A cikin makon farko
19A ran nan da magariba, ranar farko ta mako, ƙofofin ɗakin da almajiran suke ciki na kulle don tsoron Yahudawa, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsaka, ya ce musu, “Salama alaikun!” 20Da ya faɗi haka, ya nuna musu hannuwansa da kwiɓinsa. Sai almajiran suka yi farin ciki da ganin Ubangiji. 21Sai Yesu ya sāke ce musu, “Salama alaikun! Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka ni ma na aike ku.” 22Da ya faɗi haka ya busa musu numfashinsa, ya ce musu, “Ku karɓi Ruhu Mai Tsarki. 23 Duk waɗanda kuka gafarta wa zunubansu, an gafarta musu ke nan. Duk waɗanda ba ku gafarta wa ba kuwa, ba a gafarta ba ke nan.”Rashin Bangaskiyar Toma24Toma kuwa, ɗaya daga cikin goma sha biyun nan, wanda ake kira Ɗan Tagwai, ba ya nan tare da su sa’ad da Yesu ya zo. 25Sai sauran almajiran suka ce masa, “Mun ga Ubangiji.” Amma ya ce musu, “In ban ga gurbin ƙusoshi a hannuwansa ba, in sa yatsata a gurbin ƙusoshin, in kuma sa hannuna a kwiɓinsa ba, ba zan ba da gaskiya ba.”26Bayan kwana takwas har wa yau almajiransa na cikin gidan, Toma ma yana nan tare da su, ƙofofi suna kulle, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsaka, ya ce, “Salama alaikun.” 27Sa’an nan ya ce wa Toma, “Sa yatsanka nan, ka ji hannuwana. Miƙo hannunka kuma ka sa a kwiɓina. Kada ka zama marar ba da gaskiya, sai dai mai ba da gaskiya.” 28Toma ya amsa masa ya ce, “Ya Ubangijina Allahna kuma!” 29Sai Yesu ya ce masa, “Wato saboda ka gan ni ka ba da gaskiya? Albarka tā tabbata ga waɗanda ba su gani ba, amma kuwa suka ba da gaskiya.”Manufar Littafin Nan30Yesu ya yi waɗansu mu’ujizai da yawa dabam dabam a gaban almajiran, waɗanda ba a rubuta a littafin nan ba. 31Amma an rubuta waɗannan ne, domin ku ba da gaskiya Yesu shi ne Almasihu, Ɗan Allah, ta wurin gaskatawa kuma ku sami rai a cikin sunansa.. (Yohanna 20: 19-30)
Bayan satin farko
Yesu Ya Bayyana ga Almajirai Bakwai1Bayan haka Yesu ya sāke bayyana kansa ga almajiran a bakin Tekun Tibariya. Ga kuwa yadda ya bayyana kansa. 2Bitrus, da Toma wanda ake kira Ɗan Tagwai, da Nata’ala na Kana ta ƙasar Galili, da ‘ya’yan nan na Zabadi, da kuma waɗansu almajiransa biyu, duk suna nan tare, 3 Sai Bitrus ya ce musu, “Za ni su.” Suka ce masa, “Mu ma mā tafi tare da kai.” Sai suka fita suka shiga jirgi. Amma a daren nan ba su kama kome ba.4Gari na wayewa sai ga Yesu tsaye a bakin gaci, amma almajiran ba su gane Yesu ne ba. 5Sai Yesu ya ce musu, “Samari, kuna da kifi?” Suka amsa masa suka ce, “A’a.” 6 Ya ce musu, “Ku jefa taru dama da jirgin za ku samu.” Suka jefa, har suka kāsa jawo shi don yawan kifin. 7Sai almajirin nan da Yesu yake ƙauna ya ce wa Bitrus, “Ubangiji ne dai!” Da Bitrus ya ji, ashe, Ubangiji ne ya yi ɗamara da taguwarsa, don a tuɓe yake, ya fāɗa tekun. 8Sauran almajirai kuwa suka zo a cikin ƙaramin jirgi, janye da tarun cike da kifi, don ba su da nisa daga gaci, kamar misalin kamu ɗari biyu ne.9Da fitowarsu gaci sai suka ga garwashi a wurin, da kifi kai, da kuma gurasa. 10Yesu ya ce musu, “Ku kawo waɗansu kifi a na waɗanda kuka kama yanzu.” 11Sai Bitrus ya hau jirgin, ya jawo tarun gaci, cike da manyan kifaye dari da hamsin da uku. Amma duk da yawansu haka, tarun bai kece ba. 12Sai Yesu ya ce musu, “Ku zo ku karya kumallo.” Daga cikin almajiran kuwa ba wanda ya yi ƙarfin halin tambayarsa ko shi wane ne, domin sun sani Ubangiji ne. 13Sai Yesu ya zo ya ɗauki gurasar, ya ba su, haka kuma kifin. 14Wannan ne fa zuwa na uku da Yesu ya bayyana ga almajiran bayan an tashe shi daga matattu.Yi Kiwon Tumakina15Da suka karya kumallo Yesu ya ce wa Bitrus, “Bitrus ɗan Yahaya, ka fi waɗannan ƙaunata?” Ya ce masa, “I, ya Ubangiji, ka dai sani ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka yi kiwon ‘ya’yan tumakina.” 16Ya sāke faɗa masa, faɗa ta biyu, “Bitrus ɗan Yahaya, kana ƙaunata?” Ya ce masa, “I, ya Ubangiji, ka dai sani ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka kiyaye tumakina.” 17Yesu ya faɗa masa, faɗa ta uku, “Bitrus ɗan Yahaya, kana sona?” Sai Bitrus ya yi baƙin ciki don a faɗar nan ta uku ya ce masa, “Kana sona?” Shi kuwa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ai, ka san kome duka, ka kuwa sani ina sonka.”Yesu ya ce masa, “Ka yi kiwon tumakina. 18Lalle hakika, ina gaya maka, lokacin samartakarka kakan yi wa kanka ɗamara, ka tafi inda ka nufa, amma in ka tsufa, za ka miƙe hannuwanka, wani ya yi maka ɗamara, ya kai ka inda ba ka nufa ba.” 19(Ya faɗi wannan ne yana kwatanta irin mutuwar da Bitrus zai yi ya ɗaukaka Allah.) Bayan ya faɗi haka, ya ce masa, “Bi ni.”Almajirin da Yesu Yake Ƙauna20 Sai Bitrus ya waiwaya ya ga almajirin nan da Yesu yake ƙauna yana biye da su, wato wanda ya jingina gab da Yesu lokacin cin jibin nan da ya ce, “Ya Ubangiji, wane ne zai bāshe ka?” 21Da Bitrus ya gan shi, ya ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, wannan fa?” 22Yesu ya ce masa, “In na nufe shi da wanzuwa har in zo, mene ne naka a ciki? Kai dai, bi ni!” 23Saboda haka maganan nan ta bazu cikin ‘yan’uwa, cewa almajirin nan ba zai mutu ba. Alhali kuwa Yesu bai ce masa ba zai mutu ba, ya dai ce, “In na nufe shi da wanzuwa har in zo, mene ne naka a ciki?”24Wannan shi ne almajirin da yake ba da shaida a kan waɗannan al’amura, ya kuma rubuta su, mun kuwa sani shaida tasa tabbatacciya ce.25Akwai waɗansu al’amura kuma masu yawa da Yesu ya aikata, in da za a rubuta kowannensu ɗaya ɗaya da ɗaya ɗaya, ina tsammani ko duniya kanta ba za ta iya ɗaukar littattafan da za a rubuta ba.(Yohanna 21: 1-25)
Tashinsa zuwa sama
1 Ya Tiyofalas, tarihin nan na farko wanda na rubuta, ya shafi dukan abubuwan da Yesu ya fara yi, da kuma waɗanda ya fara koyarwa, 2har ya zuwa ranar da aka ɗauke shi aka kai shi Sama, bayan ya yi umarni ta wurin Ruhu Mai Tsarki ga manzannin da ya zaɓa. 3Ya bayyana kansa gare su a raye bayan shan wuya tasa, tare da tabbatarwa masu yawa, masu ƙarfi kuma, yana bayyana gare su a kai a kai har kwana arba’in, yana zancen al’amuran Mulkin Allah. 4 Sa’ad da yake tare da su, ya umarce su kada su tashi daga Urushalima, amma su jira cikar alkawarin nan da Uba ya yi, “wanda kuka ji daga bakina, 5domin Yahaya kam, da ruwa ya yi baftisma, amma kafin ‘yan kwanaki da Ruhu Mai Tsarki za a yi muku baftisma.”An Ɗauke Almasihu Sama(Mar 16.19-20; Luk 24.50-53)6Saboda haka da suka taru, suka tambaye shi suka ce, “Ya Ubangiji, yanzu ne za ka sāke kafa wa Isra’ila mulki?” 7Ya ce musu, “Sanin lokatai da zamanai, da Uba ya sa cikin ikonsa, ba naku ba ne. 8 Amma za ku sami iko sa’ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauko muku, za ku kuma zama shaiduna a Urushalima, da duk ƙasar Yahudiya, da ta Samariya, har ya zuwa iyakar duniya.”9 Da ya faɗi haka, suna cikin dubawa, sai aka ɗauke shi Sama, wani gajimare ya tafi da shi, ba su ƙara ganinsa ba. 10Suna cikin zuba ido sama, shi kuma yana tafiya, sai ga mutum biyu tsaye kusa da su, saye da fararen tufafi. 11Sai suka ce, “Ya ku mutanen Galili, don me kuke tsaye kuna duban sama? Yesun nan da aka ɗauke daga gare ku aka kai shi Sama, zai komo ne ta yadda kuka ga tafiyarsa zuwa Sama.”” (Ayyukan Manzanni 1:1-11)