Skip to content
Home » From Books » Page 7

From Books

Qur’an- Surat 37: 102-110 (The Saffat).

Taurat: Genesis 22:1-18

102.To, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: “Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?” (Yãron) ya ce: “Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri.”103

To, a lõkacin da suka yi sallama, (Ibrahĩm) ya kãyar da shi ga gẽfen gõshinsa.

,104.Kuma Muka kira shi cẽwa “Ya Ibrahĩm!”

105.“Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin.” Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

106Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna.

107.Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma.

108. Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe.

109. Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm.

110.Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

1  Bayan waɗannan al’amura Allah ya jarraba Ibrahim ya ce masa, “Ibrahim!”
Sai ya ce, “Ga ni.”
2  Ya ce, “Ɗauki ɗanka, tilon ɗanka Ishaku, wanda kake ƙauna, ka tafi ƙasar Moriya, a can za ka miƙa shi hadayar ƙonawa a bisa kan ɗayan duwatsun da zan faɗa maka.”
3Sai Ibrahim ya tashi tun da sassafe, ya ɗaura wa jakinsa shimfiɗa ya kuwa ɗauki biyu daga cikin samarinsa tare da shi, da kuma ɗansa Ishaku, ya faskara itace na yin hadayar ƙonawa. Ya kuwa tashi ya tafi inda Allah ya faɗa masa. 4A rana ta uku Ibrahim ya ta da idanunsa ya hangi wurin daga nesa. 5Ibrahim ya ce wa samarinsa, “Ku tsaya nan wurin jakin, ni da saurayin za mu yi gaba mu yi sujada, sa’an nan mu komo wurinku.”
6Ibrahim ya ɗauki itacen hadayar ƙonawa, ya ɗora wa ɗansa Ishaku, shi kuma ya ɗauki wuta da wuƙa a hannunsa. Dukansu biyu kuwa suka tafi tare. 7Ishaku ya ce wa mahaifinsa Ibrahim, “Baba!”
Sai ya ce, “Ga ni, ɗana.”
Ya ce, “Ga wuta, ga itace, amma ina ragon hadayar ƙonawa?”
8Ibrahim ya ce, “Allah zai tanada wa kansa ragon hadayar ƙonawa, ya ɗana.” Sai su biyu suka tafi tare.
9  Sa’ad da suka zo wurin da Allah ya faɗa masa, sai Ibrahim ya gina bagade a can, ya jera itace a kai. Ya ɗaure Ishaku ɗansa, ya sa shi a bisa itacen bagaden. 10Sai Ibrahim ya miƙa hannu ya ɗauki wuƙar don ya yanka ɗansa. 11Amma mala’ikan Ubangiji ya yi kiransa daga sama, ya ce, “Ibrahim, Ibrahim!”
Sai ya ce, “Ga ni.”
12Ya ce, “Kada ka sa hannunka a kan saurayin, kada kuwa ka yi masa wani abu, gama yanzu na sani kai mai tsoron Allah ne, da yake ba ka ƙi ba da ɗanka, tilonka, a gare ni ba.” 13Ibrahim ya ta da idanunsa, ya duba, ga rago kuwa a bayansa, da ƙahoni a sarƙafe cikin kurmi. Ibrahim kuwa ya tafi ya kamo ragon, ya miƙa shi hadayar ƙonawa maimakon ɗansa. 14Sai Ibrahim ya sa wa wurin suna, “Ubangiji zai tanada,” kamar yadda ake faɗa har yau, “A bisa kan dutsen Ubangiji, za a tanada.”
15Mala’ikan Ubangiji kuma ya sāke kiran Ibrahim, kira na biyu daga sama, 16 ya ce, “Na riga na rantse da zatina, tun da ka yi wannan, ba ka kuwa ƙi ba da tilon ɗanka ba, 17 hakika zan sa maka albarka, zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sama, kamar yashi kuma a gāɓar teku. Zuriyarka za su mallaki ƙofar maƙiyanka, 18 ta wurin zuriyarka kuma al’umman duniya za su sami albarka, saboda ka yi biyayya da umarnina.” 
Alamar Ibrahim – Qur’an Alamar Ibrahim – Taurat (Farawa 12: 1-7)
Surat 3:84

Ka ce: “Mun yi ĩmãni da Allah kuma da abin da aka saukar mana da abin da aka saukar wa Ibrãhĩma da Isma’ĩla da Is’hãƙa da Yãƙũba da jĩkõki, da abin da aka bai wa Mũsã da ĩsã da annabãwa daga Ubangijinsu, bã mu bambantãwa a tsakãnin kõwa daga gare su. Kuma mũ, zuwa gare Shi mãsu sallamãwa ne.”

Surat 4:54 (The Women)

Ko suna hãsadar mutãne ne a kan abin da Allah Ya bã su daga falalarSa? To, lalle ne, Mun bai wa gidan Ibrãhĩm Littãfida hikima kuma Mun bã su mulki mai girma.

1  Ana nan sai Ubangiji ya ce wa Abram, “Ka fita daga ƙasarka, da danginka, da gidan mahaifinka zuwa ƙasar da zan nuna maka. 2Zan kuwa maishe ka al’umma mai girma, zan sa maka albarka, in sa ka ka yi suna, domin ka zama sanadin albarka. 3 Waɗanda suka sa maka albarka zan sa musu albarka, amma zan la’anta waɗanda suka la’anta ka. Dukan al’umman duniya za su roƙe ni in sa musu albarka kamar yadda na sa maka.”
4Abram kuwa ya kama hanya bisa ga faɗar Ubangiji, Lutu kuma ya tafi tare da shi, Abram yana da shekara saba’in da biyar sa’ad da ya yi ƙaura daga Haran. 5Abram kuwa ya ɗauki matarsa Saraya da Lutu, ɗan ɗan’uwansa, da dukan dukiyarsu, da dukan mallakarsu waɗanda suka tattara a Haran.
Sa’ad da suka kai ƙasar Kan’ana, 6Abram ya ratsa ƙasar zuwa Shekem, wurin itacen oak na More. A lokacin nan Kan’aniyawa suke a ƙasar. 7 Sai Ubangiji ya bayyana ga Abram, ya ce, “Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa.” Sai ya gina bagade gagina bagade ga Ubangiji, wanda ya bayyana gare shi
Alamar Ibrahim (Kashi Na 2) – Qur’an Alamar Ibrahim (Kashi Na 2) – Taurat

Suratut 37: 83-84,99-101 (AL-ṢAFFĀT).

83. Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake.

84. A lõkacin da ya je wa dangijinsa da zũciya kuɓutacciya.

99. Kuma (Ibrahĩm] ya ce: “Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni.”

100. “Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne.”

101. Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro mai haƙuri.

Farawa 15:1-6

1Bayan waɗannan al’amura, maganar Ubangiji ta zo ga Abram cikin wahayi cewa, “Abram, kada ka ji tsoro, ni ne garkuwarka, kana da lada mai yawa.”
2Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, me za ka ba ni, ga shi kuwa, ba ni da ɗa? Ko kuwa Eliyezer na Dimashƙu ne zai gāje ni?” 3Abram kuma ya ce, “Ga shi, ba ka ba ni zuriya ba, ga shi ma wani yaron gidana ne zai gāje ni.”
4Sai ga maganar Ubangiji ta zo gare shi cewa, “Mutumin nan, ba shi zai gāje ka ba, ɗan cikinka shi zai gāje ka.” 5 Sai Ubangiji ya fito da shi waje ya ce, “Ina so ka dubi sararin sama, ka kuma ƙidaya taurari, in kana iya ƙidaya su.” Sai kuma ya ce masa, “Haka zuriyarka za ta zama.” 6 Ya amince da Ubangiji, Ubangiji kuwa ya lasafta wannan adalci ne a gare shi.