimaki a gaban bijimai masu mugun hali.
22  Zan faɗa wa mutanena abin da ka yi,
Zan yabe ka cikin taronsu.
23“Ku yabe shi, ku bayin Ubangiji!
Ku girmama shi, ku zuriyar Yakubu!
Ku yi masa sujada, ku jama’ar Isra’ila!
24Ba ya ƙyale matalauta,
Ko ya ƙi kulawa da wahalarsu,
Ba ya rabuwa da su,
Amma yakan amsa lokacin da suka nemi taimako.”
25Zan yabe ka a gaban babban taron jama’a
Saboda abin da ka yi,
A gaban dukan masu yi maka biyayya,
Zan miƙa sadakokin da na alkawarta.
26Matalauta za su ci yadda suke so,
Masu zuwa wurin Ubangiji za su yabe shi,
Su arzuta har abada!
27Dukan al’ummai za su tuna da Ubangiji,
Za su zo gare shi daga ko’ina a duniya,
Dukan kabilai za su yi masa sujada.
28Ubangiji Sarki ne,
Yana mulki a kan al’ummai.
29Masu girmankai duka za su rusuna masa,
‘Yan adam duka za su rusuna masa,
Dukan waɗanda aka ƙaddara musu mutuwa.
30Zuriya masu zuwa za su bauta masa,
Mutane za su ambaci Ubangiji ga zuriya mai zuwa.
31Mutanen da ba a haifa ba tukuna, za a faɗa musu,
“Ubangiji ya ceci jama’arsa!”