Skip to content

Qur’an- Surat 37: 102-110 (The Saffat).

Taurat: Genesis 22:1-18

102.To, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: “Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?” (Yãron) ya ce: “Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri.”103

To, a lõkacin da suka yi sallama, (Ibrahĩm) ya kãyar da shi ga gẽfen gõshinsa.

,104.Kuma Muka kira shi cẽwa “Ya Ibrahĩm!”

105.“Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin.” Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

106Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna.

107.Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma.

108. Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe.

109. Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm.

110.Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

1  Bayan waɗannan al’amura Allah ya jarraba Ibrahim ya ce masa, “Ibrahim!”
Sai ya ce, “Ga ni.”
2  Ya ce, “Ɗauki ɗanka, tilon ɗanka Ishaku, wanda kake ƙauna, ka tafi ƙasar Moriya, a can za ka miƙa shi hadayar ƙonawa a bisa kan ɗayan duwatsun da zan faɗa maka.”
3Sai Ibrahim ya tashi tun da sassafe, ya ɗaura wa jakinsa shimfiɗa ya kuwa ɗauki biyu daga cikin samarinsa tare da shi, da kuma ɗansa Ishaku, ya faskara itace na yin hadayar ƙonawa. Ya kuwa tashi ya tafi inda Allah ya faɗa masa. 4A rana ta uku Ibrahim ya ta da idanunsa ya hangi wurin daga nesa. 5Ibrahim ya ce wa samarinsa, “Ku tsaya nan wurin jakin, ni da saurayin za mu yi gaba mu yi sujada, sa’an nan mu komo wurinku.”
6Ibrahim ya ɗauki itacen hadayar ƙonawa, ya ɗora wa ɗansa Ishaku, shi kuma ya ɗauki wuta da wuƙa a hannunsa. Dukansu biyu kuwa suka tafi tare. 7Ishaku ya ce wa mahaifinsa Ibrahim, “Baba!”
Sai ya ce, “Ga ni, ɗana.”
Ya ce, “Ga wuta, ga itace, amma ina ragon hadayar ƙonawa?”
8Ibrahim ya ce, “Allah zai tanada wa kansa ragon hadayar ƙonawa, ya ɗana.” Sai su biyu suka tafi tare.
9  Sa’ad da suka zo wurin da Allah ya faɗa masa, sai Ibrahim ya gina bagade a can, ya jera itace a kai. Ya ɗaure Ishaku ɗansa, ya sa shi a bisa itacen bagaden. 10Sai Ibrahim ya miƙa hannu ya ɗauki wuƙar don ya yanka ɗansa. 11Amma mala’ikan Ubangiji ya yi kiransa daga sama, ya ce, “Ibrahim, Ibrahim!”
Sai ya ce, “Ga ni.”
12Ya ce, “Kada ka sa hannunka a kan saurayin, kada kuwa ka yi masa wani abu, gama yanzu na sani kai mai tsoron Allah ne, da yake ba ka ƙi ba da ɗanka, tilonka, a gare ni ba.” 13Ibrahim ya ta da idanunsa, ya duba, ga rago kuwa a bayansa, da ƙahoni a sarƙafe cikin kurmi. Ibrahim kuwa ya tafi ya kamo ragon, ya miƙa shi hadayar ƙonawa maimakon ɗansa. 14Sai Ibrahim ya sa wa wurin suna, “Ubangiji zai tanada,” kamar yadda ake faɗa har yau, “A bisa kan dutsen Ubangiji, za a tanada.”
15Mala’ikan Ubangiji kuma ya sāke kiran Ibrahim, kira na biyu daga sama, 16 ya ce, “Na riga na rantse da zatina, tun da ka yi wannan, ba ka kuwa ƙi ba da tilon ɗanka ba, 17 hakika zan sa maka albarka, zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sama, kamar yashi kuma a gāɓar teku. Zuriyarka za su mallaki ƙofar maƙiyanka, 18 ta wurin zuriyarka kuma al’umman duniya za su sami albarka, saboda ka yi biyayya da umarnina.”