Skip to content

From Books

Yohanna surori 13-16

1Ana nan tun kafin Idin Ƙetarewa, da Yesu ya san lokacinsa ya yi da zai tashi daga wannan duniya ya koma wurin Uba, da yake ya ƙaunaci mutanensa da suke duniya, ya ƙaunace su har matuƙa. 2Ana cikin cin abincin dare, Iblis kuwa ya riga ya sa a zuciyar Yahuza Iskariyoti ɗan Saminu yă bāshe shi. 3Yesu kuwa, da yake ya san Uba ya sa kome a hannunsa, ya kuma sani daga wurin Allah ya fito, wurin Allah kuma zai koma, 4sai ya tashi daga cin abincin, ya ajiye mayafinsa, ya ɗauko ɗan zane ya yi ɗamara da shi. 5Sa’an nan ya zuba ruwa a daro, ya fara wanke ƙafafun almajiran, yana shafe su da abin da ya yi ɗamara da shi. 6Sai ya zo kan Bitrus, shi kuwa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ashe, kai ne za ka wanke mini ƙafa?” 7Yesu ya amsa ya ce, “Yanzu kam, ba ka san abin da nake yi ba, amma daga baya za ka fahimta.” 8Bitrus ya ce masa, “Wane ni! Ai, ba za ka wanke mini ƙafa ba har abada!” Yesu ya amsa masa ya ce, “In ban wanke maka ba, ba ka da rabo a gare ni.” 9Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ba ma ƙafafuna kaɗai ba, har ma da hannuwana da kaina!” 10Yesu ya ce masa, “Wanda ya yi wanka ba ya bukatar wanke kome, sai ƙafafunsa kawai, domin ya riga ya tsarkaka sarai. Ku ma tsarkakakku ne, amma ba dukanku ne ba.” 11Don ya san wanda zai bāshe shi, shi ya sa ya ce, “Ba dukanku ne tsarkakakku ba.”
12 Bayan ya wanke ƙafafunsu, ya yafa mayafinsa, sai ya sāke kishingiɗa, ya ce musu, “Kun gane abin da na yi muku? 13Kuna kirana Malam, da kuma Ubangiji. Daidai ne kuwa, don haka nake. 14Tun da yake ni Ubangijinku da kuma Malaminku, har na wanke muku ƙafa, ashe, ku ma wajibi ne ku wanke wa juna. 15Na yi muku ishara domin ku ma ku yi yadda na yi muku 16 Lalle hakika, ina gaya muku, bawa ba ya fin ubangijinsa, manzo kuma ba ya fin wanda ya aiko shi. 17In dai kun san wannan, kuna kuma aikatawa, ku masu farin ciki ne. 18 Ba dukanku nake nufi ba. Na san waɗanda na zaɓa. Wannan kuwa duk domin a cika Nassi ne cewa, ‘Wanda yake cin abincina ya tasar mini.’ 19Tun yanzu zan sanar da ku abu tun bai faru ba, domin sa’ad da ya faru ku ba da gaskiya ni ne shi. 20 Lalle hakika, ina gaya muku, wanda ya yi na’am da duk wanda na aiko, ya yi na’am da ni ke nan. Wanda ya yi na’am da ni kuwa, to, ya yi na’am da wanda ya aiko ni.”
Yesu Ya Ce Za a Bāshe Shi
(Mat 26.20-25Mar 14.17-21Luk 22.21-23)
21Bayan da Yesu ya faɗi haka, ya ji nauyi a ransa, ya yi shaida ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, ɗayanku zai bāshe ni.” 22Sai almajiran suka duddubi juna, suka rasa da wanda yake. 23Wani daga cikin almajiransa kuwa, wanda Yesu yake ƙauna, yana kishingiɗe gab da Yesu. 24Sai Bitrus ya alamta masa ya ce, “Gaya mana, da wa yake?” 25Shi kuwa da yake kishingiɗe haka gab da Yesu ya karkata, ya ce masa, “Ya Ubangiji, wane ne?” 26Sai Yesu ya amsa ya ce, “Shi ne wanda zan tsoma ‘yar lomar nan in ba shi.” Da ya tsoma ‘yar lomar kuwa, sai ya ba Yahuza, Ɗan Saminu Iskariyoti. 27Da karɓar ‘yar loman nan Shaiɗan ya shige shi. Yesu ya ce masa, “Yi abin da za ka yi, maza.” 28Amma cikin waɗanda suke cin abinci, ba wanda ya san dalilin da ya sa Yesu ya faɗa masa haka. 29Har waɗansu ma sun yi zaton Yesu ya ce masa ya yi musu sayayyar idi ne, ko kuwa ya ba gajiyayyu wani abu, don Yahuza ne yake riƙe da jakar kuɗinsu. 30Shi kuwa da karɓar ‘yar lomar, sai ya fita, da dare ne kuwa.
Sabon Umarni
31Bayan ya fita kuma sai Yesu ya ce, “Yanzu ne aka ɗaukaka Ɗan Mutum, aka kuma ɗaukaka Allah ta wurinsa. 32Allah kuma zai ɗaukaka shi zuwa ga zatinsa, nan da nan kuwa zai ɗaukaka shi. 33 Ya ku ‘ya’yana ƙanana, saura ɗan lokaci kaɗan ina tare da ku. Za ku neme ni, amma kamar yadda na faɗa wa Yahudawa cewa, ‘Inda za ni ba za ku iya zuwa ba,’ haka nake faɗa muku yanzu. 34 Sabon umarni nake ba ku, shi ne ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, haka ku ma, ku ƙaunaci juna. 35Ta haka, kowa zai gane ku almajiraina ne, in dai kuna ƙaunar juna.”
Bitrus Zai Yi Musun Sanin Yesu
(Mat 26.31-35Mar 14.27-31Luk 22.31-34)
36Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ina za ka?” Yesu ya amsa ya ce, “Inda za ni, ba za ka iya bina yanzu ba, amma daga baya za ka bi ni.” 37Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, don me, ba zan iya binka a yanzu ba? Ai, zan ba da raina saboda kai.” 38Yesu ya amsa ya ce, “Ashe, za ka ba da ranka saboda ni? Lalle hakika, ina gaya maka, kafin zakara ya yi cara, za ka yi musun sanina sau uku.
Yesu Ne Hanya zuwa Wurin Uban
1“Kada ku damu. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni. 2A gun Ubana akwai wurin zama da yawa. Da ba haka ne ba, da na faɗa muku, domin zan tafi in shirya muku wuri. 3In kuwa na je na shirya muku wuri, sai in dawo in kai ku wurina, domin inda nake, ku ma ku zama kuna can. 4Inda za ni kuwa kun san hanya.” 5Sai Toma ya ce masa, “Ya Ubangiji, ba mu san inda za ka ba, ƙaƙa za mu san hanyar?” 6Yesu ya ce masa, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina. 7Da kun san ni, da kun san Ubana ma. Amma daga yanzu kun san shi, kun kuma gan shi.”
8Sai Filibus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ka nuna mana Uban, bukatarmu ta biya ke nan.” 9Yesu ya ce masa, “Na daɗe tare da ku haka, amma har yanzu ba ka san ni ba, Filibus? Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban. Yaya za ka ce, ‘Nuna mana Uban’”? 10Wato ba ka gaskata ba cikin Uba nake, Uba kuma cikina? Maganar da nake faɗa muku, ba domin kaina nake faɗa ba, Uba ne da yake zaune a cikina yake yin ayyukansa. 11Ku gaskata ni, a cikin Uba nake, Uba kuma cikina, ko kuwa ku gaskata ni saboda ayyukan kansu.
12“Lalle hakika, ina gaya muku, duk wanda yake gaskatawa da ni ayyukan da nake yi shi ma haka zai yi. Har ma, zai yi ayyukan da suka fi waɗannan, domin zan tafi wurin Uba. 13Duk abin da kuka roƙa da sunana kuma zan yi, domin a ɗaukaka Uban ta wurin Ɗan. 14Kome kuke roƙa da sunana, zan yi shi.”
Alkawarin Zuwan Ruhu Mai Tsarki
15“In dai kuna ƙaunata, za ku bi umarnina. 16Ni ma zan roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimako ya kasance tare da ku har abada. 17Shi ne Ruhu na gaskiya, wanda duniya ba ta iya samunsa, domin ba ta ganinsa, ba ta kuma san shi ba. Ku kam, kun san shi, domin yana zaune tare da ku, zai kuma kasance a zuciyarku.
18“Ba zan bar ku marayu ba, zan zo wurinku. 19Saura ɗan lokaci kaɗan duniya ba za ta ƙara ganina ba, amma ku za ku gan ni. Saboda ni a raye nake, ku ma za ku rayu. 20A ran nan ne fa za ku sani, ni cikin Uba nake, ku kuma a cikina, ni kuma a cikinku. 21Duk wanda ya san umarnaina, yake kuma binsu, shi ne mai ƙaunata. Mai ƙaunata kuwa, Ubana zai ƙaunace shi, ni kuma zan ƙaunace shi, in bayyana kaina gare shi.” 22Sai Yahuza (ba Iskariyoti ba) ya ce masa, “Ya Ubangiji, me ya sa za ka bayyana kanka gare mu, ba ga duniya ba?” 23Yesu ya amsa masa ya ce, “Kowa yake ƙaunata, zai kiyaye maganata, Ubana kuwa zai ƙaunace shi, za mu zo wurinsa mu zauna tare da shi. 24Wanda ba ya ƙaunata, ba ya kiyaye maganata. Maganar da kuke ji kuwa ba tawa ba ce, ta Uba ce wanda ya aiko ni.
25“Duk wannan na faɗa muku ne tun muna tare. 26Amma Mai Taimako, Ruhu Mai Tsarki, wanda Uba zai aiko da sunana, shi ne zai koya muku kome, ya kuma tuna muku duk abin da na faɗa muku. 27Na bar ku da salama. Salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada ku damu, kada kuma ku ji tsoro. 28Kun dai ji na ce muku zan tafi, in kuma dawo wurinku. Da kuna ƙaunata da kun yi murna saboda za ni wurin Uba, domin kuwa Uban ya fi ni. 29To, yanzu na faɗa muku tun bai faru ba, domin sa’ad da ya faru, ku ba da gaskiya. 30Ba zan ƙara yi muku magana mai yawa ba, domin mai mulkin duniyan nan yana zuwa, ba shi kuwa da wani hannu a kaina, 31sai dai domin duniya tă sani ina ƙaunar Uban, ina kuma yin yadda Uba ya umarce ni, ku tashi mu tafi daga nan.
Yesu Ne Itacen Inabi na Hakika
1“Ni ne itacen inabi na hakika, Ubana kuwa shi ne manomi. 2Kowane reshe a cikina da ba ya ‘ya’ya, sai ya datse shi. Kowane reshe mai yin ‘ya’ya kuwa yakan tsarkake shi don ya ƙara haihuwa. 3Koyanzu ma ku tsarkakku ne saboda maganar da na faɗa muku. 4Ku zauna a cikina, ni kuma a cikinku. Kamar yadda reshen inabi, ba ya iya ‘ya’ya shi kaɗai, sai ko ya zauna itacen inabin, haka ku ma ba za ku iya ba, sai kun zauna a cikina. 5Ni ne itacen inabin, ku kuwa rassan. Wanda ya zauna a cikina, ni kuma a cikinsa, shi ne mai yin ‘ya’ya da yawa. Domin in ba game da ni ba, ba za ku iya kome ba. 6Duk wanda bai zauna a cikina ba, za a yar da shi can, kamar reshe, yă bushe, a kuma tattara irinsu a jefa wuta, a ƙone. 7In kun zauna a cikina, maganata kuma ta zauna a cikinku, za ku roƙi duk abin da kuke so, za a kuwa yi muku. 8Yadda ake ɗaukaka Ubana ke nan, in kuna ‘ya’ya da yawa, ta haka kuma kuke tabbata almajiraina. 9Kamar yadda Uba ya ƙaunace ni, haka ni ma na ƙaunace ku. To, ku zauna cikin ƙaunar da nake muku. 10In kun bi umarnina, za ku zauna cikin ƙaunar da nake muku, kamar yadda ni na bi umarnin Ubana, na kuma zauna cikin ƙaunar da yake mini. 11Na gaya muku haka domin farin cikina ya kasance a cikinku, farin cikinku kuma ya zama cikakke.
12  “Wannan fa shi ne umarnina, cewa ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku. 13Ba ƙaunar da ta fi haka ga mutane, wato mutum yă ba da ransa saboda aminansa. 14Ku aminaina ne in kuna yin abin da na umarce ku. 15Nan gaba ba sauran in ce da ku bayi, don bawa bai san abin da ubangijinsa yake yi ba. Sai dai in ce da ku aminai, domin na sanar da ku duk abin da na jiyo wurin Ubana. 16Ba ku kuka zaɓe ni ba, ni ne na zaɓe ku, na sa ku ku je ku yi ‘ya’ya, ‘ya’yanku kuma su tabbata, domin kome kuka roƙi Uba da sunana yă ba ku. 17Na umarce ku haka domin ku ƙaunaci juna.”
Ƙiyayyar Duniya
18In duniya ta ƙi ku, ku sani sai da ta ƙi ni kafin ta ƙi ku. 19Da ku na duniya ne da duniya ta so abinta, amma saboda ku ba na duniya ba ne, na kuma zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku. 20 Ku tuna da maganar da na yi muku cewa, “Bawa ba ya fin ubangijinsa.” In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun kiyaye maganata, da sai su kiyaye taku ma. 21Duk wannan za su yi muku saboda sunana, don ba su san wanda ya aiko ni ba. 22Da ba domin na zo na yi musu magana ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu kam, ba su da wani hanzari a kan zunubinsu. 23Wanda ya ƙi ni ya ƙi Ubana ma. 24Da ba domin na yi ayyuka a cikinsu da ba wanda ya taɓa yi sai ni ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun gani, sun kuma ƙi mu, ni da Ubana duka. 25 An yi wannan kuwa domin a cika maganar da yake a rubuce a cikin Shari’arsu cewa, “Sun ƙi ni ba dalili.” 26Amma sa’ad da Mai Taimako ya zo, wanda zan aiko muku daga wurin Uba, wato Ruhu na gaskiya, mai fitowa daga wurin Uba, shi ne zai shaida ni. 27Ku ma shaidu ne, domin tun farko kuke tare da ni.
1“Na faɗa muku duk wannan ne domin in kawar muku da sanadin tuntuɓe. 2Za su fisshe ku daga jama’a. Hakika, lokaci ma na zuwa da kowa ya kashe ku, zai zaci bautar Allah yake yi. 3Za su yi haka ne kuwa domin ba su san Uba ko ni ba. 4Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin in lokacinsu ya yi ku tuna na faɗa muku.”
Aikin Ruhu Mai Tsarki
“Ban faɗa muku abubuwan nan tun da farko ba, domin ina tare da ku. 5Yanzu kuwa za ni wurin wanda ya aiko ni, duk da haka a cikinku, ba wanda ya tambaye ni, ‘Ina za ka?’ 6Amma saboda na faɗa muku waɗannan abubuwa, ga shi baƙin ciki ya cika zuciyarku. 7Duk da haka ina gaya muku gaskiya, zai fiye muku in tafi, domin in ban tafi ba, Mai Taimakon nan ba zai zo gare ku ba. In kuwa na tafi, zan aiko shi gare ku. 8Sa’ad da kuwa ya zo zai faɗakar da duniya a kan zunubi, da adalci, da kuma hukunci. 9Wato a kan zunubi, domin ba su gaskata da ni ba, 10a kan adalci, don za ni wurin Uba, ba kuwa za ku ƙara ganina ba. 11a kan hukunci kuma, domin an yanke wa mai mulkin duniyar nan hukunci.
12“Ina da sauran abubuwa da yawa da zan gaya muku tukuna, amma ba za ku iya ɗaukarsu a yanzu ba. 13Sa’ad da kuwa Ruhu na gaskiya ya zo, zai bishe ku cikin dukan gaskiya, domin ba zai yi magana don kansa ba, sai dai duk abin da ya ji, shi zai faɗa, zai kuma sanar da ku al’amuran da za su auku. 14Zai ɗaukaka ni, domin zai ɗauko daga cikin abin da yake nawa ya sanar da ku. 15Duk abin da Uba yake da shi, nawa ne. Shi ya sa na ce zai ɗauko daga cikin abin da yake nawa ya sanar da ku.”
Baƙin Ciki Zai Koma Farin Ciki
16“Bayan ɗan lokaci kaɗan, ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma, za ku gan ni.” 17Sai waɗansu almajiransa suka ce wa juna, “Me yake nufi da ce mana, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma za ku gan ni’? da kuma cewa, ‘Domin za ni wurin Uba’?” 18Suka ce, “Me yake nufi da, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan’ ɗin? Ai, ba mu san abin da yake faɗa ba.” 19Yesu kuwa ya sani suna so su tambaye shi, sai ya ce musu, “Wato kuna tambayar juna ne abin da nake nufi da cewa, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma za ku gan ni’? 20Lalle hakika, ina gaya muku, za ku yi kuka da kuma gunji, amma duniya za ta yi farin ciki. Za ku yi baƙin ciki, amma baƙin cikinku zai koma farin ciki. 21Idan mace tana naƙuda takan sha wuya, don lokacin haihuwarta ya yi. Amma da zarar ta haifi jinjirin, ba ta ƙara tunawa da wahalar da ta sha, domin murnar an sami baƙon duniya. 22Haka ku ma yanzu kuke tare da baƙin ciki, amma zan sāke ganinku, sa’an nan zuciyarku za ta yi fari, ba kuwa mai ɗauke muku farin cikinku. 23A ran nan, ba za ku yi mini wata tambaya ba. Lalle hakika, ina gaya muku, kome kuka roƙi Uba zai ba ku saboda sunana. 24Har yanzu dai ba ku roƙi kome da sunana ba. Ku roƙa, za ku samu, domin farin cikinku ya zama cikakke.”
Na Yi Nasara da Duniya
25“Duk wannan na faɗa muku da misalai ne. Lokaci yana zuwa da ba zan ƙara faɗa muku kome da misalai ba, sai dai in ba ku labarin Uba a sarari. 26A ran nan za ku yi roƙo da sunana. Ban kuwa ce muku zan roƙar muku Uba ba, 27domin shi Uban kansa na ƙaunarku, domin kun ƙaunace ni, kun kuma gaskata daga wurin Uban na fito. 28Daga wurin Uban ne na fito, na shigo duniya, har wa yau kuma zan bar duniya in koma wurin Uba.”
29Sai almajiransa suka ce, “Yauwa! Yanzu ne fa kake magana a sarari, ba da misali ba! 30Yanzu ne muka tabbata ka san kome, ba sai wani ya tambaye ka ba. Ta haka muka gaskata daga wurin Allah ka fito.” 31Yesu ya amsa musu ya ce, “Ashe, yanzu kun gaskata? 32To, lokaci na zuwa, har ma ya yi, da za a warwatsa ku, kowa yă koma gidansu, ku bar ni ni kaɗai. Duk da haka kuwa ba ni kaɗai nake ba, domin Uba na tare da ni. 33Na faɗa muku wannan ne domin a gare ni ku sami salama. A duniya kuna shan wuya, amma dai ku yi farin ciki, ai, na yi nasara da duniya.”

Kubawar Shari’a 28:1 – 31:29

1  “Idan kun yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, kuna aikata dukan umarnansa waɗanda nake umartarku da su yau, to, Ubangiji Allahnku zai fifita ku fiye da dukan sauran al’umma. 2Idan kun yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, dukan albarkun nan za su sauko muku, su zama naku.
3“Za ku zama masu albarka, ko kuna cikin gari, ko kuna cikin karkara.
4“’Ya’yanku za su zama masu albarka, haka nan kuma amfanin gonakinku, da ‘ya’yan dabbobinku, da ‘ya’yan shanunku, da ‘ya’yan tumakinku da awakinku.
5“Kwandunanku da makwaɓan za su yalwata ƙullunku.
6“Da albarka za ku shiga, da albarka kuma za ku fita.
7“Ubangiji zai sa ku fatattaki abokan gābanku a gabanku waɗanda suke tasar muku. Ta hanya guda za su auka muku, amma ta hanyoyi bakwai za su gudu daga gabanku.
8“Ubangiji zai sa wa abin da yake cikin rumbunanku albarka da dukan aikin hannuwanku. Zai sa muku albarka a ƙasar da yake ba ku.
9“Ubangiji zai sa ku zama tsattsarkar jama’arsa kamar yadda ya rantse muku, idan za ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin tafarkunsa. 10Dukan mutanen duniya za su gane ku na Ubangiji ne, za su ji tsoronku. 11Ubangiji zai arzuta ku ƙwarai da ‘ya’ya, da ‘ya’yan dabbobi, da amfanin gona, a ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninku zai ba ku. 12Ubangiji zai buɗe muku taskarsa ta sammai, don ya ba ƙasarku ruwa a kan kari, zai kuma sa albarka a kan dukan aikin hannuwanku. Al’ummai da yawa za su karɓi rance a wurinku, amma ku, ba za ku karɓi rance ba. 13Ubangiji zai sa ku zama kai, ba wutsiya ba. Kullum ci gaba za ku yi, ba baya ba, idan kuka yi biyayya da umarnan Ubangiji Allahnku waɗanda nake umartarku da su yau, in kun lura, kun yi aiki da su, 14idan kuma ba ku kauce zuwa dama ko hagu daga maganar da na umarce ku da ita yau ba, wato don ku bi waɗansu gumaka, ku bauta musu.”
Sakamakon Rashin Biyayya
(L.Fir 26.14-46)
15“Amma idan ba za ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku ba, ko kuwa ba ku lura kuka aikata umarnansa da dokokinsa waɗanda nake umartar da su yau ba, to, dukan waɗannan la’ana za su auko muku, su same ku.
16“La’anannu za ku zama a gari da karkara.
17“La’anannu ne kwandunanku da makwaɓan ƙullunku.
18“La’anannu ne ‘ya’yanku, da amfanin gonakinku, da ‘ya’yan shanunku, da ‘ya’yan tumakinku da na awakinku.
19“Da la’ana za ku shiga, da la’ana kuma za ku fita.
20“Ubangiji zai aiko muku da la’ana, da ruɗewa, da damuwa cikin dukan abin da za ku yi, har ya hallaka ku, ku lalace da sauri saboda mugayen ayyukanku, domin kuma kuka rabu da ni. 21Ubangiji zai aiko muku da annoba wadda za ta manne muku, ta cinye ku cikin ƙasar da za ku shiga, ku mallake ta. 22Ubangiji zai buge ku da ciwon fuka, da zazzaɓi, da ciwon kumburi, da zafi mai tsanani, da fari, da burtuntuna, da fumfuna. Waɗannan za su yi ta damunku har ku lalace. 23Samaniya da take bisa kanku za ta zama tagulla, ƙasar kuma da kuke a bisa kanta ta zama baƙin ƙarfe. 24Ubangiji zai mai da ruwan sama na ƙasarku gāri da ƙura, zai zubo muku da shi daga sama har ku hallaka.
25“Ubangiji zai sa abokan gabanku su rinjaye ku cikin yaƙi. Ta hanya guda za ku auka musu, amma ta hanyoyi bakwai za ku gudu daga gabansu. Za ku zama abin ƙi ga dukan mulkokin duniya. 26Gawawwakinku za su zama abinci ga dukan tsuntsayen sama, da namomin duniya. Ba wanda zai kore su. 27Ubangiji zai buge ku da marurai irin na Masar, da basur, da ƙazwa, da ƙaiƙayi waɗanda ba za su warke ba. 28Ubangiji kuma zai buge ku da ciwon hauka, da makanta, da rikicewar hankali. 29Da tsakar rana za ku riƙa lalubawa kamar makaho, ba za ku yi arziki cikin ayyukanku ba. Za a riƙa zaluntarku, ana yi muku ƙwace kullum, ba wanda zai cece ku.
30“Za ku yi tashin yarinya, wani ne zai kwana da ita. Za ku gina gida, wani ne zai zauna a ciki. Za ku dasa inabinku, wani ne zai girbe amfanin. 31Za a yanka sanku a idonku, amma ba za ku ci ba. Za a ƙwace jakinku ƙiri ƙiri a idonku, ba za a mayar muku da shi ba. Za a ba magabtanku tumakinku, ba wanda zai cece ku. 32A idonku za a ba da ‘ya’yanku mata da maza ga wata al’umma dabam, za ku yi ta jin kewarsu, amma a banza, gama ba ku da ikon yin kome. 33Mutanen da ba ku sani ba, su za su ci amfanin gonakinku da dukan amfanin wahalarku. Za a zalunce ku, a murƙushe ku kullum. 34Abubuwan da idanunku za su gani za su sa ku zama mahaukata. 35Ubangiji zai bugi gwiwoyinku da ƙafafunku da marurai tun daga tafin ƙafarku har zuwa ƙoƙwan kanku.
36“Ubangiji zai bashe ku, ku da sarkin da kuka naɗa wa kanku ga wata al’ummar da ku da kakanninku ba ku sani ba. Can za ku bauta wa gumakan itace da na duwatsu. 37Za ku zama abin ƙi, da abin karin magana, da abin habaici a cikin dukan mutane inda Ubangiji zai kora ku.
38“Za ku shuka iri da yawa a gonakinku, amma kaɗan za ku girbe gama fara za su cinye. 39Za ku dasa gonakin inabi, ku nome su, amma ba za ku sha ruwan inabin, ko ku tsinke ‘ya’yan inabin ba, gama tsutsa za ta cinye shi. 40Za ku sami itatuwan zaitun ko’ina cikin ƙasarku, amma ba za ku sami man da za ku shafa ba, gama ‘ya’yan za su kakkaɓe. 41Za ku haifi ‘ya’ya mata da maza, amma ba za su zama naku ba, gama za a kai su bauta. 42Ƙwari za su cinye dukan itatuwanku da dukan amfanin ƙasarku.
43“Baƙin da suke tare da ku za su yi ta ƙaruwa, ku kuwa za ku yi ta komawa baya baya. 44Za ku karɓi rance a wurinsu, su ba za su karɓi rance a wurinku ba. Su za su zama kai, ku kuwa za ku zama wutsiya.
45“Dukan waɗannan la’anoni za su auko muku, su bi ku, su same ku, har ku hallaka, domin ba ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku ba, ba ku kiyaye umarnai da dokoki da ya umarce ku da su ba. 46Za su zama alama da abin mamaki a kanku da zuriyarku har abada. 47Ba ku bauta wa Ubangiji Allahnku da murna da farin ciki ba, saboda dukan abin da ya ba ku a yalwace, 48domin haka za ku bauta wa magabtanku waɗanda Ubangiji zai turo muku. Za ku bauta musu da yunwa, da ƙishirwa, da tsiraici, da talauci. Za su sa karkiyar ƙarfe a wuyanka har su hallaka ku. 49Ubangiji zai kawo wata al’umma daga nesa, wato daga bangon duniya, mai kai sura kamar gaggafa, wadda za ta yi gāba da ku. Al’ummar da ba ku san harshenta ba, 50al’umma mai zafin hali, wadda ba ta kula da tsofaffi, ba ta kuma jin tausayin yara. 51Za ta ci shanunku da amfanin ƙasarku har ku hallaka. Ba za ta bar muku hatsi ko ruwan inabi, ko mai, ko ‘ya’yan shanunku, ko na tumaki da na awakinku ba, har ta lalatar da ku. 52Za su kewaye garuruwanku da yaƙi, har dogayen garukanku, da kagaranku waɗanda kuke dogara gare su, su rurrushe. Za su kewaye garuruwan ƙasarku da yaƙi a ƙasar da Ubangiji Allahnku ya ba ku. 53Za ku ci naman ‘ya’yanku, mata da maza, waɗanda Ubangiji Allahnku ya ba ku, saboda irin tsananin kewayewar da magabtanku suka yi muku da yaƙi. 54Nagarin mutum mai taushin zuciya wanda yake tare da ku, zai ƙi ɗan’uwansa, da matarsa, da ‘ya’yansa da suka ragu, 55domin kada ya ba wani daga cikinsu naman ‘ya’yansa wanda yake ci, gama ba abin da ya rage masa saboda irin tsananin kewayewar garuruwanku da yaƙi wanda abokan gabanku suka kawo muku. 56 Matar kirki mai taushin zuciya wadda take tare da ku wadda ba za ta sa tafin ƙafarta a ƙasa ba saboda taushin zuciyarta da kyakkyawan halinta, za ta ƙi ƙaunataccen mijinta, da ɗanta, da ‘yarta. 57A ɓoye za ta ci mahaifar da take biyo bayan ta haihu, da ‘ya’yan da za ta haifa, saboda ba ta da wani abinci lokacin da magabtanku za su kewaye garuruwanku da yaƙi mai tsanani.
58“Idan ba ku lura, ku aikata dukan maganar dokokin nan da aka rubuta a wannan littafi ba, domin ku ji tsoron sunan nan mai ɗaukaka, mai kwarjini, wato sunan Ubangiji Allahnku, 59to, Ubangiji zai aukar muku, ku da zuriyarku, da munanan masifu waɗanda ba su kawuwa, da mugayen cuce-cuce marasa warkewa. 60Sai ya sāke kawo muku cuce-cuce irin na Masar, waɗanda kuka ji tsoronsu, za su kuwa manne muku. 61Har yanzu kuma Ubangiji zai kawo muku kowace irin cuta, da kowace irin annoba, waɗanda ba a ambace su a littafin dokokin nan ba, har ku hallaka. 62Ko da yake kuna da yawa kamar taurarin sama, za ku zama ‘yan kaɗan, domin ba ku yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku ba. 63Kamar yadda Ubangiji ya ji daɗi ya arzuta ku, ya riɓaɓɓanya ku, haka nan kuma zai ji daɗi ya lalatar da ku, ya hallaka ku. Za a fitar da ku daga ƙasar da za ku shiga, ku mallaka.
64“Ubangiji zai warwatsa ku cikin dukan al’ummai daga wannan bangon duniya zuwa wancan. Can za ku bauta wa gumakan itace da na dutse waɗanda ku da kakanninku ba ku san su ba. 65Ba za ku sami zaman lafiya wurin waɗannan al’ummai ba, ko tafin ƙafarku ma ba zai sami wurin hutawa ba. Ubangiji kuma zai sa fargaba a zuciyarku, ya sa idanunku su lalace, ranku zai yi suwu. 66Kullum ranku zai kasance da damuwa, za ku zauna da tsoro dare da rana, kuna tsoron abin da zai sami ranku. 67Da safe za ku ce, ‘Da ma maraice ne.’ Da maraice kuma za ku ce, ‘Da ma safiya ce,’ saboda tsoron da yake a zuciyarku, da abubuwan da idanunku suke gani. 68Ubangiji zai komar da ku Masar cikin jiragen ruwa, ko da yake na ce ba za ku ƙara tafiya can ba. Can za ku sayar da kanku bayi mata da maza, amma ba wanda zai saye ku.
1Waɗannan ne zantuttukan alkawari da Ubangiji ya umarci Musa ya faɗa wa Isra’ilawa a ƙasar Mowab, wato banda alkawarin da ya yi da su a bisa Dutsen Horeb.
2Sai Musa ya kira dukan Isra’ilawa ya ce musu, “Ai, kun ga dukan abin da Ubangiji ya yi wa Fir’auna da barorinsa a dukan ƙasar Masar. 3Idanunku sun ga manyan wahalai, da alamu, da mu’ujizai masu girma. 4Duk da haka har wa yau Ubangiji bai ba ku zuciyar ganewa, ko idanun gani, ko kunnuwan ji ba. 5Shekara arba’in na bi da ku cikin jeji. Rigunanku da takalmanku ba su tsufa ba. 6Ba ku ci hatsi ba, ba ku kuma sha ruwan inabi ba, ko barasa, don ku sani shi ne Ubangiji Allahnku. 7 Sa’ad da kuka isa wannan wuri, sai Sihon Sarkin Heshbon, da Og, Sarkin Bashan, suka fito su yi yaƙi da mu, amma muka ci su. 8 Muku ƙwace ƙasarsu, muka ba Ra’ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa, su gāda. 9Saboda haka sai ku kiyaye, ku aikata dukan zantuttukan wannan alkawari don ku arzuta a cikin dukan abin da za ku yi.
10“Yau, ga ku nan tsaye, dukanku a gaban Ubangiji Allahnku, shugabannin kabilanku, da dattawanku, da shugabannin sojojinku, da dukan mazajen Isra’ila, 11da ‘ya’yanku, da matanku, da baƙin da suke a zangonku, da mai yi muku faskare ko mai ɗebo muku ruwa. 12Don ku ƙulla alkawari da Ubangiji Allahnku, alkawarin da Ubangiji Allahnku yake yi da ku yau. 13Don ya mai da ku jama’arsa yau, shi kuma ya zama Allahnku kamar yadda ya yi muku magana, da yadda kuma ya rantse wa kakanninku, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu. 14Ba da ku kaɗai nake yin wannan alkawari ba, 15amma da wanda ba ya nan tare da mu yau, da shi wanda yake tare da mu a nan yau, a gaban Ubangiji Allahnmu.
16“Kun sani dai yadda muka zauna a ƙasar Masar, da yadda muka yi ta ratsawa ta tsakiyar al’ummai muka wuce. 17Kun ga abubuwan da suke da su masu banƙyama, wato gumakansu na itace, da na dutse, da na azurfa, da na zinariya. 18 Kada zuciyar wani mutum, ko ta wata mata ko na wani iyali, ko wata kabila cikinku yau, ta bar bin Ubangiji Allahnku, ta koma ga bauta wa gumakan al’umman nan. Kada a iske wani tushe a cikinku mai ba da ‘ya’ya masu dafi, masu ɗaci. 19Idan wani mutum ya ji zantuttukan la’anan nan sa’an nan ya sa wa kansa albarka a zuciyarsa, yana cewa, ‘Ba abin da zai same ni ko na bi taurin zuciyata,’ wannan zai haddasa lalacewar ɗanye da busasshe gaba ɗaya. 20Ubangiji ba zai gafarce shi ba, amma fushin Ubangiji da kishinsa za su auko a kan wannan mutum, dukan la’anar kuma da aka rubuta a littafin nan za ta bi ta kansa, Ubangiji kuma zai shafe sunansa daga duniya. 21Ubangiji zai ware mutumin nan daga dukan kabilan Isra’ila, don ya hukunta shi bisa ga dukan la’anar da aka rubuta a wannan littafin dokoki.
22“Tsararraki masu zuwa nan gaba, wato ‘ya’yan da za su gaje ku, da baƙon da ya zo daga ƙasa mai nisa, za su ga annobar ƙasar, da cuce-cucen da Ubangiji zai ɗora mata. 23 Dukan ƙasa za ta zama kibritu da gishiri, ba shuka, ba amfani, ciyawa kuma ba ta tsirowa, kamar yadda Ubangiji ya kabantar da Saduma da Gwamrata, da Adam da Zeboyim, da zafin fushinsa. 24Dukan al’ummai za su ce, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi haka da wannan ƙasa? Me ya sa ya yi fushi mai tsanani haka?’ 25Sa’an nan jama’a za su ce, ‘Saboda sun yi watsi da alkawarin Ubangiji Allah na kakanninsu, wato alkawarin da ya yi da su sa’ad da ya fisshe su daga ƙasar Masar. 26Suka tafi suka bauta wa gumaka, suka yi musu sujada, gumakan da ba su san su ba, ba Ubangiji ne ya ba su ba. 27Saboda haka Ubangiji ya husata da wannan ƙasa, ya kawo mata kowace irin la’anar da aka rubuta a wannan littafin. 28Ubangiji ya tumɓuke su da zafin fushinsa, da babbar hasala, daga ƙasarsu, ya watsa su cikin wata ƙasa dabam kamar yadda suke a yau.’
29“Sanin gaibu na Ubangiji Allahnmu ne, amma abubuwan da aka bayyana namu ne, mu da ‘ya’yanmu har abada, don mu kiyaye dukan maganar dokokin nan.
1“Sa’ad da duk waɗannan abubuwa suka same ku, wato albarka da la’ana waɗanda na sa a gabanku, in kun tuna da su a zuciyarku a duk inda kuke cikin al’ummai inda Ubangiji Allahnku ya kora ku, 2kuka sāke komowa wurin Ubangiji Allahnku, ku da ‘ya’yanku kuka yi biyayya da maganarsa da zuciya ɗaya, da dukan ranku, bisa ga yadda na umarce ku yau, 3sa’an nan Ubangiji Allahnku zai komo da ku daga bauta, ya yi muku jinƙai. Zai tattaro ku daga cikin al’ummai inda ya warwatsa ku. 4Idan korarrunku suna can ƙurewar duniya, Ubangiji Allahnku zai tattaro ku daga can, ya dawo da ku. 5Ubangiji Allahnku kuma zai komo da ku cikin ƙasar da kakanninku suka mallaka, za ku mallake ta. Ubangiji zai arzuta ku, ya riɓaɓɓanya ku fiye da kakanninku. 6Ubangiji Allahnku kuma zai tausasa zuciyarku da ta ‘ya’yanku domin ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da zuciya ɗaya da dukan ranku, domin ku rayu. 7Ubangiji Allahnku kuwa zai ɗora wa magabtanku da maƙiyanku waɗanda suka tsananta muku waɗannan la’ana. 8Sa’an nan za ku yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, ku kiyaye dukan umarnan nan waɗanda na umarce ku da su yau. 9Ubangiji Allahnku zai arzuta dukan aikin hannuwanku ƙwarai, ya kuma arzutar da ‘ya’yanku da ‘ya’yan shanu, da amfanin gona, gama Ubangiji zai ji daɗi ya arzuta ku kuma yadda ya ji daɗin kakanninku, 10idan za ku yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, ku kiyaye umarnansa da dokokinsa waɗanda suke rubuce a littafin dokokin nan, idan kuma kun juyo wurin Ubangiji Allahnku da zuciya ɗaya da dukan ranku.
11“Gama wannan umarni da na yi muku yau, bai fi ƙarfinku ba, bai kuma yi nisa da ku ba. 12 Ba cikin Sama yake ba, balle ku ce, ‘Wa zai hau zuwa sama, ya sauko mana da shi don mu ji, mu kiyaye?’ 13Ba kuma a hayin teku yake ba, balle ku ce, ‘Wa zai haye mana wannan teku don ya kawo mana shi don mu ji, mu kiyaye?’ 14Amma umarnin yana kurkusa da ku, yana cikin bakinku da zuciyarku don ku kiyaye shi.
15“Ga shi yau, na sa rai da nagarta a gabanku, da mutuwa da mugunta. 16Idan kuka kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku waɗanda nake umartarku da su yau, idan kuma kun ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kuna yin tafiya cikin tafarkunsa, kuna kiyaye umarnansa, da dokokinsa, da farillansa, to, za ku rayu, ku riɓaɓɓanya, Ubangiji Allahnku kuwa zai sa muku albarka cikin ƙasar da za ku shiga, ku mallake ta. 17Amma idan zuciyarku ta kangare kun ƙi ku saurara, amma zuciyarku ta janye ku kun yi wa gumaka sujada, kuka bauta musu, 18to, ina faɗa muku yau, lalle za ku hallaka. Ba za ku yi tsawon rai a ƙasar da za ku haye Urdun ku shiga ciki don ku mallake ta ba. 19Ina kiran sama da duniya su zama shaidu a kanku yau, cewa na sa rai da mutuwa a gabanku, da albarka da la’ana. Ku zaɓi rai fa, don ku rayu, ku da zuriyarku. 20 Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi biyayya da maganarsa, ku manne masa, gama wannan shi ne ranku da tsawon kwanakinku, don ku zauna a ƙasar da Ubangiji Allahnku ya rantse zai ba kakanninku, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.”
1Sai Musa ya ci gaba da yi wa dukan Isra’ilawa magana. 2 Ya ce, “Yau shekarata ɗari da ashirin ne, ba na iya kaiwa da komowa. Ubangiji kuwa ya ce mini, ‘Ba za ka haye wannan Urdun ba.’ 3Ubangiji Allahnku shi ne zai yi gaba ya haye, ya hallaka al’umman da take gabanku don ku ci su. Joshuwa ne zai shugabance ku, ya haye kamar yadda Ubangiji ya faɗa. 4Ubangiji zai yi musu kamar yadda ya yi wa Sihon da Og, sarakunan Amoriyawa, da ƙasarsu, sa’ad da ya hallaka su. 5Ubangiji zai bashe su a gare ku. Za ku yi musu kamar yadda dā na umarce ku. 6Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tare da ku. Ba zai kunyatar da ku ba, ba kuwa zai yashe ku ba.”
7Sai Musa ya kira Joshuwa, ya yi masa magana a gaban dukan jama’ar Isra’ila, ya ce, “Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali, gama kai ne za ka kai wannan jama’a cikin ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba kakanninsu. Kai ne za ka ba su ita gādo. 8 Ubangiji kansa zai bi da kai, ba zai kunyatar da kai ba, ba kuwa zai yashe ka ba. Kada ka ji tsoro, kada kuma ka karai.”
A Karanta Dokokin Kowace Shekara ta Bakwai
9Sai Musa ya rubuta waɗannan dokoki, ya ba firistoci, ‘ya’yan Lawiyawa, waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawari na Ubangiji, da dukan dattawan Isra’ila. 10 Sai Musa ya umarce su, ya ce, “A ƙarshen kowace shekara bakwai, a lokacin da aka ƙayyade na shekarar yafewa, a lokacin Idin Bukkoki, 11sa’ad da dukan Isra’ilawa za su hallara a gaban Ubangiji Allahnku a inda zai zaɓa, to, sai ku karanta musu waɗannan dokoki su ji da kunnuwansu. 12Ku tara dukan jama’a wuri ɗaya, mata da maza, da yara, da baƙin da suke zaune tare da ku a garuruwanku domin su ji, su koyi tsoron Ubangiji Allahnku, su kuma lura su aikata dukan dokokin nan, 13domin ‘ya’yansu, waɗanda ba su sani ba, su ji, su koyi tsoron Ubangiji Allahnku dukan kwanakinku cikin ƙasar da za ku haye Urdun, ku mallaka.”
Umarnin Ƙarshe da Ubangiji Ya Yi wa Musa
14Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Lokacin rasuwarka ya yi, sai ka kira Joshuwa, ku shigo alfarwa ta sujada, don in ba shi ragamar mulki.” Sai Musa da Joshuwa suka tafi, suka shiga alfarwa ta sujada. 15Ubangiji kuwa ya bayyana a cikin alfarwar a al’amudin girgije. Al’amudin girgijen kuwa ya tsaya a ƙofar alfarwar.
16Ubangiji ya ce wa Musa, “Ga shi, za ka rasu ka tarar da kakanninka. Wannan jama’a kuwa za ta fara kaucewa daga hanya, su bi gumakan ƙasar da za su shiga, su zauna. Za su rabu da ni, su ta da alkawarina wanda na yi da su. 17A wannan rana zan husata da su ƙwarai, in rabu da su, in ɓoye musu fuskata, za a cinye su. Masifu da wahalai za su same su. Za su kuwa ce a ranar, ‘Masifun nan sun same mu domin Allahnmu ba ya tare da mu.’ 18Hakika kuwa, zan ɓoye musu fuskata sabili da muguntar da suka aikata, suka kuma bi gumaka.
19“Don haka, sai ka rubuta wannan waƙa, ka koya wa Isra’ilawa. Ka sa ta a bakinsu don waƙan nan ta zama shaida a gare ni game da Isra’ilawa. 20Sa’ad da na kawo su a ƙasar da take da yalwar abinci, wadda na rantse zan ba kakanninsu, har suka ci, suka ƙoshi, suka yi ƙiba, za su juya, su bi gumaka, su bauta musu. Za su raina ni, su tā da alkawarina. 21Sa’ad da yawan masifun nan da wahalan nan suka same su, to, waƙar nan za ta ba da shaida a kansu, gama zuriyarsu ba za ta manta da wannan waƙa ba, gama na san ƙudurin da suke yi kafin in kawo su ƙasar da na rantse zan bayar.”
22Saboda wannan sai Musa ya rubuta wannan waƙa a ranar, ya koya wa jama’ar Isra’ila.
23  Sai Ubangiji ya umarci Joshuwa ɗan Nun ya ce, “Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali, gama kai ne za ka kai jama’ar Isra’ila a ƙasar da na rantse zan ba su, ni kuma da kaina zan tafi tare da kai.”
24Sa’ad da Musa ya gama rubuta maganar dokokin nan sarai a littafin, 25sai ya umarci Lawiyawa waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, ya ce, 26“Ku ɗauki littafin dokokin nan, ku ajiye shi tare da akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku domin ya zama shaida a kanku, 27gama na san tayarwarku da taurinkanku. Tun ma ina da rai ke nan tare da ku kuka tayar wa Ubangiji, balle bayan rasuwata. 28Ku tattaro mini dattawan kabilanku da manyanku don in faɗa musu wannan magana a kunnensu, in kuma kira sama da duniya su zama shaida a kansu. 29Gama na sani bayan rasuwata za ku aikata mugunta, ku kauce daga hanyar da na umarce ku. Masifa za ta auko muku a kwanaki masu zuwa saboda za ku aikata mugunta a gaban Ubangiji, za ku tsokani fushinsa da aikin hannuwanku.”

Suratut 2:67-73 (Shanu)

Kuma a lõkacin da Musa yace ga mutanensa: “Lalle ne, Allah Yana umurtar ku da ku yanka wata sãniya.” Suka ce: “Shin kana riƙon mu ne da izgili?” Ya ce: “Ina nẽman tsari daga Allah da in kasance daga jãhilai.”

Suka ce: “Ka rõƙa mana Ubangijinka, Ya bayyana mana, mecẽ ce ita?” Ya ce: “Lalle ne, Shi, Yana cewa: “Lalle ne ita sãniya ce; bã tsõfuwa ba, bã kuma budurwa ba, tsakãtsaki ce a tsakãnin wancan,’ sai ku aikata abin da ake umurninku.”

Suka ce: “Ka rõƙa mana Ubangijinka Ya bayyana mana abin da yake launinta.” Ya ce: “Lalle ne, Shi Yana cewa: “Ita wata saniya ce fatsa-fatsa, mai tsan-tsan launi, tana faranta ran mausu kallonta.”

Suka ce: “Ka rõƙa mana Ubangijinka, Ya bayyana mana abin da yake ita, lalle ne shãnu suna yi mana kamã da jũna, kuma mu, idan Allah Yã so, haƙĩƙa, shiryuwa ne.”

Ya ce: “Lalle ne Shi, Yana cẽwa: “Ita wata sãniya ce; ba horarra bã tana noman ƙasa, kuma ba ta shayar da shuka, lãfiyayya ce: bãbu wani sõfane a cikinta.” Suka ce: “Yanzu kã zo da gaskiya. Sai suka yanka ta, kamar ba zã su aikata ba.

Kuma a lõkacin da kuka yi kisan kai, kuka dinga tunkuɗa wa jũna laifĩ a cikinsa, kuma Allah Mai fitar da abin da kuka kasance kuna ɓõyẽwa ne.

Sai Muka ce: “Ku dõke shi da wani sãshenta.” Kamar wancan ne Allah Yake rãyar da matattu, kuma Ya nũna muku ayõyinSa, tsammãninku kuna hankalta.