Alamar Ludu – Qur’ani |
Alamar Lutu – Taurat
|
Surat 7:80-83 (AL-AʿRĀF) 80.Da Lũɗu, a lõkacin daya ce wa mutãnensa: “Shin, kunã jẽ wa alfãsha, bãbu kõwa da ya gabãce ku da ita daga halittu?” 81.“Lalle ne ku, haƙĩƙa kunã jẽ wa maza da sha’awa, baicin mata; Ã’a, kũ mutãne ne maɓarnata.” 82.Kuma bãbu abin da ya kasance jawãbin mutãnensa, fãce ɗai suka ce: “Ku fitar da su daga alƙaryarku: lalle ne sũ, wasumutãne ne mãsu da’awar tsarki!” 83.Sai Muka tsĩrar da shi, shĩ da iyãlansa, fãce matarsa, ta kasance daga mãsu wanzuwa. 84.Kuma Muka yi ruwa a kansu da wani irin ruwa; Sai ka dũba yadda ãƙibar mãsu laifi ta kasance! Surat 11:77-83 (The HŪD) 77.Kuma a lõkacin da manzanninMu suka je wa Lũɗu aka ɓãta masa rai game da su, ya, ƙuntata rai sabõda su. Ya ce: “Wannan yini ne mai tsananin masĩfa.” 78.Kuma mutãnensa suka je masa sunã gaggãwa zuwa gare shi, kuma a gabãni, sun kasance sunã aikatãwar mũnãnan ayyuka. Ya ce: “Yã mutãnẽna! waɗannan, ‘yã’yã na sũ ne mafiya tsarki a gare ku. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku wulãkantã ni a cikin bãƙĩna. Shin, bãbu wani namiji shiryayye daga gare ku?” 79.Suka ce: “Lalle, haƙĩƙa kã sani, bã mu da wani hakki a cikin ‘ya’yanka, kuma lalle kai haƙĩƙa, kanã sane da abin da muke nufi.” 80.Ya ce: “Dã dai inã da wani ƙarfi game da ku, kõ kuwa inã da gõyon bãya daga wani rukuni mai ƙarfi?” 81.(Manzannin) Suka ce: “Yã Lũɗu! Lalle mũ, manzannin Ubangijinka ne. Bã zã su iya sãduwa zuwa gare ka ba. Sai ka yi tafiyarka a wani yankin dare da iyãlinka, kuma kada wani daga gare ku ya waiwaya fãce mãtarka. Lalle ne abin da ya same su mai sãmunta ne. Lalle wa’adinsu lõkacin sãfiya ne. Shin lõkacin sãfiya bã kusa ba ne?” 82.Sa’an nan a lõkacin da umurninMu ya je, Muka sanya na samanta ya zama na ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu a kanta (ƙasar Lũɗu) daga taɓocũrarre. 83.Alamtacce a wurin Ubangijinka. Kuma ita (ƙasar Lũɗu) ba ta zama mai nĩsa ba daga azzãlumai (kuraishãwa). |
Genesis 19
1Mala’ikun nan biyu kuwa suka isa Saduma da maraice, Lutu kuwa yana zaune a ƙofar Saduma. Sa’ad da Lutu ya gan su sai ya miƙe ya tarye su. Sai ya yi ruku’u a gabansu. 2ya ce, “Iyayengijina, ina roƙonku ku ratse zuwa gidan baranku, ku kwana, ku wanke ƙafafunku, da sassafe kuma sai ku kama hanyarku.”
Suka ce, “A’a, a titi za mu kwana.” 3Amma ya nace musu ƙwarai, sai suka ratse suka shiga gidansa, ya shirya musu liyafa, ya toya musu abinci marar yisti, suka ci.
4Amma kafin su shiga barci, mutanen birnin Saduma, samari da tsofaffi, dukan mutane gaba ɗaya suka kewaye gidan. 5 Suka kira Lutu suka ce, “Ina mutanen da suka zo wurinka da daren nan? Fito mana da su waje, don mu yi luɗu da su.”
6Lutu ya fita daga cikin gida ya rufe ƙofar a bayansa ya je wurin mutane, 7ya ce, “Ina roƙonku ‘yan’uwana, kada ku aikata mugunta haka. 8Ga shi, ina da ‘ya’ya mata biyu waɗanda ba su san namiji ba, bari in fito muku da su waje, ku yi yadda kuka ga dama da su, sai dai kada ku taɓa mutanen nan ko kaɗan, gama sun shiga ƙarƙashin inuwata.”
9Amma suka ce, “Ba mu wuri!” Suka kuma ce, “Wannan mutum ya zo baƙunci ne, yanzu kuma zai zama alƙali! Yanzu za mu yi maka fiye da yadda za mu yi musu.” Sai suka tutture Lutu suka matsa kusa don su fasa ƙofar. 10Amma baƙin suka miƙa hannunsu, suka shigar da Lutu cikin gida inda suke, suka rufe ƙofa. 11 Sai suka bugi mutanen da suke ƙofar gidan da makanta, ƙanana da manya duka, har suka gajiyar da kansu suna laluba inda ƙofa take.
Lutu ya Bar Saduma
12Mutanen suka ce wa Lutu, “Kana da wani naka a nan? Ko surukai, ko ‘ya’ya mata da maza, ko dai kome naka da yake cikin birnin? Fito da su daga wurin, 13gama muna gab da hallaka wurin nan, domin kukan da ake yi a kan mutanen ya yi yawa a gaban Ubangiji. Ubangiji kuwa ya aiko mu, mu hallaka birnin.”
14Sai Lutu ya fita ya faɗa wa surukansa waɗanda za su auri ‘ya’yansa mata, “Tashi, ku fita daga wannan wuri, gama Ubangiji yana gab da hallaka birnin.” Amma sai surukansa suka aza wasa yake yi.
15Sa’ad da safiya ta gabato, mala’ikun suka hanzarta Lutu, suna cewa, “Tashi, ka ɗauki matarka da ‘ya’yanka biyu mata da suke nan, don kada a shafe ku saboda zunubin birnin.” 16Amma da ya yi ta ja musu rai, sai mutanen suka kama hannunsa, da na matarsa, da na ‘ya’yansa biyu mata, saboda jinƙan da Ubangiji ya yi masa, suka fitar da shi suka kai shi a bayan birnin. 17Sa’ad da suka fitar da shi, suka ce, “Ka gudu domin ranka, kada ka waiwaya baya, ko ka tsaya ko’ina cikin kwari, gudu zuwa tuddai domin kada a hallaka ka.”
18Sai Lutu ya ce musu, “A’a, ba haka ba ne iyayengijina, 19ga shi, baranka ya sami tagomashi a idonka, ka kuwa nuna mini babban alheri da ka ceci raina, amma ba zan iya in kai tuddan ba, kada hatsarin ya same ni a hanya, in mutu. 20Ga ɗan gari can ya fi kusa inda zan gudu in fake. Bari in gudu zuwa can, in tsirar da raina.”
21Sai ya ce masa, “Na yarda da abin da ka ce, ba zan hallakar da garin da ka ambata ba. 22Gaggauta, ka gudu zuwa can, ba zan yi kome ba sai ka isa wurin.” Domin haka aka kira sunan garin Zowar.
Halakar Saduma da Gwamrata
23Da hantsi Lutu ya isa Zowar. 24 Sai Ubangiji ya yi ta zuba wa Saduma da Gwamrata wutar kibritu daga sama, 25ya hallakar da waɗannan birane, da dukan kwarin, da dukan mazaunan biranen, da tsire-tsire. 26 Amma matar Lutu da take bin bayansa ta waiwaya, sai ta zama surin gishiri.
|
From Books
Qur’ani |
Taurat |
(The Hud) Surat 11:25-48 Kuma haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutanensa, (ya ce): “Lalle ne ni, a gare ku mai gargaɗi bayyananne ne.” “Kada ku bautã wa kõwa fãce Allah. Lalle nĩ, inã jin tsõron azãbar yini mai raɗaɗi a kanku.” Sai mashãwarta waɗanda suka kãfirta, daga mutãnensa, suka ce: “Bã mu ganin ka fãce mutum kake kamarmu, kuma ba mu ganin wani ya bĩ ka fãce waɗanda suke sũ ƙasƙantattunmu ne marasa tunani. Kuma bã mu ganin wata falalã agare ka a kanmu. Ã’a, Munã zaton ku maƙaryata ne.” Ya ce: “Ya mutãnena! Shin, kun gani idan na kasance a kan wata hujja bayyananna daga Ubangijina, kuma Yã bã ni wata Rahama daga wurinSa, Sa’an nan aka rufe ta (ita Rahamar) daga gare ku, shin, zã mu tĩlasta mukuita, alhãli kuwa kũ mãsu ƙi gare ta ne? “Kuma yã mutãnena! Bã zan tambaye ku wata dũkiya ba akansa, ijãrata ba ta zama ba, fãce daga Allah, kuma ban zama mai kõrar waɗanda suka yĩ ĩmãni ba. Haƙĩƙa sũ, mãsu haɗuwa da Ubangijinsu ne, kuma amma ni, inã ganin ku mutãne ne jãhilai.” “Kuma ya mutãnena! Wãne ne yake taimakõna daga Allah idan na kõre su? Ashe, bã ku tunãni?” “Kuma bã ni ce muku a wurĩna taskõkin Allah suke kuma bã inã sanin gaibi ba ne. Kuma ba inã cẽwa ni Malã’ika ba ne. Kuma ba ni cẽwa ga waɗanda idãnunku suke wulãkantãwa, Allah bã zai bã su alhẽri ba. Allah ne Mafi sani ga abin da yake cikin zukatansu. Lalle ne ni, idan (nã yi haka) dã ina daga cikin azzalumai.” Suka ce: “Yã Nũhu, lalle ne kã yi jayayya da mu, sa’an nan kã yawaita yi mana jidãli, to, ka zõ mana da abin da kake yi mana wa’adi idan kã kasance daga mãsu gaskiya.” Ya ce: “Allah kawai ne Yake zo muku da shi idan Ya so. Kuma ba ku zama mabuwãya ba.” “Kuma nasĩhãta bã zã ta amfãne ku ba, idan nã yi nufin in yi muku nasĩha, idan Allah Yakasance Yanã nufin Ya halaka ku. Shĩ ne Ubangijinku, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.” Ko sunã cẽwa: (Nũhu) ya ƙirƙira shi. Ka ce: “Idan nĩ (Nũhu) na ƙirƙira shi to, laifĩnã a kaina yake, kuma nĩ mai barrantã ne daga abin da kuke yi na laifi.” Kuma aka yi wahayi zuwa ga Nũhu cẽwa: Lalle ne bãbu mai yin ĩmãni daga mutãnenka fãce wanda ya riga ya yi ĩmãnin, sabõdahaka kada ka yi baƙin ciki da abin da suka kasance sunã aikatãwa. Kuma ka sassaƙa jirgi da kyau a kan idanunMu da wahayinMu, kuma kada ka yi Mini magana a cikin sha’anin waɗanda suka kãfirta, lalle ne sũ, waɗanda akenutsarwa ne. Kuma Yanã sassaƙa jirgin cikin natsuwa, kuma a kõ yaushe waɗansu shugabanni daga mutãnensa suka shũɗe a gabansa, sai su yi izgili gare shi. Ya ce: “Idan kun yi izgili gare mu, to, haƙĩƙa mũ mã zã mu yi izgili gare ku, kamar yadda kuke yin izgili. “Sa’an nan da sannu zã ku san wanda azãba zã ta zo masa, ta wulakantã shi (a dũniya), kuma wata azãba zaunanna ta sauka a kansa (a Lãhira).” Har a lõkacin da umurninMu ya je, kuma tandã ta ɓulɓula. Muka ce: “Ka ɗauka, a cikinta, daga kõme, ma’aura biyu, da kuma iyalanka, fãce wanda magana ta gabãta a kansa, da wanda ya yi ĩmãni.” Amma kuma bãbu waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi fãce kaɗan.” Kuma ya ce: “Ku hau a cikinta, da sũnan Allah magudãnarta da matabbatarta. Lalle ne Ubangijĩna, haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.” Kuma ita tanã gudãna da su a cikin tãguwar ruwa kamai duwãtsu, sai Nũhu ya kirãyi ɗansa alhãli, kuwa ya kasance can wuri mai nĩsa. “Yã ƙaramin ɗãnã! zo ka hau tãre da mu, kuma kada ka kasance tãre da kãfirai!” Ya ce: “Zan tattara zuwa ga wani dũtse ya tsare ni daga ruwan.” (Nũhu) ya ce: “Bãbu mai tsarẽwa a yau daga umurnin Allah fãce wanda Ya yi wa rahama.” Sai taguwar ruwa ta shãmakace a tsakãninsu, sai ya kasance daga waɗanda aka nutsar. Kuma aka ce: “Yã ƙasa! Ki haɗiye ruwanki, kuma yã sama! Ki kãme.”Kuma aka faƙar da ruwan kuma aka hukunta al’amarin, kuma Jirgin ya daidaita a kan Jũdiyyi, kuma aka ce: “Nĩsa ya tabbata ga mutãne azzãlumai.” Kuma Nũhu ya kira Ubangijinsa, sa’an nan ya ce: “Yã Ubangijina! Lalle ne ɗãna na daga iyãlĩna! Kuma haƙĩƙa wa’adinKa gaskiya ne, kuma Kai ne Mafi hukuncin mãsu yin hukunci.” Ya ce: “Yã Nũhu! Lalle ne shi bã ya a ciki iyãlanka, lalle ne shĩ, aiki ne wanda ba na ƙwarai ba, sabõda haka kada ka tambaye Ni abin da bã ka da ilmi a kansa. Haƙĩƙa, Nĩ Inã yi maka gargaɗi kada ka kasance daga jãhilai.” Ya ce: “Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, inã nẽman tsari gare Ka da in tambaye Ka abin da bã ni da wani ilmi a kansa. Idan ba Ka gãfarta mini ba, kuma Ka yi mini rahama, zan kasance daga mãsu hasãra.” Aka ce: “Ya Nũhu! Ka sauka da aminci da, a gare Mu da albarka a kanka, kuma rahama ta tabbata a kan waɗansu al’ummõmi daga waɗanda suke tãre da kai. Da waɗansu al’ummõmi da zã Mu jiyar da su dãɗi, sa’an nan kuma azãba mai raɗaɗi ta shafe su daga gare Mu.” (AL-AʿRĀF) 7: 59-64 59.Lalle ne, haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnẽnsa, sai ya ce: “Yã mutãnẽna! Ku bauta waAllah! Bã ku da wani abin bautãwa waninSa. Lalle ne nĩ, inã yimuku tsõron azãbar wani Yini mai girma.” 60.Mashawarta daga mutãnensa suka ce: “Lalle ne mu, haƙĩƙa, Munã ganin ka a cikin ɓata bayyananniya.” 61.Ya ce: “Yã mutãnena! Bãbu ɓata guda gare ni, kuma amma nĩ Manzo ne daga ubangijin halittu!” 62.“Inã iyar muku da sãƙonnin Ubangijina; kuma inã yi muku nasĩha, kuma inã sani, daga Allah, abin da ba ku sani ba. 63.“Shin, kunã mãmãkin cẽwa ambato yã zo muku daga Ubangijinku a kan wani namiji, daga gare ku, dõmin ya yi muku gargaɗi, kuma dõmin ku yi taƙawa, kuma tsammãninku anã jin ƙanku?” 64.Sai suka ƙaryata shi, sa’an nan Muka tsĩrar da shi da waɗanda suke tãre da shi, a cikin jirgin; kuma Muka nutsar da waɗanda suka ƙaryata shi game da ãyõyinMu. Lalle ne sũ, sun kasance wasu mutãne ɗĩmautattu. |
Genesis 6-8 Da mutane suka fara yawaita a duniya suka kuwa haifi ‘ya’ya mata, 2sai ‘ya’yan Allah suka ga ‘yan matan mutane kyawawa ne, suka zaɓi waɗanda suke so, suka aura. 3Sai Ubangiji ya ce, “Numfashina ba zai zauna cikin mutum har abada ba, gama shi mai mutuwa ne. Nan gaba kwanakinsa ba zai ɗara shekara ɗari da ashirin ba.” 4 A waɗannan kwanaki kuwa, ‘ya’yan Allah suka shiga wurin ‘yan matan mutane, suka kuwa haifa musu ‘ya’ya. Su ne manya manyan mutanen dā, shahararru.
5 Ubangiji kuwa ya ga muguntar mutum ta ƙasaita a duniya, dukan zace-zacen tunanin zuciyarsa kuma mugunta ne kullayaumin. 6Ubangiji ya damu da ya yi mutum a duniya, abin ya ɓata masa zuciya ƙwarai. 7Sai Ubangiji ya ce, “Zan shafe mutum daga duniya, mutum da dabba, da masu rarrafe, da tsuntsayen sararin sama, gama na damu da na halicce su.” 8Amma Nuhu ya sami tagomashi a gaban Ubangiji.
9 Waɗannan su ne zuriyar Nuhu. Nuhu adali ne, salihi ne kuma a cikin zamaninsa. Nuhu ya yi tafiya tare da Allah. 10Nuhu kuwa ya haifi ‘ya’ya uku, Shem, da Ham, da Yafet. 11Amma dukan sauran mutane mugaye ne a gaban Allah, muguntarsu kuwa ta bazu ko’ina. 12Allah ya dubi duniya, ga shi kuwa ta ɓaci, gama dukan mutane sun lalatar da tafarkunsu a cikin duniya.
Nuhu ya Sassaƙa Jirgi
13Allah ya ce wa Nuhu, “Na riga na yi niyyar hallaka dukan talikai, gama duniya tana cike da ayyukansu na zunubi. 14Ka sassaƙa wa kanka jirgi na itacen gofer, ka yi ɗakuna a cikin jirgin, ka dalaye cikinsa da bayansa da ƙaro. 15Ga yadda za ka sassaƙa shi, tsawon jirgin ƙafa ɗari huɗu da hamsin, faɗinsa ƙafa saba’in da biyar, tsayinsa ƙafa arba’in da biyar. 16Ka yi wa jirgin rufe, ka bar inci goma sha takwas tsakanin rufin da gyaffansa. Ka yi shi hawa uku, ka yi ƙofa a gefe. 17Gama ga shi, zan kawo rigyawa bisa duniya, ta hallaka dukan mai numfashin rai da yake ƙarƙashin sama, dukan abin da yake a duniya zai mutu. 18Amma ni zan kafa alkawari tsakanina da kai, za ka shiga cikin jirgin, kai da ‘ya’yanka, da matarka, da matan ‘ya’yanka tare da kai. 19Daga kowane irin mai rai kuma za ka shigar da biyu biyu a cikin jirgin, domin su rayu tare da kai, amma su kasance namiji da ta mace. 20Tsuntsaye bisa ga irinsu, dabbobi bisa ga irinsu, da kowane irin mai rarrafe a ƙasa bisa ga irinsa, biyu biyu na kowane iri za su shiga tare da kai, su rayu. 21Ka ɗauki kuma kowane irin abinci da ake ci, ka tanada, zai kuwa zama abincinka da nasu.” 22 Nuhu ya yi dukan abin da Allah ya umarce shi.
1Sai Ubangiji ya ce wa Nuhu, “Ka shiga jirgin, kai da iyalinka duka, gama na ga a wannan zamani, kai adali ne a gare ni. 2Daga cikin dabbobi masu tsarki ka ɗauki bakwai bakwai, namiji da ta mace, marasa tsarki kuwa namiji da ta mace, 3da kuma tsuntsayen sararin sama bakwai bakwai, namiji da ta mace, domin a wanzar da irinsu a duniya duka. 4Gama da sauran kwana bakwai kāna in sa a yi ruwa a duniya yini arba’in da dare arba’in. Dukan abu mai rai wanda na yi zan shafe shi daga duniya.” 5Nuhu kuwa ya yi dukan abin da Ubangiji ya umarce shi.
6Nuhu yana da shekara ɗari shida lokacin da Ruwan Tsufana ya kwararo bisa duniya. 7Nuhu da ‘ya’yansa da matarsa, da matan ‘ya’yansa tare da shi suka shiga jirgi, domin su tsira daga Ruwan Tsufana. 8Daga dabbobi masu tsabta da marasa tsabta, da na tsuntsaye, da na kowane mai rarrafe a ƙasa, 9biyu biyu, namiji da mata, suka shiga jirgi tare da Nuhu, kamar yadda Allah ya umarci Nuhu. 10Sai bayan kwana bakwai ruwayen suka kwararo bisa duniya.
11 A ranar sha bakwai ga wata na biyu, na shekara ta ɗari shida na rayuwar Nuhu, a ran nan sai dukan maɓuɓɓugai na manyan zurfafa suka fashe, tagogin sammai suka buɗe. 12Ruwa yana ta kwararowa bisa duniya yini arba’in da dare arba’in.
13A wannan rana Nuhu da ‘ya’yansa, Shem, da Ham, da Yafet, da matar Nuhu da matan ‘ya’yansa tare suka shiga jirgin, 14su da kowace dabbar jeji bisa ga irinta, da dukan dabbobin gida bisa ga irinsu, da kowane mai rarrafe wanda yake rarrafe bisa ƙasa, bisa ga irinsa, da kowane tsuntsun gida da na jeji wanda yake numfashi. 15-16Su waɗanda suka shiga, namiji ne da ta mace na kowane taliki, suka shiga jirgin kamar yadda Allah ya umarce shi. Sai Ubangiji ya kulle jirgi daga baya.
17Aka yi ta kwararo ruwa bisa duniya har kwana arba’in, ruwayen kuwa suka ƙaru, har suka ɗaga jirgin sama, ya kuwa tashi can ƙoli birbishin duniya. 18Ruwa ya bunƙasa ya ƙaru ƙwarai bisa duniya, jirgin kuwa ya yi ta yawo bisa fuskar ruwaye. 19Ruwa kuwa ya bunƙasa ainun a bisa duniya, har ya rufe kawunan dukan duwatsu masu tsayi da yake ƙarƙashin sammai duka. 20Ruwa ya bunƙasa bisa duwatsu ya yi musu zara da ƙafa ashirin da biyar. 21Duk taliki wanda yake motsi bisa duniya ya mutu, da tsuntsaye, da dabbobin gida, da na jeji, da dukan masu rarrafe waɗanda suke rarrafe bisa duniya, da kowane mutum, 22da kowane abin da yake bisa sandararriyar ƙasa wanda yake da numfashin rai cikin kafafen hancinsa ya mutu. 23Ubangiji ya shafe kowane mai rai wanda yake bisa ƙasa, da mutum, da dabba, da masu rarrafe, da tsuntsayen sararin sama, an shafe su daga duniya. Nuhu kaɗai aka bari, da waɗanda suke tare da shi cikin jirgi. 24Ruwa kuma ya mamaye duniya har kwana ɗari da hamsin.
1Allah kuwa ya tuna da Nuhu da dukan dabbobin gida da na jeji waɗanda suke cikin jirgi tare da shi. Allah ya sa iska ta hura bisa duniya, ruwaye suka janye. 2Maɓuɓɓugan zurfafa da tagogin sammai suka rufe, aka dakatar da ruwa daga sammai, 3ruwa ya yi ta janyewa daga duniya. Bayan kwana ɗari da hamsin sai ruwa ya ragu. 4Ya zama kuwa a ran sha bakwai ga wata na bakwai, sai jirgin ya tafi ya tsaya bisa kan dutsen Ararat. 5Ruwa ya yi ta raguwa har wata na goma. A ran ɗaya ga wata na goma, sai kawunan duwatsu suka ɓullo.
6A ƙarshen kwana arba’in Nuhu ya buɗe tagar jirgin da ya yi, 7sai ya saki hankaka. Hankaka ya yi ta kai da kawowa har lokacin da ruwan ya ƙafe a duniya. 8Sai kuma ya aiki kurciya ta gani ko ruwa ya janye, 9amma kurciyar ba ta sami inda za ta sauka ba, sai ta komo wurinsa cikin jirgi, gama har yanzu ruwa na rufe ƙasa duka. Sai ya miƙa hannunsa ya ɗauko ta ya shigar da ita cikin jirgi tare da shi. 10Ya jira kuma har kwana bakwai, sai kuma ya sāke aiken kurciyar daga cikin jirgin. 11Kurciyar kuwa ta komo wurinsa da maraice, ga shi kuwa, a bakinta sabon tohon zaitun wanda ta tsinko, domin haka Nuhu ya gane ruwa ya janye daga duniya. 12Sai ya sāke dakatawa har kwana bakwai, ya kuma aiki kurciya, amma ba ta ƙara komowa wurinsa ba.
13A rana ta fari ga wata na fari na shekara ta ɗari shida da ɗaya na Nuhu, ruwa ya ƙafe a duniya. Sai Nuhu ya buɗe murfin jirgin, ya duba, sai ga ƙasa busasshiya. 14Ran ashirin da bakwai ga wata na biyu, duniya ta bushe.
15Sa’an nan sai Allah ya ce wa Nuhu, 16“Fito daga cikin jirgi, kai da matarka, da ‘ya’yanka da matan ‘ya’yanka tare da kai. 17Ka fito da kowane abu mai rai tare da kai, dukan talikai, wato tsuntsaye, da dabbobi, da kowane abu mai rarrafen da yake rarrafe bisa ƙasa, domin su hayayyafa su kuma riɓaɓɓanya a duniya.” 18Sai Nuhu ya fito, da ‘ya’yansa, da matarsa da matan ‘ya’yansa tare da shi, 19da kowace irin dabba, da kowane mai rarrafe, da kowane irin tsuntsu, da kowane irin abin da yake motsi a bisa duniya, suka fito daga jirgi ɗaki ɗaki bisa ga irinsu.
Nuhu ya Miƙa Hadaya
20Nuhu ya gina wa Ubangiji bagade, ya ɗiba daga cikin kowace irin dabba mai tsarki, da kowane tsuntsu mai tsarki, ya miƙa hadayu na ƙonawa a bisa bagaden. 21Sa’ad da Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce, “Ba zan ƙara la’anta ƙasa sabili da mutum ba, ko da yake zace-zacen zuciyar mutum mugunta ne tun daga ƙuruciyarsa. Ba zan kuma ƙara hallaka kowane mai rai ba kamar yadda na yi a dā. 22Muddin duniya tana nan, lokacin shuka da lokacin girbi, damuna da rani, yini da dare, ba za su daina ba.
|
Surat 5:28-31 (AL-MĀʾIDAH ) |
Farawa 4:1-12 |
28″Lalle ne idan ka shimfiɗa hannunka zuwa gare ni dõmin ka kashe ni, ban zama mai shimfiɗa hannuna zuwa gare ka ba dõmin in kashe ka. Lalle ne nĩ inã tsõron Allah Ubangijin tãlikai.29.
“Lalle ne nĩ inã nufin ka kõma da zunubina game da zunubinka, har ka kasance daga abõkan wuta. Kuma wannan shĩ ne sakamakon azzãlumai.” .30.Sai ransa ya ƙawãtar masa kashewar ɗan’uwansa, sai kuwa ya kashe shi, sa’an nan ya wayi gari daga mãsu hasãra. 31.Sai Allah Ya aiki wani hankãka, yanã tõno a cikin ƙasa dõmin ya nuna masa yadda zai turbuɗe gãwar ɗan’uwansa. Ya ce: “Kaitõna! Nã kãsa in kasance kamar wannan hankãka dõmin in turbuɗe gãwar ɗan’uwana?” Sai ya wãyi gari daga mãsu nadãmã. |
1Adamu kuwa ya san matarsa Hawwa’u, ta kuwa yi ciki, ta haifi Kayinu. Sai ta ce, “Na sami ɗa namiji da iznin Ubangiji.” 2Ta kuma haifi ɗan’uwansa Habila. Habila makiyayin tumaki ne, Kayinu kuwa manomi ne. 3Wata rana, sai Kayinu ya kawo sadaka ga Ubangiji daga amfanin gona. 4 Habila kuwa ya kawo nasa ƙosassu daga cikin ‘ya’yan fari na garkensa. Ubangiji kuwa ya kula da Habila da sadakarsa, 5amma Kayinu da sadakarsa, bai kula da su ba. Saboda haka Kayinu ya husata ƙwarai, har tsikar jikinsa ta tashi.
6Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Me ya sa ka husata, me kuma ya sa har tsikar jikinka ta tashi? 7In da ka yi daidai, ai, da ka yi murmushi. Amma tun da ka yi mugunta, to, zunubi zai yi fakonka don ya rinjaye ka kamar naman jeji. Yana so ya mallake ka, amma tilas ne ka rinjaye shi.”
8 Kayinu ya ce wa ɗan’uwansa Habila, “Mu tafi cikin saura.” A lokacin da suke cikin saura, sai Kayinu ya tasar wa ɗan’uwansa Habila, har ya kashe shi.
9Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Ina Habila ɗan’uwanka?”
Ya ce, “Ban sani ba, ni makiyayin ɗan’uwana ne?”
10 Sai Ubangiji ya ce, “Me ke nan ka yi? Muryar jinin ɗan’uwanka tana yi mini kuka daga ƙasa. 11Yanzu fa, kai la’ananne ne daga cikin ƙasar da ta buɗe baki, ta karɓi jinin ɗan’uwanka daga hannunka. 12In ka yi noma, ƙasar ba za ta ƙara ba ka cikakken amfaninta ba, za ka zama mai yawo barkatai, mai kai da kawowa a duniya.”
|