Fitowa 12:1-42 |
1 Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna cikin ƙasar Masar, 2wannan wata zai zama wata na farko a shekara a gare su. 3A faɗa wa dukan taron Isra’ilawa cewa, “A rana ta goma ga watan nan, kowane namiji ya ɗauki ɗan rago ko ɗan akuya daga cikin garke domin iyalinsa, dabba ɗaya domin kowane gida. 4Idan da wanda iyalinsa ba za su iya cinye dabba guda ɗungum ba, saboda iyalin kima ne, to, sai su haɗa kai da maƙwabtansu, su ɗauki dabba guda gwargwadon yawansu. 5Tilas ne dabbar ta kasance lafiyayyiya ƙalau, bana ɗaya. Za ku kamo daga cikin tumakinku ko awaki. 6Za ku turke dabbar har rana ta goma sha huɗu ga wata, wato sa’ad da dukan taron jama’ar Isra’ila za su yanka ragunansu da maraice. 7Sa’an nan ku ɗibi jinin, ku sa a dogaran ƙofa duka biyu, da bisa kan ƙofar gidajen da za a ci naman dabbobin. 8A daren nan za ku gasa naman, ku ci da abinci marar yisti, da ganyaye masu ɗaci. 9Kada ku ci shi ɗanye ko daffaffe da ruwa, amma a gasa shi, da kan, da ƙafafun, da kayan cikin. 10Kada ku bar kome ya kai gobe, abin da ya kai gobe kuwa, sai ku ƙone shi. 11Ga yadda za ku ci shi, da ɗamara a gindinku, da takalma a ƙafafunku, da sanda a hannunku, da gaggawa kuma za ku ci shi. Idin Ƙetarewa ne ga Ubangiji. 12A daren nan zan ratsa ƙasar Masar, in bugi kowane ɗan fari na ƙasar, na mutum da na dabba. Zan hukunta gumakan Masar duka, gama ni ne Ubangiji. 13Jinin da yake bisa gidajenku zai nuna inda kuke. Sa’ad da na ga jinin zan tsallake ku, ba kuma wani bala’in da zai same ku, ya hallaka ku, a lokacin da zan bugi ƙasar Masar. 14 Ranan nan za ta zama ranar tunawa a gare ku, za ku kiyaye ta, ranar idi ga Ubangiji. Dukan zamananku za ku kiyaye ta, idi ga Ubangiji har abada.
15“Za ku yi kwana bakwai kuna cin abinci marar yisti. A rana ta fari za ku fitar da yisti daga cikin gidajenku, gama duk wanda ya ci abin da aka sa wa yisti tun daga rana ta fari har zuwa ta bakwai za a fitar da shi daga cikin Isra’ila. 16A kan rana ta fari za ku yi tsattsarkan taro, haka kuma za ku yi a rana ta bakwai. A cikin waɗannan ranaku ba za a yi kowane aiki ba, sai na abin da kowa zai ci. 17Za ku kiyaye idin abinci marar yisti, gama a wannan rana na fitar da rundunarku daga ƙasar Masar. Ku kiyaye wannan rana dukan zamananku. Wannan farilla ce ta har abada. 18Za ku ci abinci marar yisti da maraice a kan rana ta goma sha huɗu ga wata na fari, har zuwa rana ta ashirin da ɗaya ga watan da maraice. 19Amma kada a iske yisti a gidajenku har kwana bakwai, gama idan wani ya ci abin da aka sa wa yisti za a fitar da shi daga cikin taron jama’ar Isra’ila, ko shi baƙo ne ko kuwa haifaffen ƙasar. 20Dukan abin da yake da yisti ba za ku ci shi ba, wato sai abinci marar yisti ne kaɗai za ku ci a dukan gidajenku.”
21Musa ya kirayi dattawan Isra’ila duka, ya ce musu, “Gaggauta, ku zaɓa wa kanku ɗan tunkiya ko akuya bisa ga iyalanku, ku yanka domin Idin Ƙetarewa. 22Ku ɗauki tuntun ezob, ku tsoma cikin jinin da yake a kasko, ku yarfa wa dogaran ƙofa duka biyu, da bisa kan ƙofar. Kada kowa ya fita daga gidansa sai da safe. 23 Gama Ubangiji zai ratsa don ya kashe Masarawa, sa’ad da ya ga jinin a bisa kan ƙofar, da dogaran ƙofa duka biyu sai ya wuce ƙofar, ba zai bar mai hallakarwa ya shiga gidanku, ya kashe ku ba. 24Za ku kiyaye waɗannan ƙa’idodi, ku riƙe su farilla, ku da ‘ya’yanku har abada. 25Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji zai ba ku kamar yadda ya alkawarta, wajibi ne ku kiyaye wannan farilla. 26Sa’ad da ‘ya’yanku suka tambaye ku, ‘Ina ma’anar wannan farilla?’ 27Za ku ce, ‘Hadaya ce ta Idin Ƙetarewa ga Ubangiji, domin ya tsallake gidajen Isra’ilawa a Masar, lokacin da ya kashe Masarawa, amma bai taɓa gidajenmu ba’ ” Sai jama’ar suka durƙusa suka yi sujada. 28Isra’ilawa suka tafi suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa da Haruna.
Mutuwar ‘Ya’yan Fari
29 Da tsakar dare sai Ubangiji ya karkashe dukan ‘ya’yan fari maza a ƙasar Masar, tun daga ɗan farin Fir’auna, wato magajinsa, har zuwa ɗan farin ɗan sarka da yake a kurkuku, har da dukan ‘ya’yan fari maza na dabbobi. 30Da dare Fir’auna ya tashi, shi da dukan fādawansa, da dukan Masarawa, suka yi kuka mai tsanani a Masar, gama ba gidan da ba a yi mutuwa ba. 31Sai Fir’auna ya sa aka kirawo masa Musa da Haruna da daren, ya ce musu, “Tashi, ku da jama’arku, ku fita daga cikin jama’ata. Tafi, ku bauta wa Ubangiji kamar yadda kuka ce. 32Kwashi garkunanku na tumaki da awaki, da na shanu, ku yi tafiyarku kamar yadda kuka ce, amma ku sa mini albarka.”
33Masarawa suka iza mutanen su gaggauta, su fita ƙasar, gama suka ce, “Ƙarewa za mu yi idan ba ku tafi ba.” 34Sai jama’ar suka ɗauki ƙullun da ba a sa masa yisti ba, da ƙorensu na aikin ƙullun, suka ƙunshe a mayafansu, suka saɓa a kafaɗunsu. 35 Isra’ilawa kuwa suka yi yadda Musa ya faɗa musu, suka roƙi Masarawa kayan adonsu na azurfa da na zinariya, da kuma tufafi. 36Ubangiji ya sa jama’a su yi farin jini a wurin Masarawa, saboda haka Masarawa suka ba su abin da suka roƙa. Ta haka suka washe Masarawa.
Isra’ilawa Sun Fita Masar
37Isra’ilawa mutum wajen zambar ɗari shida maza (600,000), banda iyalansu, suka kama tafiya daga Ramases zuwa Sukkot. 38Babban taron tattarmuka kuma suka tafi tare da su, da garkunan tumaki da awaki, da na shanu tinjim. 39Suka toya abinci marar yisti da ƙullun da suka fita da shi daga Masar, gama ba su sa yisti cikin ƙullun ba domin an iza ƙyeyarsu, ba su sami damar dakatawa ba, ba su kuwa shirya wa kansu guzuri ba.
40 Zaman da Isra’ilawa suka yi a Masar shekara ce arbaminya da talatin. 41A ranar da shekara arbaminya da talatin ɗin nan suka cika, a ran nan ne dukan rundunar Ubangiji suka fita daga ƙasar Masar. 42Daren nan da Ubangiji ya sa domin ya fito da Isra’ilawa daga ƙasar Masar, daren ne wanda wajibi ne Isra’ilwa su kiyaye domin su girmama Ubangiji dukan zamanansu.
|