Skip to content
Home » From Books » Page 4

From Books

Yohanna 13-16

Yesu Ya Wanke Ƙafafun Almajiransa
1Ana nan tun kafin Idin Ƙetarewa, da Yesu ya san lokacinsa ya yi da zai tashi daga wannan duniya ya koma wurin Uba, da yake ya ƙaunaci mutanensa da suke duniya, ya ƙaunace su har matuƙa. 2Ana cikin cin abincin dare, Iblis kuwa ya riga ya sa a zuciyar Yahuza Iskariyoti ɗan Saminu yă bāshe shi. 3Yesu kuwa, da yake ya san Uba ya sa kome a hannunsa, ya kuma sani daga wurin Allah ya fito, wurin Allah kuma zai koma, 4sai ya tashi daga cin abincin, ya ajiye mayafinsa, ya ɗauko ɗan zane ya yi ɗamara da shi. 5Sa’an nan ya zuba ruwa a daro, ya fara wanke ƙafafun almajiran, yana shafe su da abin da ya yi ɗamara da shi. 6Sai ya zo kan Bitrus, shi kuwa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ashe, kai ne za ka wanke mini ƙafa?” 7Yesu ya amsa ya ce, “Yanzu kam, ba ka san abin da nake yi ba, amma daga baya za ka fahimta.” 8Bitrus ya ce masa, “Wane ni! Ai, ba za ka wanke mini ƙafa ba har abada!” Yesu ya amsa masa ya ce, “In ban wanke maka ba, ba ka da rabo a gare ni.” 9Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ba ma ƙafafuna kaɗai ba, har ma da hannuwana da kaina!” 10Yesu ya ce masa, “Wanda ya yi wanka ba ya bukatar wanke kome, sai ƙafafunsa kawai, domin ya riga ya tsarkaka sarai. Ku ma tsarkakakku ne, amma ba dukanku ne ba.” 11Don ya san wanda zai bāshe shi, shi ya sa ya ce, “Ba dukanku ne tsarkakakku ba.”
12 Bayan ya wanke ƙafafunsu, ya yafa mayafinsa, sai ya sāke kishingiɗa, ya ce musu, “Kun gane abin da na yi muku? 13Kuna kirana Malam, da kuma Ubangiji. Daidai ne kuwa, don haka nake. 14Tun da yake ni Ubangijinku da kuma Malaminku, har na wanke muku ƙafa, ashe, ku ma wajibi ne ku wanke wa juna. 15Na yi muku ishara domin ku ma ku yi yadda na yi muku 16 Lalle hakika, ina gaya muku, bawa ba ya fin ubangijinsa, manzo kuma ba ya fin wanda ya aiko shi. 17In dai kun san wannan, kuna kuma aikatawa, ku masu farin ciki ne. 18 Ba dukanku nake nufi ba. Na san waɗanda na zaɓa. Wannan kuwa duk domin a cika Nassi ne cewa, ‘Wanda yake cin abincina ya tasar mini.’ 19Tun yanzu zan sanar da ku abu tun bai faru ba, domin sa’ad da ya faru ku ba da gaskiya ni ne shi. 20 Lalle hakika, ina gaya muku, wanda ya yi na’am da duk wanda na aiko, ya yi na’am da ni ke nan. Wanda ya yi na’am da ni kuwa, to, ya yi na’am da wanda ya aiko ni.”
Yesu Ya Ce Za a Bāshe Shi
(Mat 26.20-25Mar 14.17-21Luk 22.21-23)
21Bayan da Yesu ya faɗi haka, ya ji nauyi a ransa, ya yi shaida ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, ɗayanku zai bāshe ni.” 22Sai almajiran suka duddubi juna, suka rasa da wanda yake. 23Wani daga cikin almajiransa kuwa, wanda Yesu yake ƙauna, yana kishingiɗe gab da Yesu. 24Sai Bitrus ya alamta masa ya ce, “Gaya mana, da wa yake?” 25Shi kuwa da yake kishingiɗe haka gab da Yesu ya karkata, ya ce masa, “Ya Ubangiji, wane ne?” 26Sai Yesu ya amsa ya ce, “Shi ne wanda zan tsoma ‘yar lomar nan in ba shi.” Da ya tsoma ‘yar lomar kuwa, sai ya ba Yahuza, Ɗan Saminu Iskariyoti. 27Da karɓar ‘yar loman nan Shaiɗan ya shige shi. Yesu ya ce masa, “Yi abin da za ka yi, maza.” 28Amma cikin waɗanda suke cin abinci, ba wanda ya san dalilin da ya sa Yesu ya faɗa masa haka. 29Har waɗansu ma sun yi zaton Yesu ya ce masa ya yi musu sayayyar idi ne, ko kuwa ya ba gajiyayyu wani abu, don Yahuza ne yake riƙe da jakar kuɗinsu. 30Shi kuwa da karɓar ‘yar lomar, sai ya fita, da dare ne kuwa.
Sabon Umarni
31Bayan ya fita kuma sai Yesu ya ce, “Yanzu ne aka ɗaukaka Ɗan Mutum, aka kuma ɗaukaka Allah ta wurinsa. 32Allah kuma zai ɗaukaka shi zuwa ga zatinsa, nan da nan kuwa zai ɗaukaka shi. 33 Ya ku ‘ya’yana ƙanana, saura ɗan lokaci kaɗan ina tare da ku. Za ku neme ni, amma kamar yadda na faɗa wa Yahudawa cewa, ‘Inda za ni ba za ku iya zuwa ba,’ haka nake faɗa muku yanzu. 34 Sabon umarni nake ba ku, shi ne ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, haka ku ma, ku ƙaunaci juna. 35Ta haka, kowa zai gane ku almajiraina ne, in dai kuna ƙaunar juna.”
Bitrus Zai Yi Musun Sanin Yesu
(Mat 26.31-35Mar 14.27-31Luk 22.31-34)
36Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ina za ka?” Yesu ya amsa ya ce, “Inda za ni, ba za ka iya bina yanzu ba, amma daga baya za ka bi ni.” 37Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, don me, ba zan iya binka a yanzu ba? Ai, zan ba da raina saboda kai.” 38Yesu ya amsa ya ce, “Ashe, za ka ba da ranka saboda ni? Lalle hakika, ina gaya maka, kafin zakara ya yi cara, za ka yi musun sanina sau uku.”
Yesu Ne Hanya zuwa Wurin Uban
1“Kada ku damu. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni. 2A gun Ubana akwai wurin zama da yawa. Da ba haka ne ba, da na faɗa muku, domin zan tafi in shirya muku wuri. 3In kuwa na je na shirya muku wuri, sai in dawo in kai ku wurina, domin inda nake, ku ma ku zama kuna can. 4Inda za ni kuwa kun san hanya.” 5Sai Toma ya ce masa, “Ya Ubangiji, ba mu san inda za ka ba, ƙaƙa za mu san hanyar?” 6Yesu ya ce masa, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina. 7Da kun san ni, da kun san Ubana ma. Amma daga yanzu kun san shi, kun kuma gan shi.”
8Sai Filibus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ka nuna mana Uban, bukatarmu ta biya ke nan.” 9Yesu ya ce masa, “Na daɗe tare da ku haka, amma har yanzu ba ka san ni ba, Filibus? Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban. Yaya za ka ce, ‘Nuna mana Uban’”? 10Wato ba ka gaskata ba cikin Uba nake, Uba kuma cikina? Maganar da nake faɗa muku, ba domin kaina nake faɗa ba, Uba ne da yake zaune a cikina yake yin ayyukansa. 11Ku gaskata ni, a cikin Uba nake, Uba kuma cikina, ko kuwa ku gaskata ni saboda ayyukan kansu.
12“Lalle hakika, ina gaya muku, duk wanda yake gaskatawa da ni ayyukan da nake yi shi ma haka zai yi. Har ma, zai yi ayyukan da suka fi waɗannan, domin zan tafi wurin Uba. 13Duk abin da kuka roƙa da sunana kuma zan yi, domin a ɗaukaka Uban ta wurin Ɗan. 14Kome kuke roƙa da sunana, zan yi shi.”
Alkawarin Zuwan Ruhu Mai Tsarki
15“In dai kuna ƙaunata, za ku bi umarnina. 16Ni ma zan roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimako ya kasance tare da ku har abada. 17Shi ne Ruhu na gaskiya, wanda duniya ba ta iya samunsa, domin ba ta ganinsa, ba ta kuma san shi ba. Ku kam, kun san shi, domin yana zaune tare da ku, zai kuma kasance a zuciyarku.
18“Ba zan bar ku marayu ba, zan zo wurinku. 19Saura ɗan lokaci kaɗan duniya ba za ta ƙara ganina ba, amma ku za ku gan ni. Saboda ni a raye nake, ku ma za ku rayu. 20A ran nan ne fa za ku sani, ni cikin Uba nake, ku kuma a cikina, ni kuma a cikinku. 21Duk wanda ya san umarnaina, yake kuma binsu, shi ne mai ƙaunata. Mai ƙaunata kuwa, Ubana zai ƙaunace shi, ni kuma zan ƙaunace shi, in bayyana kaina gare shi.” 22Sai Yahuza (ba Iskariyoti ba) ya ce masa, “Ya Ubangiji, me ya sa za ka bayyana kanka gare mu, ba ga duniya ba?” 23Yesu ya amsa masa ya ce, “Kowa yake ƙaunata, zai kiyaye maganata, Ubana kuwa zai ƙaunace shi, za mu zo wurinsa mu zauna tare da shi. 24Wanda ba ya ƙaunata, ba ya kiyaye maganata. Maganar da kuke ji kuwa ba tawa ba ce, ta Uba ce wanda ya aiko ni.
25“Duk wannan na faɗa muku ne tun muna tare. 26Amma Mai Taimako, Ruhu Mai Tsarki, wanda Uba zai aiko da sunana, shi ne zai koya muku kome, ya kuma tuna muku duk abin da na faɗa muku. 27Na bar ku da salama. Salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada ku damu, kada kuma ku ji tsoro. 28Kun dai ji na ce muku zan tafi, in kuma dawo wurinku. Da kuna ƙaunata da kun yi murna saboda za ni wurin Uba, domin kuwa Uban ya fi ni. 29To, yanzu na faɗa muku tun bai faru ba, domin sa’ad da ya faru, ku ba da gaskiya. 30Ba zan ƙara yi muku magana mai yawa ba, domin mai mulkin duniyan nan yana zuwa, ba shi kuwa da wani hannu a kaina, 31sai dai domin duniya tă sani ina ƙaunar Uban, ina kuma yin yadda Uba ya umarce ni, ku tashi mu tafi daga nan.”
Yesu Ne Itacen Inabi na Hakika
1“Ni ne itacen inabi na hakika, Ubana kuwa shi ne manomi. 2Kowane reshe a cikina da ba ya ‘ya’ya, sai ya datse shi. Kowane reshe mai yin ‘ya’ya kuwa yakan tsarkake shi don ya ƙara haihuwa. 3Koyanzu ma ku tsarkakku ne saboda maganar da na faɗa muku. 4Ku zauna a cikina, ni kuma a cikinku. Kamar yadda reshen inabi, ba ya iya ‘ya’ya shi kaɗai, sai ko ya zauna itacen inabin, haka ku ma ba za ku iya ba, sai kun zauna a cikina. 5Ni ne itacen inabin, ku kuwa rassan. Wanda ya zauna a cikina, ni kuma a cikinsa, shi ne mai yin ‘ya’ya da yawa. Domin in ba game da ni ba, ba za ku iya kome ba. 6Duk wanda bai zauna a cikina ba, za a yar da shi can, kamar reshe, yă bushe, a kuma tattara irinsu a jefa wuta, a ƙone. 7In kun zauna a cikina, maganata kuma ta zauna a cikinku, za ku roƙi duk abin da kuke so, za a kuwa yi muku. 8Yadda ake ɗaukaka Ubana ke nan, in kuna ‘ya’ya da yawa, ta haka kuma kuke tabbata almajiraina. 9Kamar yadda Uba ya ƙaunace ni, haka ni ma na ƙaunace ku. To, ku zauna cikin ƙaunar da nake muku. 10In kun bi umarnina, za ku zauna cikin ƙaunar da nake muku, kamar yadda ni na bi umarnin Ubana, na kuma zauna cikin ƙaunar da yake mini. 11Na gaya muku haka domin farin cikina ya kasance a cikinku, farin cikinku kuma ya zama cikakke.
12  “Wannan fa shi ne umarnina, cewa ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku. 13Ba ƙaunar da ta fi haka ga mutane, wato mutum yă ba da ransa saboda aminansa. 14Ku aminaina ne in kuna yin abin da na umarce ku. 15Nan gaba ba sauran in ce da ku bayi, don bawa bai san abin da ubangijinsa yake yi ba. Sai dai in ce da ku aminai, domin na sanar da ku duk abin da na jiyo wurin Ubana. 16Ba ku kuka zaɓe ni ba, ni ne na zaɓe ku, na sa ku ku je ku yi ‘ya’ya, ‘ya’yanku kuma su tabbata, domin kome kuka roƙi Uba da sunana yă ba ku. 17Na umarce ku haka domin ku ƙaunaci juna.”
Ƙiyayyar Duniya
18In duniya ta ƙi ku, ku sani sai da ta ƙi ni kafin ta ƙi ku. 19Da ku na duniya ne da duniya ta so abinta, amma saboda ku ba na duniya ba ne, na kuma zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku. 20 Ku tuna da maganar da na yi muku cewa, “Bawa ba ya fin ubangijinsa.” In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun kiyaye maganata, da sai su kiyaye taku ma. 21Duk wannan za su yi muku saboda sunana, don ba su san wanda ya aiko ni ba. 22Da ba domin na zo na yi musu magana ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu kam, ba su da wani hanzari a kan zunubinsu. 23Wanda ya ƙi ni ya ƙi Ubana ma. 24Da ba domin na yi ayyuka a cikinsu da ba wanda ya taɓa yi sai ni ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun gani, sun kuma ƙi mu, ni da Ubana duka. 25 An yi wannan kuwa domin a cika maganar da yake a rubuce a cikin Shari’arsu cewa, “Sun ƙi ni ba dalili.” 26Amma sa’ad da Mai Taimako ya zo, wanda zan aiko muku daga wurin Uba, wato Ruhu na gaskiya, mai fitowa daga wurin Uba, shi ne zai shaida ni. 27Ku ma shaidu ne, domin tun farko kuke tare da ni.

Labarin Yan Mata Goma

1  “Sa’an nan za a kwatanta Mulkin Sama da ‘yan mata goma da suka ɗauki fitilunsu suka tafi taryen ango. 2Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuwa masu hikima. 3Don kuwa a lokacin da wawayen nan suka ɗauki fitilunsu, ashe, ba su riƙo mai ba. 4Masu hikimar nan kuwa sun riƙo kwalaben mai da fitilunsu. 5Da yake angon ya yi jinkiri, duk sai suka yi gyangyaɗi, har barci ya share su. 6Can tsakar dare sai aka ji kira, ana cewa, ‘Ga ango nan! Ku fito ku tarye shi!’ 7Duk ‘yan matan nan suka tashi suka gyaggyara fitilunsu. 8Sai wawayen nan suka ce wa masu hikimar, ‘Ku sa mana ɗan manku kaɗan mana, fitilunmu na mutuwa!’ 9Amma masu hikimar suka amsa suka ce, ‘Ai, watakila ba zai ishe mu mu da ku ba. Gara ku je wurin masu sayarwa ku sayo.’ 10Tun suna wajen sayen, sai angon ya iso, waɗanda suke shirye suka shiga wurin biki tare da shi, aka kuma rufe ƙofa. 11Daga baya sai waɗancan ‘yan matan ma suka iso, suka ce, ‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji, ka buɗe mana!’ 12Sai ya amsa ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, ni ban san ku ba.’ 13Don haka, sai ku zauna a faɗake, don ba ku san ranar ba, ko kuwa sa’ar.”
Misali na Talanti
14  “Kamar mutum ne da zai yi tafiya, ya kira bayinsa, ya danƙa musu dukiyarsa. 15Ya ba ɗaya talanti biyar, ɗaya talanti biyu, wani kuma ya ba shi ɗaya, kowa dai gwargwadon ƙarfinsa. Sa’an nan ya tafi. 16Shi wanda ya karɓi talanti biyar ɗin nan, nan da nan sai ya je ya yi ta jujjuya su, har wuri ya bugi wuri. 17Haka kuma wanda ya karɓi talanti biyu, shi ma sai wuri ya bugi wuri. 18Amma wannan da ya karɓi talanti ɗaya ɗin, sai ya je ya tona rami ya ɓoye kuɗin ubangijinsa. 19To, da aka daɗe sai ubangijin bayin nan ya dawo ya daidaita lissafi da su. 20Shi wannan da ya karɓi talanti biyar sai ya matso ya kawo waɗansu talanti biyar, ya ce, ‘Ya ubangiji, kā ba ni talanti biyar, ga shi kuma, na ci ribar biyar.’ 21Sai ubangijinsa ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki, mai aminci. Kā yi gaskiya a kan ƙaramin abu, zan ɗora ka a kan mai yawa. Ka zo ku yi farin ciki tare da ubangidanka.’ 22Sai mai talanti biyun nan kuma ya matso, ya ce, ‘Ya ubangiji, kā ba ni talanti biyu, ga shi kuma, na ci ribar biyu.’ 23Sai ubangijinsa ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki, mai aminci. Kā yi gaskiya a kan ƙaramin abu, zan ɗora ka a kan mai yawa. Ka zo ku yi farin ciki tare da ubangijinka.’ 24Shi kuma wanda ya karɓi talanti guda ɗin, sai ya matso, ya ce, ‘Ya ubangiji, na sani kai mutum ne mai tsanani, kana son girbi inda ba kai ka shuka ba, mai son banza ne. 25Shi ya sa na ji tsoro, har na je na yi tono na ɓoye talantinka. To, ga kayanka nan!’ 26Sai ubangijinsa ya amsa masa ya ce, ‘Kai mugun bawa, malalaci! Ashe, ka sani ina girbi inda ba ni na shuka ba, ni kuma mai son banza ne? 27Ya kamata ka sa kuɗina a ma’aji, da na dawo kuma da sai in karɓi abina har da riba! 28Don haka sai ku karɓe talantin daga gunsa, ku bai wa mai goman nan. 29 Don duk mai abu a kan ƙara wa, har ya yalwata. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa. 30 Ku kuma jefa banzan bawan nan a baƙin duhu. Nan za a yi kuka da cizon baki.’ ”
Shara’anta wa Al’ummai
31  “Sa’ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa tare da mala’iku duka, sa’an nan ne zai zauna a maɗaukakin kursiyinsa. 32Za a tara dukan al’ummai a gabansa, zai kuma ware su dabam dabam, kamar yadda makiyayi yake ware tumaki da awaki. 33Zai sa tumaki a damansa, awaki kuwa a hagunsa. 34Sa’an nan ne Sarki zai ce wa waɗanda suke dama da shi, ‘Ku zo, ya ku da Ubana ya yi wa albarka, sai ku gāji mulkin da aka tanadar muku tun daga farkon duniya. 35Domin na ji yunwa, kun ba ni abinci. Na ji ƙishirwa, kun ba ni na sha. Na yi baƙunci, kun saukar da ni. 36Na yi huntanci, kun tufasar da ni. Na yi rashin lafiya, kun ziyarce ni. Ina kurkuku, kun kula da ni.’ 37Sa’an nan ne masu adalci za su amsa masa su ce, ‘Ya Ubangiji, a yaushe muka gan ka da yunwa muka cishe ka, ko kuwa da ƙishirwa muka shayar da kai? 38A yaushe kuma muka gan ka baƙo muka sauke ka, ko kuwa huntu muka tufasar da kai? 39Ko kuma a yaushe muka gan ka da rashin lafiya, ko a kurkuku muka kula da kai?’ 40Sai Sarkin zai amsa musu ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, tun da yake kun yi wa ɗaya daga cikin waɗannan ‘yan’uwana mafi ƙanƙanta, ai, ni kuka yi wa.’ 41Sa’an nan zai ce wa waɗanda suke na hagun, ‘Ku rabu da ni, la’anannu, ku shiga madawwamiyar wuta, wadda aka tanadar wa Iblis da mala’ikunsa. 42Don na ji yunwa, ba ku ba ni abinci ba. Na ji ƙishirwa, ba ku ba ni abin sha ba. 43Na yi baƙunci, ba ku sauke ni ba. Na yi huntanci, ba ku tufasar da ni ba. Na yi rashin lafiya, ina kuma kurkuku, ba ku kula da ni ba.’ 44Sa’an nan su ma za su amsa su ce, ‘Ya Ubangiji, a yaushe muka gan ka da yunwa, ko da ƙishirwa, ko da baƙunci, ko da huntanci, ko da rashin lafiya, ko a kurkuku, ba mu kula da kai ba?’ 45Sa’an nan zai amsa musu ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, tun da yake ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ai, ni ne ba ku yi mini ba.’ 46 Waɗannan ne za su shiga madawwamiyar azaba, masu adalcikuwa rai madawwami.

Matiyu 21:23 – 23:39

Tambaya Game da Mulkin Yesu

23Ya shiga Haikali yana cikin koyarwa, sai manyan firistoci da shugabannin jama’a suka zo wurinsa, suka ce, “Da wane izini kake yin abubuwan nan, wa ya ba ka izinin?” 24Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. In kun ba ni amsa, ni ma sai in gaya muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan. 25To, baftismar da Yahaya ya yi, daga ina take? Daga Sama take, ko kuwa ta mutum ce?” Sai suka yi ta muhawwara da juna, suna cewa, “In muka ce, ‘Daga Sama take,’ sai ya ce mana, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’ 26In kuwa muka ce, ‘Ta mutum ce,’ ai, muna jin tsoron jama’a, don duk kowa ya ɗauki Yahaya a kan annabi ne.” 27Sai suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Shi kuma ya ce musu, “Haka ni kuma ba zan faɗa muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan ba.”
Misali na Mai ‘Ya’ya Biyu Maza
28“To, me kuka gani? An yi wani mutun mai ‘ya’ya biyu maza. Ya je wurin na farkon, ya ce, ‘Ɗana, yau je ka ka yi aiki a garkar inabi.’ 29Sai ya ce, ‘Na ƙi.’ Amma daga baya sai ya tuba, ya tafi. 30Sai ya je gun na biyun ya faɗa masa haka. Shi kuwa ya amsa ya ce, ‘To, za ni, baba,’ amma bai je ba. 31To, wane ne a cikin su biyun ya yi abin da ubansu yake so?” Sai suka ce, “Na farkon.” Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga Mulkin Allah. 32 Ga shi, Yahaya ya zo ya bayyana muku hanyar adalci, ba ku gaskata shi ba. Amma masu karɓar haraji da karuwai sun gaskata shi, duk da ganin haka kuma, daga baya ba ku tuba kun gaskata shi ba.”
Misali na Manoman da Suka Yi Sufurin Garkar Inabi
33  “To, ga kuma wani misali. An yi wani maigida da ya yi garkar inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabi a ciki, ya kuma gina wata ‘yar hasumiyar tsaro. Ya ba waɗansu manoma sufurin garkar, sa’an nan ya tafi wata ƙasa. 34Da kakar inabi ta kusa, sai ya aiki bayinsa wurin manoman nan su karɓo masa gallar garkar. 35Manoman kuwa suka kama bayinsa, suka yi wa ɗaya dūka, suka kashe ɗaya, suka kuma jajjefi ɗaya. 36Har wa yau ya sāke aiken waɗansu bayi fiye da na dā, suka kuma yi musu haka. 37Daga baya sai ya aiki ɗansa gare su, yana cewa, ‘Sā ga girman ɗana.’ 38Amma da manoman suka ga ɗan, suka ce wa juna, ‘Ai, wannan shi ne magajin, ku zo mu kashe shi, gādonsa ya zama namu.’ 39Sai suka kama shi, suka jefa shi bayan shinge, suka kashe shi. 40To, sa’ad da ubangijin garkar nan ya zo, me zai yi wa manoman nan?” 41Sai suka ce masa, “Zai yi wa mutanen banzan nan mugun kisa, ya ba waɗansu manoma sufurinta, waɗanda za su riƙa ba shi gallar garkar a lokacin nunanta.”
42  Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karantawa a Littattafai ba? cewa,
“ ‘Dutsen da magina suka ƙi,
Shi ne ya zama mafificin dutsen gini.
Wannan aikin Ubangiji ne,
A gare mu kuwa abin al’ajabi ne.’
43“Domin haka ina gaya muku, za a karɓe Mulkin Allah daga gare ku, a bai wa wata al’umma wadda za ta ba da amfani nagari. 44Kowa ya faɗo a kan dutsen nan, sai ya ragargaje. Amma wanda dutsen nan ya faɗa wa, niƙe shi zai yi kamar gari.”
45Da manyan firistoci da Farisiyawa suka ji misalan nan da ya yi, sai suka gane, ashe, da su yake. 46Amma da suka nemi kama shi, suka ji tsoron jama’a, don su sun ɗauke shi shi annabi ne
Misali na Bikin Aure
1Yesu ya sāke yi musu magana da misalai ya ce, 2“Za a kwatanta Mulkin Sama da wani sarki, wanda ya yi wa ɗansa biki. 3Sai ya aiki bayinsa su kirawo waɗanda aka gayyata bikin, amma waɗanda aka gayyatar suka ƙi zuwa. 4Har wa yau ya sāke aiken waɗansu bayi, ya ce, ‘Ku gaya wa waɗanda aka gayyata, “Ga shi, na shisshirya abinci, an yanka shanuna da kiwatattun maruƙana, duk an shirya kome, ku zo bikin mana!” ’ 5Amma suka ƙi kula, suka tafi abinsu, wani ya tafi gona tasa, wani kuma cinikinsa. 6Sauran kuwa suka kame bayinsa, suka wulaƙanta su, suka kashe su. 7Sarki ya yi fushi, ya tura sojansa, suka hallaka masu kisankan nan, suka ƙone garinsu ƙurmus. 8Sa’an nan ya ce wa bayinsa, ‘Bikin fa ya shiryu sosai, amma waɗanda aka gayyata ba su cancanta ba. 9Saboda haka ku tafi ƙofofin gari, ku gayyato duk waɗanda kuka samu, su zo bikin.’ 10Sai bayin suka yi ta bin titi titi, suka tattaro duk waɗanda suka samu, mugaye da nagargaru duka, har wurin bikin ya cika maƙil da baƙi.
11“Da sarki ya shigo ganin baƙin sai ya ga wani mutum a can wanda bai sa riga irin ta biki ba. 12Sai ya ce masa, ‘Malam, ta yaya ka shigo nan ba tare da sa riga irin ta biki ba?’ Mutumin kuwa ya rasa ta cewa. 13 Sai sarki ya ce wa barorinsa, ‘Ku ɗaure shi ƙafa da hannu, ku jefa shi cikin matsanancin duhu. Nan za a yi kuka da cizon baƙi.’ 14Gama da yawa ake kira, amma kaɗan ne zaɓaɓɓu.”
Biyan Haraji ga Kaisar
15Sai Farisiyawa suka je suka yi shawara yadda za su burma shi cikin maganarsa. 16Suka aiko almajiransu wurinsa tare da waɗansu mutanen Hirudus, suka ce, “Malam, ai, mun sani kai mai gaskiya ne, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi, ba ka kuma zaɓen kowa, don ka ɗauki kowa da kowa daidai. 17To, faɗa mana abin da ka gani. Shin, daidai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa?” 18Yesu kuwa domin ya gane muguntarsu, sai ya ce musu, “Don me kuke jarraba ni? Ku munafukai! 19Ku nuna mini kuɗin harajin.” Sai suka kawo masa dinari. 20Yesu ya ce musu, “Surar nan da sunan nan na wane ne?” 21Suka ce, “Na Kaisar ne.” Sa’an nan ya ce musu, “To, sai ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.” 22Da suka ji haka, sai suka yi mamaki, suka rabu da shi, suka yi tafiyarsu.
Tambaya a kan Tashin Matattu
23  A ran nan sai waɗansu Sadukiyawa (su da suke cewa, ba tashin matattu) suka zo wurinsa, suka yi masa tambaya, 24 suka ce, “Malam, Musa dai ya ce, ‘In mutum ya mutu, bai bar na baya ba, sai lalle ɗan’uwansa ya auri matar, ya haifa wa ɗan’uwansa ‘ya’ya.’ 25To, an yi waɗansu ‘yan’uwa maza bakwai a cikinmu. Na farkon ya yi aure, da ya rasu, da yake bai haifu kuma ba, sai ya bar wa ɗan’uwansa matarsa. 26Haka ya faru ga na biyun da na ukun, har ya kai kan na bakwai ɗin. 27Bayansu duka sai matar ta rasu. 28To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu, su bakwai ɗin? Don duk sun aure ta.”
29Amma Yesu ya amsa musu ya ce, “Kun ɓăta ne, domin ba ku san Littattafai ba, ba ku kuma san ikon Allah ba. 30Domin a tashin matattu, ba a aure, ba a aurarwa, sai dai kamar mala’ikun da suke Sama ake. 31Game da tashin matattu, ashe, ba ku taɓa karanta abin da Allah ya ce muku ba? cewa, 32 ‘Ni ne Allahn Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.’ Ai, waɗanda Allah shi ne Allahnsu rayayyu ne, ba matattu ba.” 33Da jama’a suka ji haka, sai suka yi mamakin koyarwarsa.
Umarni Mafi Girma
34Amma da Farisiyawa suka ji ya ƙure Sadukiyawa, suka taru. 35Ɗaya daga cikinsu, wani masanin Attaura, ya yi masa tambaya, yana gwada shi, ya ce, 36“Malam, wane umarni ne mafi girma a cikin Attaura?” 37 Ya ce masa, “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka. 38Wannan shi ne babban umarni na farko. 39 Na biyu kuma kamarsa yake, ‘Ka ƙaunaci ɗan’uwanka kamar kanka.’ 40 A kan umarnin nan biyu duk Attaura da koyarwar annabawa suka rataya.”
Tambaya a kan Ɗan Dawuda
41Tun Farisiyawa suna tare gu ɗaya, sai Yesu ya yi musu tambaya, 42ya ce, “Yaya kuka ɗauki Almasihu? Shi ɗan wane ne?” Sai suka ce masa, “Ɗan Dawuda ne.” 43Ya ce musu, “To, yaya kuwa Dawuda, ta ikon Ruhu, ya ce da shi Ubangiji? Har ya ce,
44  “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,
Zauna a damana,
Sai na ɗora ka a kan maƙiyanka.’
45“Tun da Dawuda ya kira shi Ubangiji ne, to, ƙaƙa zai zama ɗansa?” 46Ba kuwa wanda ya iya tanka masa. Daga ran nan kuwa ba wanda ya yi ƙarfin halin sāke tambayarsa wani abu.
Yesu Ya Fallashi Malaman Attaura da Farisiyawa
1Sa’an nan Yesu ya yi wa jama’a da almajiransa magana, ya ce, 2“Malaman Attaura da Farisiyawa suka tsaya a matsayin Musa. 3Don haka, sai ku kiyaye, ku kuma aikata duk abin da suka gaya muku, amma banda aikinsu. Don suna faɗa ne, ba aikatawa. 4Sukan ɗaura kaya masu nauyi, masu wuyar ɗauka, su jibga wa mutane a kafaɗa. Amma su kansu ko tallafa musu da ɗan yatsa ba sa yi. 5 Duk ayyukansu suna yi ne don idon mutane, suna yin layunsu fantam-fantam, lafin rigunansu kuma har gwiwa. 6Suna son mazaunan alfarma a wurin biki, da mafifitan mazaunai a majami’u, 7a gaishe su a kasuwa, a kuma riƙa ce da su ‘Malam’. 8Amma ku kam, kada a ce muku ‘Malam’, domin Malaminku ɗaya ne, ku duka kuwa ‘yan’uwa ne. 9Kada ku kira kowa ‘Uba’ a duniya, domin Uba ɗaya ne yake gare ku, wanda yake cikin Sama. 10Kada kuma a kira ku ‘Shugabanni’, domin Shugaba ɗaya gare ku, wato, Almasihu. 11 Amma wanda yake babba a cikinku shi zai zama baranku. 12 Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.
13“Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kun toshe wa mutane ƙofar Mulkin Sama. Ku kanku ba ku shiga ba, kuna kuwa hana masu niyyar shiga shiga. 14[Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan ci kayan matan da mazansu sun mutu, kukan yi doguwar addu’a don ɓad da sawu. Saboda haka za a yi muku hukunci mafi tsanani.] 15Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan kewaye ƙasashe da tekuna don samun almajiri ɗaya tak, in kuwa kun samu, kukan mai da shi ɗan wuta fiye da ku, ninkin ba ninkin.
16“Kaitonku, makafin jagora, ku da kuke cewa, ‘Kowa ya rantse da Haikalin ba kome, amma duk wanda ya rantse da zinariyar Haikalin, sai rantsuwarsa ta kama shi.’ 17Ku makafi, wawaye! Wanne ya fi girma, zinariyar ce ko kuwa Haikalin da yake tsarkake zinariyar? 18Kukan ce, ‘Kowa ya rantse da bagaden hadaya, ba kome. Amma duk wanda ya rantse da sadakar da aka ɗora a kai, sai rantsuwarsa ta kama shi.’ 19Ku makafi! Wanne ya fi girma, sadakar ko kuwa bagaden hadaya da yake tsarkake sadakar? 20Don haka kowa ya rantse da bagaden hadaya, ya rantse ke nan da shi, da duk abin da yake a kansa. 21Duk kuma wanda ya rantse da Haikalin ya rantse da shi, da kuma wanda yake zaune a cikinsa. 22 Kowa kuma ya rantse da Sama, ya rantse da kursiyin Allah, da kuma wanda yake zaune a kansa.
23  “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan fitar da zakkar na’ana’a, da anise, da lafsur, amma kun yar da muhimman jigajigan Attaura, wato, gaskiya, da jinƙai, da aminci. Waɗannan ne ya kamata ku yi, ba tare da yar da sauran ba. 24Makafin jagora, kukan tace ƙwaro ɗan mitsil, amma kukan haɗiye raƙumi!
25“Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan wanke bayan ƙwarya da akushi, amma a ciki cike suke da zalunci da zari. 26Kai makahon Bafarisiye! Sai ka fara tsarkake cikin ƙwaryar da akushin don bayansu ma ya tsarkaka.
27  “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kamar kaburburan da aka shafa wa farar ƙasa kuke, masu kyan gani daga waje, daga ciki kuwa sai ƙasusuwan matattu da ƙazanta iri iri. 28Haka nan a idon mutane ku adalai ne, amma ciki sai munafunci da mugun aiki.
29“Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan yi gini a kan kaburburan annabawa, kuna ƙawata gubbobin adalai. 30Kuna cewa, ‘Da mun zauna a zamanin kakanninmu, da ba mu taya su zub da jinin annabawa ba.’ 31Ta haka kuka shaidi kanku ku ne ‘ya’yan masu kisan annabawa. 32To, sai ku cikasa ayyukan kakanninku! 33 Ku macizai! Yaya za ku tsere wa hukuncin Gidan Wuta? 34Saboda haka nake aiko muku da annabawa, da masu hikima, da masanan Attaura, za ku kashe waɗansunsu, ku gicciye waɗansu, ku kuma yi wa waɗansu bulala a majami’unku, kuna binsu gari gari kuna gwada musu azaba. 35 Don alhakin jinin dukan adalai da aka zubar a duniya yă komo a kanku, tun daga jinin Habila adali, har ya zuwa na Zakariya ɗan Berikiya, wanda kuka kashe a tsakanin Haikalin da bagaden hadaya. 36Hakika, ina gaya muku, duk wannan zai auko wa mutanen wannan zamani.”
Yesu Ya Ji Juyayin Urushalima
37“Ya mutanen Urushalima! Ya mutanen Urushalima! Masu kisan annabawa, masu jifan waɗanda aka aiko a gare ku! Sau nawa ne na so in tattaro ku kamar yadda kaza take tattara ‘yan tsakinta cikin fikafikanta, amma kun ƙi! 38 Ga shi, an bar muku gidanku a yashe! 39 Ina dai gaya muku, ba za ku ƙara ganina ba, sai ran da kuka ce, ‘Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji.’ ”