Skip to content

Wa’azi a kan Dutse(Mat 5.—7)

1Da Yesu ya ga taro masu yawa sai ya hau dutse. Da ya zauna, almajiransa kuma suka zo gunsa. 2Sai ya buɗe baki ya koya musu.Albarku(Luk 6.20-23)3“Albarka tā tabbata ga waɗanda suka san talaucinsu na ruhu, domin Mulkin Sama nasu ne.4  “Albarka tā tabbata ga masu nadāma, domin za a sanyaya musu rai.5  “Albarka tā tabbata ga masu tawali’u, domin za su gāji duniya.6  “Albarka tā tabbata ga masu kwaɗaita ga adalci, domin za a biya musu muradi.7“Albarka tā tabbata ga majiya tausayi, domin su ma za a ji tausayinsu.8  “Albarka tā tabbata ga masu tsarkakakkiyar zuciya, domin za su ga Allah.9“Albarka tā tabbata ga masu ƙulla zumunci, domin za a ce da su ‘ya’yan Allah.10  “Albarka tā tabbata ga masu shan tsanani saboda aikata adalci, domin Mulkin Sama nasu ne.11  “Albarka tā tabbata gare ku sa’ad da mutane suka zage ku, suka tsananta muku, suka kuma ƙaga muku kowace irin mugunta, saboda ni. 12 Ku yi murna da farin ciki matuƙa, domin sakamakonku mai yawa ne a Sama, gama haka aka tsananta wa annabawan da suka riga ku13  “Ku ne gishirin duniya. Amma in gishiri ya sāne, da me za a daɗaɗa shi? Ba shi da sauran amfani, sai dai a zubar, mutane kuma su tattake.14  “Ku ne hasken duniya. Ai, birnin da aka gina bisa tudu ba shi ɓoyuwa. 15 Ba a kunna fitila a rufe ta da masaki, sai dai a ɗora ta a kan maɗorinta, sa’an nan ta ba duk mutanen gida haske. 16 To, haskenku yă riƙa haskakawa haka a gaban mutane, domin su ga kyawawan ayyukanku, su kuma ɗaukaka Ubanku da yake cikin Sama.”Koyarwar Yesu a kan Attaura17“Kada ku yi zaton na zo ne in shafe Attaura da koyarwar annabawa. Na zo ne ba domin in shafe su ba, sai dai domin in cika su. 18 Hakika ina gaya muku, kafin sararin sama da ƙasa su shuɗe, ko wasali ko ɗigo na Attaura ba za su shuɗe ba, sai an cika dukan kome. 19Don haka duk wanda ya yar da umarni ɗaya mafi ƙanƙanta daga cikin umarnan nan, har ya koya wa mutane haka, za a ce da shi mafi ƙanƙanta a Mulkin Sama. Duk wanda ya bi su kuwa, har ya koyar da su, za a ce da shi mai girma a Mulkin Sama. 20Ina dai gaya muku, in adalcinku bai fi na malaman Attaura da Farisiyawa ba, ba za ku shiga Mulkin Sama ba faufau.”Koyarwar Yesu a kan Fushi(Luk 12.57-59)21  “Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā, ‘Kada ka yi kisankai, kowa ya yi kisa kuwa, za a hukunta shi.’ 22Amma ni ina gaya muku, kowa yake fushi da ɗan’uwansa ma, za a hukunta shi. Kowa ya ce da ɗan’uwansa wawa, za a kai shi gaban majalisa. Kowa kuma ya ce, ‘Kai wofi!’ hakkinsa shiga Gidan Wuta. 23Saboda haka, in kana cikin miƙa sadakarka a kan bagadin hadaya, a nan kuma ka tuna ɗan’uwanka na da wata magana game da kai, 24sai ka dakatar da sadakarka a gaban bagadin hadaya tukuna, ka je ku shirya da ɗan’uwanka, sa’an nan ka zo ka miƙa sadakarka. 25Ka hanzarta shiryawa da mai ƙararka tun kuna tafiya gaban shari’a, don kada mai kararka ya bashe ka ga alƙali, alƙali kuma ya miƙa ka ga dogari, a kuma jefa ka a kurkuku. 26Hakika ina gaya maka, ba za ka fita daga nan ba, sai ka biya duk, babu sauran ko anini.”Koyarwar Yesu a kan Zina27  “Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’ 28Amma ni ina gaya muku, kowa ya dubi mace duban sha’awa, ya riga ya yi zinar zuci ke nan da ita. 29 In idonka na dama yana sa ka yi laifi, to, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓinka da a jefa duk jikinka ɗungum a Gidan Wuta. 30In kuma hannunka na dama, yana sa ka yi laifi, to, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓinka da a jefa jikinka ɗungum a Gidan Wuta.”Koyarwar Yesu a kan Kisan Aure(Mat 19.9; Mar 10.11-12; Luk 16.18)31  “An kuma ce, ‘Kowa ya saki matarsa, sai ya ba ta takardar saki.’ 32 Amma ni ina gaya muku, kowa ya saki matarsa, in ba a kan laifin zina ba, ya sa ta hanyar zina ke nan. Wanda kuma ya auri sakakkiya, ya yi zina.”Koyarwar Yesu a kan Rantsuwa33  “Har wa yau dai kun ji an faɗa wa mutanen dā, ‘Kada ka rantse a kan ƙarya, sai dai ka cika wa’adin da ka ɗaukar wa Ubangiji.’ 34 Amma ni ina gaya muku, kada ma ku rantse sam, ko da sama, domin ita ce kursiyin Allah, 35 ko da ƙasa, domin ita ce matashin ƙafarsa, ko kuma da Urushalima, domin ita ce birnin Babban Sarki. 36Kada kuwa ka rantse da kanka, don ba za ka iya mai da ko gashi ɗaya fari ko baƙi ba. 37Abin da duk za ku faɗa ya tsaya a kan ‘I’ ko ‘A’a’ kawai. In dai ya zarce haka, to, daga Mugun ya fito.”38  “Kun dai ji an faɗa, ‘Sakayyar ido, ido ne, sakayyar haƙori kuma haƙori ne.’ 39Amma ni ina gaya muku, kada ku ƙi a cuce ku. Amma ko wani ya mare ka a kuncin dama, to, juya masa ɗayan kuma. 40In kuwa wani ya yi ƙararka da niyyar karɓe taguwarka, to, ka bar masa mayafinka ma. 41In kuma wani ya tilasta maka ku yi tafiyar mil guda tare, to, ku yi tafiyar mil biyu ma. 42Kowa ya roƙe ka, ka ba shi, mai neman rance a wurinka kuwa, kada ka hana shi.”43“Kun dai ji an faɗa, ‘Ka so ɗan’uwanka, ka ƙi magabcinka.’ 44Amma ni ina gaya muku, ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa masu tsananta muku addu’a, 45domin ku zama ‘ya’yan Ubanku wanda yake cikin Sama. Domin yakan sa rana tasa ta fito kan mugaye da kuma nagargaru, ya kuma sako ruwan sama ga masu adalci da marasa adalci. 46In masoyanku kawai kuke ƙauna, wane lada ne da ku? Ashe, ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba? 47In kuwa ‘yan’uwanku kaɗai kuke gayarwa, me kuka yi fiye da waɗansu? Ashe, ko al’ummai ma ba haka suke yi ba? 48 Saboda haka sai ku zama cikakku, kamar yadda Ubanku na Sama take cikakke.”

Koyarwar Yesu a kan Ba Da Sadaka

1  “Ku yi hankali kada ibadarku ta zama ta ganin ido. Domin in kun yi haka, ba za ku sami sakamako wurin Ubanku da yake a Sama ba.2“Wato, in za ka yi sadaka, kada ka yi kwakwazo yadda munafukai suke yi a majami’u da kuma kan hanya don dai mutane su yabe su. Gaskiya nake faɗa muku, sun sami iyakar ladarsu ke nan. 3Amma in kana yin sadaka, kada hannunka na hagu ya san abin da hannunka na dama yake yi, 4domin sadakarka tă zama a asirce, Ubanku kuwa da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.”Koyarwar Yesu a kan Addu’a(Luk 11.2-4)5  “In za ku yi addu’a, kada ku zama kamar munafukai, don sun cika son yin addu’a a tsaye a majami’u da kan hanya, wai mutane su gan su. Gaskiya nake gaya muku, sun sami iyakar ladansu. 6Amma in za ka yi addu’a, sai ka shiga lollokinka, ka rufe ƙofa, ka yi addu’a ga Ubanku wanda yake ɓoye, Ubanku kuwa da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.7“In kuwa kuna addu’a, kada ku yi ta maimaitawar banza, kamar yadda al’ummai suke yi, a zatonsu za a saurare su saboda yawan maganarsu. 8Kada ku zama kamarsu, domin Ubanku ya san bukatarku tun kafin ku roƙe shi. 9Saboda haka sai ku yi addu’a kamar haka,“ ‘Ya Ubanmu, wanda yake cikin Sama,A kiyaye sunanka da tsarki.10Mulkinka yă zo,A aikata nufinka a duniya kamar yadda ake yi a Sama.11Ka ba mu abincinmu na yau.12Ka gafarta mana laifofinmu,Kamar yadda mu ma muke gafarta wa waɗanda suke yi mana laifi.13Kada ka kai mu wurin jaraba,Amma ka cece mu daga Mugun.’14  “Domin in kun yafe wa mutane laifofinsu, Ubanku na Sama zai yafe muku. 15In kuwa ba ku yafe wa mutane laifofinsu ba, Ubanku ma ba zai yafe muku naku ba.”Koyarwar Yesu a kan Azumi16“In kuma kuna yin azumi, kada ku turɓune fuska kamar munafukai, don sukan yanƙwane fuska, wai don mutane su ga suna azumi ne. Hakika, ina gaya muku, sun sami iyakar ladansu ke nan. 17Amma in kana azumi, ka shafa mai a ka, ka kuma wanke fuska, 18don kada mutane su ga alama kana azumi, sai dai Ubanku da yake ɓoye ya gani. Ubanku kuma da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.”Tara Dukiya a Sama(Luk 12.33-34)19  “Kada ku tara wa kanku dukiya a duniya, inda asu da tsatsa suke ɓatawa, inda ɓarayi kuma suke karyawa su yi sata. 20Sai dai ku tara wa kanku dukiya a Sama, inda ba asu da tsatsa da za su ɓata, inda kuma ba ɓarayin da za su karya su yi sata. 21Domin kuwa inda dukiyarka take, a nan zuciyarka ma take.”Fitilar Jiki(Luk 11.34-36)22“Ido shi ne fitilar jiki. In idonka lafiyayye ne, duk jikinka ma sai ya cika da haske. 23In kuwa idonka da lahani, duk jikinka sai ya cika da duhu. To, in hasken da yake gare ka duhu ne, ina misalin yawan duhun!”Bauta wa Allah ko Dukiya(Luk 16.13)24“Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu; ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗaya, ko kuwa ya amince wa ɗayan, ya raina ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah da dukiya gaba ɗaya.”Damuwa da Alhini(Luk 12.22-31)25“Saboda haka ina gaya muku, kada ku damu a kan rayuwarku game da abin da za ku ci, da abin da za ku sha, ko kuwa jikinku, abin da za ku yi sutura. Ashe, rai bai fi abinci ba? Jiki kuma bai fi tufafi ba? 26Ku dubi dai tsuntsaye. Ai, ba sa shuka, ba sa girbi, ba sa kuma tarawa a rumbuna, amma kuwa Ubanku na Sama na ci da su. Ashe, ko ba ku fi martaba nesa ba? 27Wane ne a cikinku, don damuwarsa, zai iya ƙara ko da taƙi ga tsawon rayuwarsa? 28To, don me kuke damuwa a kan tufafi? Ku dubi dai furannin jeji, yadda suke girma, ba sa aikin fari, ba sa na baƙi, 29 duk da haka ina gaya muku, ko Sulemanu ma, shi da adonsa duk, bai taɓa yin adon da ya fi na ɗayansu ba. 30To, ga shi, Allah yana ƙawata tsire-tsiren jeji ma haka, waɗanda yau suke raye, gobe kuwa a jefa su a murhu, balle ku? Ya ku masu ƙarancin bangaskiya! 31Don haka kada ku damu, kuna cewa, ‘Me za mu ci’ ko? ‘Me za mu sha?’ Ko kuwa, ‘Me za mu sa?’ 32Ai, al’ummai ma suna ta neman duk irin waɗannan abubuwa, Ubanku na Sama kuwa ya san kuna bukatarsu duka. 33Muhimmin abu na farko, sai ku ƙwallafa rai ga al’amuran Mulkin Allah, da kuma adalcinsa, har ma za a ƙara muku dukan waɗannan abubuwa.34“Saboda haka kada ku damu don gobe, ai, gobe ta Allah ce. Wahalce-wahalcen yau ma sun isa wahala.”

MAT 7

Kada Ku Ɗora wa Kowa Laifi(Luk 6.37-38,41-42)1“Kada ku ɗora wa kowa laifi, don kada a ɗora muku. 2 Don da irin hukuncin da kuka zartar, da shi za a zartar muku. Mudun da kuka auna, da shi za a auna muku. 3Don me kake duban ɗan hakin da yake idon ɗan’uwanka, amma gungumen da yake a naka ido ba ka kula ba? 4Ko kuwa yaya za ka iya ce wa ɗan’wanka, ‘Bari in cire maka ɗan hakin daga idonka,’ alhali kuwa da gungume a naka ido? 5Kai munafuki! Sai ka fara cire gungumen da yake idonka tukuna, sa’an nan ka gani sosai yadda za ka cire ɗan hakin daga idon ɗan’uwanka.6“Kada ku ba karnuka abin da yake tsattsarka. Kada kuma ku jefa wa alhanzir lu’ulu’unku, don kada su tattake su, su juyo su kyakketa ku.”Ku Roƙa, Ku Nema, Ku Ƙwanƙwasa(Luk 11.9-13)7“Ku yi ta roƙo, za a ba ku. Ku yi ta nema, za ku samu. Ku yi ta ƙwanƙwasawa, za a kuwa buɗe muku. 8Duk wanda ya roƙa, akan ba shi, mai nema yana tare da samu. Wanda ya ƙwanƙwasa kuma za a buɗe masa. 9To, wane ne a cikinku, ɗansa zai roƙe shi gurasa, ya ba shi dutse? 10Ko kuwa ya roƙe shi kifi, ya ba shi maciji? 11To, ku da kuke mugaye ma, kuka san yadda za ku ba ‘ya’yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama da zai ba da abubuwan alheri ga masu roƙonsa? 12 Saboda haka duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Attaura da koyarwar annabawa.”Ƙunƙuntar Ƙofa(Luk 13.24)13“Ku shiga ta ƙunƙuntar ƙofa, gama ƙofa zuwa hallaka faffaɗa ce, hanyarta mai sauƙin bi ce, masu shiga ta cikinta suna da yawa. 14Domin kuwa ƙofar zuwa rai ƙunƙunta ce, hanyarta mai wuyar bi ce, masu samunta kuwa kaɗan ne.”Akan Gane Itace ta ‘Ya’yansa(Luk 6.43-44)15“Ku kula da annabawan ƙarya, waɗanda sukan zo muku da siffar tumaki, amma a zuci kyarketai ne masu ƙāwa. 16Za ku gane su ta irin aikinsu. A iya ciran inabi a jikin ƙaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙƙiya? 17Haka kowane itacen kirki yakan haifi kyawawan ‘ya’ya. Mummunan itace kuwa yakan haifi munanan ‘ya’ya. 18Kyakkyawan itace ba dama ya haifi munanan ‘ya’ya. Haka kuma mummunan itace ba dama ya haifi kyawawan ‘ya’ya. 19 Duk itacen da ba ya ‘ya’ya masu kyau, sai a sare shi a jefa a wuta. 20Don haka, da irin aikinsu za a gane su.”Ban Taɓa Saninku ba(Luk 13.25-27)21“Ba duk mai ce mini, ‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji,’ ne zai shiga Mulkin Sama ba, sai dai wanda ya yi abin da Ubana da yake cikin Sama yake so. 22A ranar nan da yawa za su ce mini, ‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci da sunanka ba? Ba mu fitar da aljannu da sunanka ba? Ba mu kuma yi ayyukan al’ajabi masu yawa da sunanka ba?’ 23 Sa’an nan zan ce musu, ‘Ni ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu yin mugun aiki.’ ”Kafa Harsashin Gini Iri Biyu(Luk 6.47-49)24“Saboda haka, kowa da yake jin maganar nan tawa, yake kuma aikata ta, za a kwatanta shi da mutum mai hikima, wanda ya gina gidansa a kan fā. 25Da ruwa ya sauko, koguna suka yi cikowa, iska ta taso ta bugi gidan, amma bai faɗi ba, domin an gina shi a kan fā ne. 26Kowa ya ji maganar nan tawa, bai aikata ta kuma ba, za a misalta shi da wawan mutum, wanda ya gina gidansa a kan rairayi. 27Da ruwa ya sauko, koguna suka yi cikowa, sai iska ta taso ta bugi gidan har ya rushe, mummunar ragargajewa kuwa!”Hakikancewar Yesu(Mar 1.22)

Da Yesu ya gama duk wannan magana, sai taro suka yi mamakin koyarwarsa, 29domin yana koya musu da hakikancewa, ba kamar malamansu na Attaura ba.