Skip to content

Alamar Adamu – Qur’ani

 Alamar Adamu – Taurat

(The Heights) Surat 7:19-26

“Kuma ya Ãdam! Ka zauna kai da matarka a Aljanna sai ku ci daga inda kuka so; kuma kada ku kusanci wannan itãciya, har ku kasance daga azzãlumai.”

Sai Shaiɗan ya sanya musu waswãsi dõmin ya bayyana musu abin da aka rufe daga barinsu, daga al’aurarsu, kuma ya ce: “Ubangijinku bai hanã ku daga wannan itãciya ba fãce dõmin kada ku kasance malã’iku biyu ko kuwa ku kasance daga madawwama.”

Kuma ya yi musu rantsuwa; Lalle ne nĩ, a gare ku, haƙĩƙa, daga mãsu nasĩha ne.

Sai ya saukar da su da rũɗi. Sa’an nan a lõkacin da suka ɗanɗani itãciyar, al’aurarsu ta bayyana gare su, kuma suka shiga sunã lĩƙawar ganye a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ubangjinsu Ya kira su: “Shin, Ban hanã ku ba daga waccan itãciya, kuma Na ce muku lalle ne Shaiɗan, a gare ku, maƙiyi ne bayyananne?”

Suka ce: “Ya Ubangijinmu! Mun zãlunci kanmu. Kuma idan ba Ka gãfarta mana ba, kuma Ka yi mana rahama, haƙĩƙa, Munã kasancẽwa daga mãsu hasãra.”

Ya ce: “Ku sauka, sãshenku zuwa ga sãshe yanã maƙiyi, kuma kunã da matabbata a cikin ƙasa, da ɗan jin dãɗi zuwa ga wani lõkabi.”

Ya ce: “A cikinta kuke rãyuwa, kuma a cikinta kuke mutuwa, kuma daga gare ta ake fitar da ku.”

Yã ɗiyan Ãdam! Lalle ne Mun saukar da wata tufa a kanku, tanã rufe muku al’aurarku, kuma da ƙawã. Kuma tufar taƙawa wancan ce mafi alhẽri. Wancan daga ãyõyin Allah ne, tsammãninsu sunã tunãwa!

(Ta Ha) Surat 20: 121-123

Sai suka ci daga gare ta, sabõda haka al’aurunsu suka bayyana, kuma suka shiga sunã lulluɓãwa a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ãdamu ya sãɓã wa Ubangijinsa, sabõda haka ya ɓace.

Sa’an nan kuma Ubangjinsa Ya zãɓẽ shi, Ya karɓi tũba gare shi, kuma Ya shiryar (da shi).

Ya ce: “Ku sauka kũ biyu daga gare ta gabã ɗaya, sãshenku yanã maƙiyi ga sãshe. To, imma dai wata shitiya ta jẽ muku daga gare Ni, to, wanda ya bi shiryarwãta, to, bã ya ɓacẽwa, kuma bã ya wahala.”

Farawa 2:15-17

15Ubangiji Allah ya ɗauki mutumin ya zaunar da shi cikin gonar Aidan ya noma ta, ya kiyaye ta. 16Ubangiji Allah ya yi wa mutumin umarni, ya ce, “Kana da ‘yanci ka ci daga kowane itace da yake a gonar, 17amma daga itacen sanin nagarta da mugunta ba za ka ci ba, gama a ranar da ka ci shi za ka mutu lalle.”

Farawa 3:1-23

1  Maciji ya fi kowace dabba da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa matar, “Ko Allah ya ce, ‘Ba za ku ci daga wani itacen da yake a gonar ba?’ ”
2Sai matar ta ce wa macijin, “Mā iya ci daga cikin itatuwan gonar, 3amma Allah ya ce, ‘Ba za ku ci daga cikin ‘ya’yan itacen da yake tsakiyar gonar ba, ba za ku taɓa shi ba, don kada ku mutu.’ ”
4Amma macijin ya ce wa matar, “Hakika ba za ku mutu ba. 5Gama Allah ya sani a ranar da kuka ci daga itacen nan idanunku za su buɗe, za ku kuwa zama kamar Allah, ku san nagarta da mugunta.”
6Matar ta ga yadda itacen yana da kyau, ‘ya’yansa kuma kyawawa, abin sha’awa ne kuma ga ido, abin marmari ne domin ba da hikima, ta tsinka daga ‘ya’yansa, ta kuwa ci, ta kuma bai wa mijinta waɗansu, shi kuma ya ci. 7Sai dukansu biyu idanunsu suka buɗe, sa’an nan suka gane tsirara suke, sai suka samo ganyayen ɓaure suka ɗinɗinka suka yi wa kansu sutura.
8Da suka ji motsin Allah yana yawo a gonar da sanyin la’asariya, sai mutumin da matarsa suka ɓuya wa Ubangiji Allah cikin itatuwan gonar. 9Amma Ubangiji Allah ya kira mutumin, ya ce, “Ina kake?”
10Sai ya ce, “Na ji motsinka cikin gonar, na kuwa ji tsoro, domin tsirara nake, na kuwa ɓoye kaina.”
11Ya ce, “Wa ya faɗa maka tsirara kake? Ko ka ci daga cikin itacen da na ce kada ka ci ne?”
12Mutumin ya ce, “Matan nan da ka ba ni, ita ce ta ba ni ‘ya’yan itacen, na kuwa ci.”
13  Ubangiji Allah kuma ya ce wa matar, “Mene ne wannan da kika yi?”
Matar ta ce, “Macijin ne ya yaudare ni, na kuwa ci.”
14Ubangiji Allah ya ce wa maciji, “Tun da ka aikata wannan, za a hukunta ka. Kai kaɗai wannan la’ana za ta bi. Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya, turɓaya za ka ci muddin rayuwarka. 15 Zan sa ƙiyayya tsakaninka da matar, tsakanin zuriyarka da zuriyarta, shi zai ƙuje kanka, kai za ka ƙuje diddigensa.”
16Ga matar kuwa ya ce, “Zan tsananta naƙudarki ainun, da azaba za ki haifi ‘ya’ya, duk da haka muradinki zai koma ga mijinki, zai kuwa mallake ki.”
17  Ga Adamu kuwa ya ce, “Ka kasa kunne ga muryar matarka, har ka ci daga ‘ya’yan itacen da na dokace ka, ‘Kada ka ci daga cikinsu.’ Tun da ka aikata wannan za a la’antar da ƙasa saboda kai, da wahala za ka ci daga cikinta muddin rayuwarka.
18“Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za ta ba ka, za ka kuwa ci ganyayen saurar. 19Za ka yi zuffa da aiki tuƙuru kafin ka sami abinci, har ka koma ƙasa, gama da ita aka siffata ka, kai turɓaya ne, ga turɓaya kuma za ka koma.” (2Tas 
20Mutumin ya sa wa matarsa suna Hawwa’u, domin ita ce uwar ‘yan adam. 21Ubangiji Allah kuwa ya yi wa mutumin da matarsa tufafi na fata, ya suturce su.
An Fitar da Adamu da Hawwa’u daga Gonar
22  Sa’an nan Ubangiji Allah ya ce, “Ga shi, mutum ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, ya san nagarta da mugunta, yanzu fa, kada ya miƙa hannunsa ya ɗiba daga cikin itacen rai ɗin nan, ya ci, ya rayu har abada.” 23Domin haka Ubangiji Allah ya fisshe shi daga cikin gonar Aidan, ya noma ƙasa, wato inda aka ɗauko shi.