Alamar Adamu – Qur’ani |
Alamar Adamu – Taurat |
(The Heights) Surat 7:19-26 “Kuma ya Ãdam! Ka zauna kai da matarka a Aljanna sai ku ci daga inda kuka so; kuma kada ku kusanci wannan itãciya, har ku kasance daga azzãlumai.” Sai Shaiɗan ya sanya musu waswãsi dõmin ya bayyana musu abin da aka rufe daga barinsu, daga al’aurarsu, kuma ya ce: “Ubangijinku bai hanã ku daga wannan itãciya ba fãce dõmin kada ku kasance malã’iku biyu ko kuwa ku kasance daga madawwama.” Kuma ya yi musu rantsuwa; Lalle ne nĩ, a gare ku, haƙĩƙa, daga mãsu nasĩha ne. Sai ya saukar da su da rũɗi. Sa’an nan a lõkacin da suka ɗanɗani itãciyar, al’aurarsu ta bayyana gare su, kuma suka shiga sunã lĩƙawar ganye a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ubangjinsu Ya kira su: “Shin, Ban hanã ku ba daga waccan itãciya, kuma Na ce muku lalle ne Shaiɗan, a gare ku, maƙiyi ne bayyananne?” Suka ce: “Ya Ubangijinmu! Mun zãlunci kanmu. Kuma idan ba Ka gãfarta mana ba, kuma Ka yi mana rahama, haƙĩƙa, Munã kasancẽwa daga mãsu hasãra.” Ya ce: “Ku sauka, sãshenku zuwa ga sãshe yanã maƙiyi, kuma kunã da matabbata a cikin ƙasa, da ɗan jin dãɗi zuwa ga wani lõkabi.” Ya ce: “A cikinta kuke rãyuwa, kuma a cikinta kuke mutuwa, kuma daga gare ta ake fitar da ku.” Yã ɗiyan Ãdam! Lalle ne Mun saukar da wata tufa a kanku, tanã rufe muku al’aurarku, kuma da ƙawã. Kuma tufar taƙawa wancan ce mafi alhẽri. Wancan daga ãyõyin Allah ne, tsammãninsu sunã tunãwa! (Ta Ha) Surat 20: 121-123 Sai suka ci daga gare ta, sabõda haka al’aurunsu suka bayyana, kuma suka shiga sunã lulluɓãwa a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ãdamu ya sãɓã wa Ubangijinsa, sabõda haka ya ɓace. Sa’an nan kuma Ubangjinsa Ya zãɓẽ shi, Ya karɓi tũba gare shi, kuma Ya shiryar (da shi). Ya ce: “Ku sauka kũ biyu daga gare ta gabã ɗaya, sãshenku yanã maƙiyi ga sãshe. To, imma dai wata shitiya ta jẽ muku daga gare Ni, to, wanda ya bi shiryarwãta, to, bã ya ɓacẽwa, kuma bã ya wahala.” |
Farawa 2:15-17 15Ubangiji Allah ya ɗauki mutumin ya zaunar da shi cikin gonar Aidan ya noma ta, ya kiyaye ta. 16Ubangiji Allah ya yi wa mutumin umarni, ya ce, “Kana da ‘yanci ka ci daga kowane itace da yake a gonar, 17amma daga itacen sanin nagarta da mugunta ba za ka ci ba, gama a ranar da ka ci shi za ka mutu lalle.” Farawa 3:1-23 1 Maciji ya fi kowace dabba da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa matar, “Ko Allah ya ce, ‘Ba za ku ci daga wani itacen da yake a gonar ba?’ ”
2Sai matar ta ce wa macijin, “Mā iya ci daga cikin itatuwan gonar, 3amma Allah ya ce, ‘Ba za ku ci daga cikin ‘ya’yan itacen da yake tsakiyar gonar ba, ba za ku taɓa shi ba, don kada ku mutu.’ ”
4Amma macijin ya ce wa matar, “Hakika ba za ku mutu ba. 5Gama Allah ya sani a ranar da kuka ci daga itacen nan idanunku za su buɗe, za ku kuwa zama kamar Allah, ku san nagarta da mugunta.”
6Matar ta ga yadda itacen yana da kyau, ‘ya’yansa kuma kyawawa, abin sha’awa ne kuma ga ido, abin marmari ne domin ba da hikima, ta tsinka daga ‘ya’yansa, ta kuwa ci, ta kuma bai wa mijinta waɗansu, shi kuma ya ci. 7Sai dukansu biyu idanunsu suka buɗe, sa’an nan suka gane tsirara suke, sai suka samo ganyayen ɓaure suka ɗinɗinka suka yi wa kansu sutura.
8Da suka ji motsin Allah yana yawo a gonar da sanyin la’asariya, sai mutumin da matarsa suka ɓuya wa Ubangiji Allah cikin itatuwan gonar. 9Amma Ubangiji Allah ya kira mutumin, ya ce, “Ina kake?”
10Sai ya ce, “Na ji motsinka cikin gonar, na kuwa ji tsoro, domin tsirara nake, na kuwa ɓoye kaina.”
11Ya ce, “Wa ya faɗa maka tsirara kake? Ko ka ci daga cikin itacen da na ce kada ka ci ne?”
12Mutumin ya ce, “Matan nan da ka ba ni, ita ce ta ba ni ‘ya’yan itacen, na kuwa ci.”
13 Ubangiji Allah kuma ya ce wa matar, “Mene ne wannan da kika yi?”
Matar ta ce, “Macijin ne ya yaudare ni, na kuwa ci.”
14Ubangiji Allah ya ce wa maciji, “Tun da ka aikata wannan, za a hukunta ka. Kai kaɗai wannan la’ana za ta bi. Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya, turɓaya za ka ci muddin rayuwarka. 15 Zan sa ƙiyayya tsakaninka da matar, tsakanin zuriyarka da zuriyarta, shi zai ƙuje kanka, kai za ka ƙuje diddigensa.”
16Ga matar kuwa ya ce, “Zan tsananta naƙudarki ainun, da azaba za ki haifi ‘ya’ya, duk da haka muradinki zai koma ga mijinki, zai kuwa mallake ki.”
17 Ga Adamu kuwa ya ce, “Ka kasa kunne ga muryar matarka, har ka ci daga ‘ya’yan itacen da na dokace ka, ‘Kada ka ci daga cikinsu.’ Tun da ka aikata wannan za a la’antar da ƙasa saboda kai, da wahala za ka ci daga cikinta muddin rayuwarka.
18“Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za ta ba ka, za ka kuwa ci ganyayen saurar. 19Za ka yi zuffa da aiki tuƙuru kafin ka sami abinci, har ka koma ƙasa, gama da ita aka siffata ka, kai turɓaya ne, ga turɓaya kuma za ka koma.” (2Tas
20Mutumin ya sa wa matarsa suna Hawwa’u, domin ita ce uwar ‘yan adam. 21Ubangiji Allah kuwa ya yi wa mutumin da matarsa tufafi na fata, ya suturce su.
An Fitar da Adamu da Hawwa’u daga Gonar
22 Sa’an nan Ubangiji Allah ya ce, “Ga shi, mutum ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, ya san nagarta da mugunta, yanzu fa, kada ya miƙa hannunsa ya ɗiba daga cikin itacen rai ɗin nan, ya ci, ya rayu har abada.” 23Domin haka Ubangiji Allah ya fisshe shi daga cikin gonar Aidan, ya noma ƙasa, wato inda aka ɗauko shi.
|
Home » From Books »
From Books
Fitowa 12:1-42 |
1 Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna cikin ƙasar Masar, 2wannan wata zai zama wata na farko a shekara a gare su. 3A faɗa wa dukan taron Isra’ilawa cewa, “A rana ta goma ga watan nan, kowane namiji ya ɗauki ɗan rago ko ɗan akuya daga cikin garke domin iyalinsa, dabba ɗaya domin kowane gida. 4Idan da wanda iyalinsa ba za su iya cinye dabba guda ɗungum ba, saboda iyalin kima ne, to, sai su haɗa kai da maƙwabtansu, su ɗauki dabba guda gwargwadon yawansu. 5Tilas ne dabbar ta kasance lafiyayyiya ƙalau, bana ɗaya. Za ku kamo daga cikin tumakinku ko awaki. 6Za ku turke dabbar har rana ta goma sha huɗu ga wata, wato sa’ad da dukan taron jama’ar Isra’ila za su yanka ragunansu da maraice. 7Sa’an nan ku ɗibi jinin, ku sa a dogaran ƙofa duka biyu, da bisa kan ƙofar gidajen da za a ci naman dabbobin. 8A daren nan za ku gasa naman, ku ci da abinci marar yisti, da ganyaye masu ɗaci. 9Kada ku ci shi ɗanye ko daffaffe da ruwa, amma a gasa shi, da kan, da ƙafafun, da kayan cikin. 10Kada ku bar kome ya kai gobe, abin da ya kai gobe kuwa, sai ku ƙone shi. 11Ga yadda za ku ci shi, da ɗamara a gindinku, da takalma a ƙafafunku, da sanda a hannunku, da gaggawa kuma za ku ci shi. Idin Ƙetarewa ne ga Ubangiji. 12A daren nan zan ratsa ƙasar Masar, in bugi kowane ɗan fari na ƙasar, na mutum da na dabba. Zan hukunta gumakan Masar duka, gama ni ne Ubangiji. 13Jinin da yake bisa gidajenku zai nuna inda kuke. Sa’ad da na ga jinin zan tsallake ku, ba kuma wani bala’in da zai same ku, ya hallaka ku, a lokacin da zan bugi ƙasar Masar. 14 Ranan nan za ta zama ranar tunawa a gare ku, za ku kiyaye ta, ranar idi ga Ubangiji. Dukan zamananku za ku kiyaye ta, idi ga Ubangiji har abada.
15“Za ku yi kwana bakwai kuna cin abinci marar yisti. A rana ta fari za ku fitar da yisti daga cikin gidajenku, gama duk wanda ya ci abin da aka sa wa yisti tun daga rana ta fari har zuwa ta bakwai za a fitar da shi daga cikin Isra’ila. 16A kan rana ta fari za ku yi tsattsarkan taro, haka kuma za ku yi a rana ta bakwai. A cikin waɗannan ranaku ba za a yi kowane aiki ba, sai na abin da kowa zai ci. 17Za ku kiyaye idin abinci marar yisti, gama a wannan rana na fitar da rundunarku daga ƙasar Masar. Ku kiyaye wannan rana dukan zamananku. Wannan farilla ce ta har abada. 18Za ku ci abinci marar yisti da maraice a kan rana ta goma sha huɗu ga wata na fari, har zuwa rana ta ashirin da ɗaya ga watan da maraice. 19Amma kada a iske yisti a gidajenku har kwana bakwai, gama idan wani ya ci abin da aka sa wa yisti za a fitar da shi daga cikin taron jama’ar Isra’ila, ko shi baƙo ne ko kuwa haifaffen ƙasar. 20Dukan abin da yake da yisti ba za ku ci shi ba, wato sai abinci marar yisti ne kaɗai za ku ci a dukan gidajenku.”
21Musa ya kirayi dattawan Isra’ila duka, ya ce musu, “Gaggauta, ku zaɓa wa kanku ɗan tunkiya ko akuya bisa ga iyalanku, ku yanka domin Idin Ƙetarewa. 22Ku ɗauki tuntun ezob, ku tsoma cikin jinin da yake a kasko, ku yarfa wa dogaran ƙofa duka biyu, da bisa kan ƙofar. Kada kowa ya fita daga gidansa sai da safe. 23 Gama Ubangiji zai ratsa don ya kashe Masarawa, sa’ad da ya ga jinin a bisa kan ƙofar, da dogaran ƙofa duka biyu sai ya wuce ƙofar, ba zai bar mai hallakarwa ya shiga gidanku, ya kashe ku ba. 24Za ku kiyaye waɗannan ƙa’idodi, ku riƙe su farilla, ku da ‘ya’yanku har abada. 25Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji zai ba ku kamar yadda ya alkawarta, wajibi ne ku kiyaye wannan farilla. 26Sa’ad da ‘ya’yanku suka tambaye ku, ‘Ina ma’anar wannan farilla?’ 27Za ku ce, ‘Hadaya ce ta Idin Ƙetarewa ga Ubangiji, domin ya tsallake gidajen Isra’ilawa a Masar, lokacin da ya kashe Masarawa, amma bai taɓa gidajenmu ba’ ” Sai jama’ar suka durƙusa suka yi sujada. 28Isra’ilawa suka tafi suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa da Haruna.
Mutuwar ‘Ya’yan Fari
29 Da tsakar dare sai Ubangiji ya karkashe dukan ‘ya’yan fari maza a ƙasar Masar, tun daga ɗan farin Fir’auna, wato magajinsa, har zuwa ɗan farin ɗan sarka da yake a kurkuku, har da dukan ‘ya’yan fari maza na dabbobi. 30Da dare Fir’auna ya tashi, shi da dukan fādawansa, da dukan Masarawa, suka yi kuka mai tsanani a Masar, gama ba gidan da ba a yi mutuwa ba. 31Sai Fir’auna ya sa aka kirawo masa Musa da Haruna da daren, ya ce musu, “Tashi, ku da jama’arku, ku fita daga cikin jama’ata. Tafi, ku bauta wa Ubangiji kamar yadda kuka ce. 32Kwashi garkunanku na tumaki da awaki, da na shanu, ku yi tafiyarku kamar yadda kuka ce, amma ku sa mini albarka.”
33Masarawa suka iza mutanen su gaggauta, su fita ƙasar, gama suka ce, “Ƙarewa za mu yi idan ba ku tafi ba.” 34Sai jama’ar suka ɗauki ƙullun da ba a sa masa yisti ba, da ƙorensu na aikin ƙullun, suka ƙunshe a mayafansu, suka saɓa a kafaɗunsu. 35 Isra’ilawa kuwa suka yi yadda Musa ya faɗa musu, suka roƙi Masarawa kayan adonsu na azurfa da na zinariya, da kuma tufafi. 36Ubangiji ya sa jama’a su yi farin jini a wurin Masarawa, saboda haka Masarawa suka ba su abin da suka roƙa. Ta haka suka washe Masarawa.
Isra’ilawa Sun Fita Masar
37Isra’ilawa mutum wajen zambar ɗari shida maza (600,000), banda iyalansu, suka kama tafiya daga Ramases zuwa Sukkot. 38Babban taron tattarmuka kuma suka tafi tare da su, da garkunan tumaki da awaki, da na shanu tinjim. 39Suka toya abinci marar yisti da ƙullun da suka fita da shi daga Masar, gama ba su sa yisti cikin ƙullun ba domin an iza ƙyeyarsu, ba su sami damar dakatawa ba, ba su kuwa shirya wa kansu guzuri ba.
40 Zaman da Isra’ilawa suka yi a Masar shekara ce arbaminya da talatin. 41A ranar da shekara arbaminya da talatin ɗin nan suka cika, a ran nan ne dukan rundunar Ubangiji suka fita daga ƙasar Masar. 42Daren nan da Ubangiji ya sa domin ya fito da Isra’ilawa daga ƙasar Masar, daren ne wanda wajibi ne Isra’ilwa su kiyaye domin su girmama Ubangiji dukan zamanansu.
|
- « Previous
- 1
- …
- 7
- 8
- 9