Skip to content

Surat 5:28-31 (AL-MĀʾIDAH )

Farawa 4:1-12

28″Lalle ne idan ka shimfiɗa hannunka zuwa gare ni dõmin ka kashe ni, ban zama mai shimfiɗa hannuna zuwa gare ka ba dõmin in kashe ka. Lalle ne nĩ inã tsõron Allah Ubangijin tãlikai.29.

“Lalle ne nĩ inã nufin ka kõma da zunubina game da zunubinka, har ka kasance daga abõkan wuta. Kuma wannan shĩ ne sakamakon azzãlumai.”

.30.Sai ransa ya ƙawãtar masa kashewar ɗan’uwansa, sai kuwa ya kashe shi, sa’an nan ya wayi gari daga mãsu hasãra.

31.Sai Allah Ya aiki wani hankãka, yanã tõno a cikin ƙasa dõmin ya nuna masa yadda zai turbuɗe gãwar ɗan’uwansa. Ya ce: “Kaitõna! Nã kãsa in kasance kamar wannan hankãka dõmin in turbuɗe gãwar ɗan’uwana?” Sai ya wãyi gari daga mãsu nadãmã.

1Adamu kuwa ya san matarsa Hawwa’u, ta kuwa yi ciki, ta haifi Kayinu. Sai ta ce, “Na sami ɗa namiji da iznin Ubangiji.” 2Ta kuma haifi ɗan’uwansa Habila. Habila makiyayin tumaki ne, Kayinu kuwa manomi ne. 3Wata rana, sai Kayinu ya kawo sadaka ga Ubangiji daga amfanin gona. 4 Habila kuwa ya kawo nasa ƙosassu daga cikin ‘ya’yan fari na garkensa. Ubangiji kuwa ya kula da Habila da sadakarsa, 5amma Kayinu da sadakarsa, bai kula da su ba. Saboda haka Kayinu ya husata ƙwarai, har tsikar jikinsa ta tashi.
6Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Me ya sa ka husata, me kuma ya sa har tsikar jikinka ta tashi? 7In da ka yi daidai, ai, da ka yi murmushi. Amma tun da ka yi mugunta, to, zunubi zai yi fakonka don ya rinjaye ka kamar naman jeji. Yana so ya mallake ka, amma tilas ne ka rinjaye shi.”
8  Kayinu ya ce wa ɗan’uwansa Habila, “Mu tafi cikin saura.” A lokacin da suke cikin saura, sai Kayinu ya tasar wa ɗan’uwansa Habila, har ya kashe shi.
9Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Ina Habila ɗan’uwanka?”
Ya ce, “Ban sani ba, ni makiyayin ɗan’uwana ne?”
10  Sai Ubangiji ya ce, “Me ke nan ka yi? Muryar jinin ɗan’uwanka tana yi mini kuka daga ƙasa. 11Yanzu fa, kai la’ananne ne daga cikin ƙasar da ta buɗe baki, ta karɓi jinin ɗan’uwanka daga hannunka. 12In ka yi noma, ƙasar ba za ta ƙara ba ka cikakken amfaninta ba, za ka zama mai yawo barkatai, mai kai da kawowa a duniya.”