Yohanna surori 13-16
1Ana nan tun kafin Idin Ƙetarewa, da Yesu ya san lokacinsa ya yi da zai tashi daga wannan duniya ya koma wurin Uba, da yake ya ƙaunaci mutanensa da suke duniya, ya ƙaunace su har matuƙa. 2Ana cikin cin abincin dare, Iblis kuwa ya riga ya sa a zuciyar Yahuza Iskariyoti ɗan Saminu yă bāshe shi. 3Yesu kuwa, da yake ya san Uba ya sa kome a hannunsa, ya kuma sani daga wurin Allah ya fito, wurin Allah kuma zai koma, 4sai ya tashi daga cin abincin, ya ajiye mayafinsa, ya ɗauko ɗan zane ya yi ɗamara da shi. 5Sa’an nan ya zuba ruwa a daro, ya fara wanke ƙafafun almajiran, yana shafe su da abin da ya yi ɗamara da shi. 6Sai ya zo kan Bitrus, shi kuwa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ashe, kai ne za ka wanke mini ƙafa?” 7Yesu ya amsa ya ce, “Yanzu kam, ba ka san abin da nake yi ba, amma daga baya za ka fahimta.” 8Bitrus ya ce masa, “Wane ni! Ai, ba za ka wanke mini ƙafa ba har abada!” Yesu ya amsa masa ya ce, “In ban wanke maka ba, ba ka da rabo a gare ni.” 9Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ba ma ƙafafuna kaɗai ba, har ma da hannuwana da kaina!” 10Yesu ya ce masa, “Wanda ya yi wanka ba ya bukatar wanke kome, sai ƙafafunsa kawai, domin ya riga ya tsarkaka sarai. Ku ma tsarkakakku ne, amma ba dukanku ne ba.” 11Don ya san wanda zai bāshe shi, shi ya sa ya ce, “Ba dukanku ne tsarkakakku ba.”
12 Bayan ya wanke ƙafafunsu, ya yafa mayafinsa, sai ya sāke kishingiɗa, ya ce musu, “Kun gane abin da na yi muku? 13Kuna kirana Malam, da kuma Ubangiji. Daidai ne kuwa, don haka nake. 14Tun da yake ni Ubangijinku da kuma Malaminku, har na wanke muku ƙafa, ashe, ku ma wajibi ne ku wanke wa juna. 15Na yi muku ishara domin ku ma ku yi yadda na yi muku 16 Lalle hakika, ina gaya muku, bawa ba ya fin ubangijinsa, manzo kuma ba ya fin wanda ya aiko shi. 17In dai kun san wannan, kuna kuma aikatawa, ku masu farin ciki ne. 18 Ba dukanku nake nufi ba. Na san waɗanda na zaɓa. Wannan kuwa duk domin a cika Nassi ne cewa, ‘Wanda yake cin abincina ya tasar mini.’ 19Tun yanzu zan sanar da ku abu tun bai faru ba, domin sa’ad da ya faru ku ba da gaskiya ni ne shi. 20 Lalle hakika, ina gaya muku, wanda ya yi na’am da duk wanda na aiko, ya yi na’am da ni ke nan. Wanda ya yi na’am da ni kuwa, to, ya yi na’am da wanda ya aiko ni.”
Yesu Ya Ce Za a Bāshe Shi
(Mat 26.20-25; Mar 14.17-21; Luk 22.21-23)
21Bayan da Yesu ya faɗi haka, ya ji nauyi a ransa, ya yi shaida ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, ɗayanku zai bāshe ni.” 22Sai almajiran suka duddubi juna, suka rasa da wanda yake. 23Wani daga cikin almajiransa kuwa, wanda Yesu yake ƙauna, yana kishingiɗe gab da Yesu. 24Sai Bitrus ya alamta masa ya ce, “Gaya mana, da wa yake?” 25Shi kuwa da yake kishingiɗe haka gab da Yesu ya karkata, ya ce masa, “Ya Ubangiji, wane ne?” 26Sai Yesu ya amsa ya ce, “Shi ne wanda zan tsoma ‘yar lomar nan in ba shi.” Da ya tsoma ‘yar lomar kuwa, sai ya ba Yahuza, Ɗan Saminu Iskariyoti. 27Da karɓar ‘yar loman nan Shaiɗan ya shige shi. Yesu ya ce masa, “Yi abin da za ka yi, maza.” 28Amma cikin waɗanda suke cin abinci, ba wanda ya san dalilin da ya sa Yesu ya faɗa masa haka. 29Har waɗansu ma sun yi zaton Yesu ya ce masa ya yi musu sayayyar idi ne, ko kuwa ya ba gajiyayyu wani abu, don Yahuza ne yake riƙe da jakar kuɗinsu. 30Shi kuwa da karɓar ‘yar lomar, sai ya fita, da dare ne kuwa.
Sabon Umarni
31Bayan ya fita kuma sai Yesu ya ce, “Yanzu ne aka ɗaukaka Ɗan Mutum, aka kuma ɗaukaka Allah ta wurinsa. 32Allah kuma zai ɗaukaka shi zuwa ga zatinsa, nan da nan kuwa zai ɗaukaka shi. 33 Ya ku ‘ya’yana ƙanana, saura ɗan lokaci kaɗan ina tare da ku. Za ku neme ni, amma kamar yadda na faɗa wa Yahudawa cewa, ‘Inda za ni ba za ku iya zuwa ba,’ haka nake faɗa muku yanzu. 34 Sabon umarni nake ba ku, shi ne ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, haka ku ma, ku ƙaunaci juna. 35Ta haka, kowa zai gane ku almajiraina ne, in dai kuna ƙaunar juna.”
Bitrus Zai Yi Musun Sanin Yesu
(Mat 26.31-35; Mar 14.27-31; Luk 22.31-34)
36Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ina za ka?” Yesu ya amsa ya ce, “Inda za ni, ba za ka iya bina yanzu ba, amma daga baya za ka bi ni.” 37Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, don me, ba zan iya binka a yanzu ba? Ai, zan ba da raina saboda kai.” 38Yesu ya amsa ya ce, “Ashe, za ka ba da ranka saboda ni? Lalle hakika, ina gaya maka, kafin zakara ya yi cara, za ka yi musun sanina sau uku.
Yesu Ne Hanya zuwa Wurin Uban
1“Kada ku damu. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni. 2A gun Ubana akwai wurin zama da yawa. Da ba haka ne ba, da na faɗa muku, domin zan tafi in shirya muku wuri. 3In kuwa na je na shirya muku wuri, sai in dawo in kai ku wurina, domin inda nake, ku ma ku zama kuna can. 4Inda za ni kuwa kun san hanya.” 5Sai Toma ya ce masa, “Ya Ubangiji, ba mu san inda za ka ba, ƙaƙa za mu san hanyar?” 6Yesu ya ce masa, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina. 7Da kun san ni, da kun san Ubana ma. Amma daga yanzu kun san shi, kun kuma gan shi.”
8Sai Filibus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ka nuna mana Uban, bukatarmu ta biya ke nan.” 9Yesu ya ce masa, “Na daɗe tare da ku haka, amma har yanzu ba ka san ni ba, Filibus? Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban. Yaya za ka ce, ‘Nuna mana Uban’”? 10Wato ba ka gaskata ba cikin Uba nake, Uba kuma cikina? Maganar da nake faɗa muku, ba domin kaina nake faɗa ba, Uba ne da yake zaune a cikina yake yin ayyukansa. 11Ku gaskata ni, a cikin Uba nake, Uba kuma cikina, ko kuwa ku gaskata ni saboda ayyukan kansu.
12“Lalle hakika, ina gaya muku, duk wanda yake gaskatawa da ni ayyukan da nake yi shi ma haka zai yi. Har ma, zai yi ayyukan da suka fi waɗannan, domin zan tafi wurin Uba. 13Duk abin da kuka roƙa da sunana kuma zan yi, domin a ɗaukaka Uban ta wurin Ɗan. 14Kome kuke roƙa da sunana, zan yi shi.”
Alkawarin Zuwan Ruhu Mai Tsarki
15“In dai kuna ƙaunata, za ku bi umarnina. 16Ni ma zan roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimako ya kasance tare da ku har abada. 17Shi ne Ruhu na gaskiya, wanda duniya ba ta iya samunsa, domin ba ta ganinsa, ba ta kuma san shi ba. Ku kam, kun san shi, domin yana zaune tare da ku, zai kuma kasance a zuciyarku.
18“Ba zan bar ku marayu ba, zan zo wurinku. 19Saura ɗan lokaci kaɗan duniya ba za ta ƙara ganina ba, amma ku za ku gan ni. Saboda ni a raye nake, ku ma za ku rayu. 20A ran nan ne fa za ku sani, ni cikin Uba nake, ku kuma a cikina, ni kuma a cikinku. 21Duk wanda ya san umarnaina, yake kuma binsu, shi ne mai ƙaunata. Mai ƙaunata kuwa, Ubana zai ƙaunace shi, ni kuma zan ƙaunace shi, in bayyana kaina gare shi.” 22Sai Yahuza (ba Iskariyoti ba) ya ce masa, “Ya Ubangiji, me ya sa za ka bayyana kanka gare mu, ba ga duniya ba?” 23Yesu ya amsa masa ya ce, “Kowa yake ƙaunata, zai kiyaye maganata, Ubana kuwa zai ƙaunace shi, za mu zo wurinsa mu zauna tare da shi. 24Wanda ba ya ƙaunata, ba ya kiyaye maganata. Maganar da kuke ji kuwa ba tawa ba ce, ta Uba ce wanda ya aiko ni.
25“Duk wannan na faɗa muku ne tun muna tare. 26Amma Mai Taimako, Ruhu Mai Tsarki, wanda Uba zai aiko da sunana, shi ne zai koya muku kome, ya kuma tuna muku duk abin da na faɗa muku. 27Na bar ku da salama. Salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada ku damu, kada kuma ku ji tsoro. 28Kun dai ji na ce muku zan tafi, in kuma dawo wurinku. Da kuna ƙaunata da kun yi murna saboda za ni wurin Uba, domin kuwa Uban ya fi ni. 29To, yanzu na faɗa muku tun bai faru ba, domin sa’ad da ya faru, ku ba da gaskiya. 30Ba zan ƙara yi muku magana mai yawa ba, domin mai mulkin duniyan nan yana zuwa, ba shi kuwa da wani hannu a kaina, 31sai dai domin duniya tă sani ina ƙaunar Uban, ina kuma yin yadda Uba ya umarce ni, ku tashi mu tafi daga nan.
Yesu Ne Itacen Inabi na Hakika
1“Ni ne itacen inabi na hakika, Ubana kuwa shi ne manomi. 2Kowane reshe a cikina da ba ya ‘ya’ya, sai ya datse shi. Kowane reshe mai yin ‘ya’ya kuwa yakan tsarkake shi don ya ƙara haihuwa. 3Koyanzu ma ku tsarkakku ne saboda maganar da na faɗa muku. 4Ku zauna a cikina, ni kuma a cikinku. Kamar yadda reshen inabi, ba ya iya ‘ya’ya shi kaɗai, sai ko ya zauna itacen inabin, haka ku ma ba za ku iya ba, sai kun zauna a cikina. 5Ni ne itacen inabin, ku kuwa rassan. Wanda ya zauna a cikina, ni kuma a cikinsa, shi ne mai yin ‘ya’ya da yawa. Domin in ba game da ni ba, ba za ku iya kome ba. 6Duk wanda bai zauna a cikina ba, za a yar da shi can, kamar reshe, yă bushe, a kuma tattara irinsu a jefa wuta, a ƙone. 7In kun zauna a cikina, maganata kuma ta zauna a cikinku, za ku roƙi duk abin da kuke so, za a kuwa yi muku. 8Yadda ake ɗaukaka Ubana ke nan, in kuna ‘ya’ya da yawa, ta haka kuma kuke tabbata almajiraina. 9Kamar yadda Uba ya ƙaunace ni, haka ni ma na ƙaunace ku. To, ku zauna cikin ƙaunar da nake muku. 10In kun bi umarnina, za ku zauna cikin ƙaunar da nake muku, kamar yadda ni na bi umarnin Ubana, na kuma zauna cikin ƙaunar da yake mini. 11Na gaya muku haka domin farin cikina ya kasance a cikinku, farin cikinku kuma ya zama cikakke.
12 “Wannan fa shi ne umarnina, cewa ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku. 13Ba ƙaunar da ta fi haka ga mutane, wato mutum yă ba da ransa saboda aminansa. 14Ku aminaina ne in kuna yin abin da na umarce ku. 15Nan gaba ba sauran in ce da ku bayi, don bawa bai san abin da ubangijinsa yake yi ba. Sai dai in ce da ku aminai, domin na sanar da ku duk abin da na jiyo wurin Ubana. 16Ba ku kuka zaɓe ni ba, ni ne na zaɓe ku, na sa ku ku je ku yi ‘ya’ya, ‘ya’yanku kuma su tabbata, domin kome kuka roƙi Uba da sunana yă ba ku. 17Na umarce ku haka domin ku ƙaunaci juna.”
Ƙiyayyar Duniya
18In duniya ta ƙi ku, ku sani sai da ta ƙi ni kafin ta ƙi ku. 19Da ku na duniya ne da duniya ta so abinta, amma saboda ku ba na duniya ba ne, na kuma zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku. 20 Ku tuna da maganar da na yi muku cewa, “Bawa ba ya fin ubangijinsa.” In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun kiyaye maganata, da sai su kiyaye taku ma. 21Duk wannan za su yi muku saboda sunana, don ba su san wanda ya aiko ni ba. 22Da ba domin na zo na yi musu magana ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu kam, ba su da wani hanzari a kan zunubinsu. 23Wanda ya ƙi ni ya ƙi Ubana ma. 24Da ba domin na yi ayyuka a cikinsu da ba wanda ya taɓa yi sai ni ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun gani, sun kuma ƙi mu, ni da Ubana duka. 25 An yi wannan kuwa domin a cika maganar da yake a rubuce a cikin Shari’arsu cewa, “Sun ƙi ni ba dalili.” 26Amma sa’ad da Mai Taimako ya zo, wanda zan aiko muku daga wurin Uba, wato Ruhu na gaskiya, mai fitowa daga wurin Uba, shi ne zai shaida ni. 27Ku ma shaidu ne, domin tun farko kuke tare da ni.
1“Na faɗa muku duk wannan ne domin in kawar muku da sanadin tuntuɓe. 2Za su fisshe ku daga jama’a. Hakika, lokaci ma na zuwa da kowa ya kashe ku, zai zaci bautar Allah yake yi. 3Za su yi haka ne kuwa domin ba su san Uba ko ni ba. 4Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin in lokacinsu ya yi ku tuna na faɗa muku.”
Aikin Ruhu Mai Tsarki
“Ban faɗa muku abubuwan nan tun da farko ba, domin ina tare da ku. 5Yanzu kuwa za ni wurin wanda ya aiko ni, duk da haka a cikinku, ba wanda ya tambaye ni, ‘Ina za ka?’ 6Amma saboda na faɗa muku waɗannan abubuwa, ga shi baƙin ciki ya cika zuciyarku. 7Duk da haka ina gaya muku gaskiya, zai fiye muku in tafi, domin in ban tafi ba, Mai Taimakon nan ba zai zo gare ku ba. In kuwa na tafi, zan aiko shi gare ku. 8Sa’ad da kuwa ya zo zai faɗakar da duniya a kan zunubi, da adalci, da kuma hukunci. 9Wato a kan zunubi, domin ba su gaskata da ni ba, 10a kan adalci, don za ni wurin Uba, ba kuwa za ku ƙara ganina ba. 11a kan hukunci kuma, domin an yanke wa mai mulkin duniyar nan hukunci.
12“Ina da sauran abubuwa da yawa da zan gaya muku tukuna, amma ba za ku iya ɗaukarsu a yanzu ba. 13Sa’ad da kuwa Ruhu na gaskiya ya zo, zai bishe ku cikin dukan gaskiya, domin ba zai yi magana don kansa ba, sai dai duk abin da ya ji, shi zai faɗa, zai kuma sanar da ku al’amuran da za su auku. 14Zai ɗaukaka ni, domin zai ɗauko daga cikin abin da yake nawa ya sanar da ku. 15Duk abin da Uba yake da shi, nawa ne. Shi ya sa na ce zai ɗauko daga cikin abin da yake nawa ya sanar da ku.”
Baƙin Ciki Zai Koma Farin Ciki
16“Bayan ɗan lokaci kaɗan, ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma, za ku gan ni.” 17Sai waɗansu almajiransa suka ce wa juna, “Me yake nufi da ce mana, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma za ku gan ni’? da kuma cewa, ‘Domin za ni wurin Uba’?” 18Suka ce, “Me yake nufi da, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan’ ɗin? Ai, ba mu san abin da yake faɗa ba.” 19Yesu kuwa ya sani suna so su tambaye shi, sai ya ce musu, “Wato kuna tambayar juna ne abin da nake nufi da cewa, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma za ku gan ni’? 20Lalle hakika, ina gaya muku, za ku yi kuka da kuma gunji, amma duniya za ta yi farin ciki. Za ku yi baƙin ciki, amma baƙin cikinku zai koma farin ciki. 21Idan mace tana naƙuda takan sha wuya, don lokacin haihuwarta ya yi. Amma da zarar ta haifi jinjirin, ba ta ƙara tunawa da wahalar da ta sha, domin murnar an sami baƙon duniya. 22Haka ku ma yanzu kuke tare da baƙin ciki, amma zan sāke ganinku, sa’an nan zuciyarku za ta yi fari, ba kuwa mai ɗauke muku farin cikinku. 23A ran nan, ba za ku yi mini wata tambaya ba. Lalle hakika, ina gaya muku, kome kuka roƙi Uba zai ba ku saboda sunana. 24Har yanzu dai ba ku roƙi kome da sunana ba. Ku roƙa, za ku samu, domin farin cikinku ya zama cikakke.”
Na Yi Nasara da Duniya
25“Duk wannan na faɗa muku da misalai ne. Lokaci yana zuwa da ba zan ƙara faɗa muku kome da misalai ba, sai dai in ba ku labarin Uba a sarari. 26A ran nan za ku yi roƙo da sunana. Ban kuwa ce muku zan roƙar muku Uba ba, 27domin shi Uban kansa na ƙaunarku, domin kun ƙaunace ni, kun kuma gaskata daga wurin Uban na fito. 28Daga wurin Uban ne na fito, na shigo duniya, har wa yau kuma zan bar duniya in koma wurin Uba.”
29Sai almajiransa suka ce, “Yauwa! Yanzu ne fa kake magana a sarari, ba da misali ba! 30Yanzu ne muka tabbata ka san kome, ba sai wani ya tambaye ka ba. Ta haka muka gaskata daga wurin Allah ka fito.” 31Yesu ya amsa musu ya ce, “Ashe, yanzu kun gaskata? 32To, lokaci na zuwa, har ma ya yi, da za a warwatsa ku, kowa yă koma gidansu, ku bar ni ni kaɗai. Duk da haka kuwa ba ni kaɗai nake ba, domin Uba na tare da ni. 33Na faɗa muku wannan ne domin a gare ni ku sami salama. A duniya kuna shan wuya, amma dai ku yi farin ciki, ai, na yi nasara da duniya.”