Skip to content

From Books

Ya Tiyofalas, tarihin nan na farko wanda na rubuta, ya shafi dukan abubuwan da Yesu ya fara yi, da kuma waɗanda ya fara koyarwa, 2har ya zuwa ranar da aka ɗauke shi aka kai shi Sama, bayan ya yi umarni ta wurin Ruhu Mai Tsarki ga manzannin da ya zaɓa. 3Ya bayyana kansa gare su a raye bayan shan wuya tasa, tare da tabbatarwa masu yawa, masu ƙarfi kuma, yana bayyana gare su a kai a kai har kwana arba’in, yana zancen al’amuran Mulkin Allah. 4 Sa’ad da yake tare da su, ya umarce su kada su tashi daga Urushalima, amma su jira cikar alkawarin nan da Uba ya yi, “wanda kuka ji daga bakina, 5domin Yahaya kam, da ruwa ya yi baftisma, amma kafin ‘yan kwanaki da Ruhu Mai Tsarki za a yi muku baftisma.”
An Ɗauke Almasihu Sama
(Mar 16.19-20Luk 24.50-53)
6Saboda haka da suka taru, suka tambaye shi suka ce, “Ya Ubangiji, yanzu ne za ka sāke kafa wa Isra’ila mulki?” 7Ya ce musu, “Sanin lokatai da zamanai, da Uba ya sa cikin ikonsa, ba naku ba ne. 8 Amma za ku sami iko sa’ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauko muku, za ku kuma zama shaiduna a Urushalima, da duk ƙasar Yahudiya, da ta Samariya, har ya zuwa iyakar duniya.”
9  Da ya faɗi haka, suna cikin dubawa, sai aka ɗauke shi Sama, wani gajimare ya tafi da shi, ba su ƙara ganinsa ba. 10Suna cikin zuba ido sama, shi kuma yana tafiya, sai ga mutum biyu tsaye kusa da su, saye da fararen tufafi. 11Sai suka ce, “Ya ku mutanen Galili, don me kuke tsaye kuna duban sama? Yesun nan da aka ɗauke daga gare ku aka kai shi Sama, zai komo ne ta yadda kuka ga tafiyarsa zuwa Sama.”

(Ayyukan Manzanni 1-11 1-11)

Farawa 1-2

Allah ya Halicci Duniya ya kuma Halicci Mutum
1A sa’ad da Allah ya fara halittar Sama da duniya, 2duniya ba ta da siffa, sarari ce kawai, duhu kuwa yana lulluɓe da fuskar zurfin teku, Ruhun Allah kuma yana shawagi bisa ruwayen. 3 Allah ya ce, “Bari haske ya kasance,” sai kuwa ya kasance. 4Allah ya ga hasken yana da kyau. Allah ya raba tsakanin hasken da duhu, 5ya ce da hasken, “Yini,” duhu kuwa, “Dare.” Ga maraice, ga safiya, kwana ɗaya ke nan.
6  Allah ya ce, “Bari sarari ya kasance tsakanin ruwaye, don ya raba tsakaninsu.” 7Allah kuwa ya yi sarari, ya kuma raba tsakanin ruwayen da suke ƙarƙashin sararin da ruwayen da suke birbishin sararin. Haka nan kuwa ya kasance. 8Allah ya ce da sarari, “Sararin sama.” Ga maraice, ga safiya, kwana na biyu ke nan.
9Allah kuwa ya ce, “Bari ruwayen da suke ƙarƙashin sararin su tattaru wuri ɗaya, bari kuma sandararriyar ƙasa ta bayyana.” Haka nan kuwa ya kasance. 10Allah ya ce da sandararriyar ƙasar, “Duniya,” tattaruwan ruwayen da aka tara kuwa, ya ce da su, “Tekuna.” Allah ya ga yana da kyau. 11Allah kuwa ya ce, “Bari ƙasa ta fid da tsire-tsire, na masu ba da tsaba, da itatuwa masu ba da ‘ya’ya, kowanne bisa ga nasa iri, waɗanda suke da ‘ya’ya masu ƙwaya a cikinsu, waɗanda irinsa suke cikin duniya.” Haka nan kuwa ya kasance. 12Ƙasa ta fid da tsire-tsire, na masu ba da ‘ya’ya waɗanda suke da ƙwayar irinsu a cikinsu, Allah ya ga yana da kyau. 13Ga maraice, ga safiya, kwana na uku ke nan.
14Allah kuwa ya ce, “Bari haskoki su kasance a cikin sararin, su raba tsakanin yini da dare, su kuma zama alamu, da yanayi na shekara, da wokatai. 15Bari kuma su zama haskoki a cikin sarari su haskaka duniya.” Haka nan kuwa ya kasance. 16Allah kuwa ya yi manyan haskokin nan biyu, haske mafi girma ya mallaki yini, ƙaramin kuwa ya mallaki dare, ya kuma yi taurarin. 17Allah ya sa su a cikin sarari su haskaka duniya, 18su yi mulkin yini da kuma dare, su raba tsakanin haske da duhu. Allah kuwa ya ga yana da kyau. 19Ga maraice, ga safiya, kwana na huɗu ke nan.
20Allah kuwa ya ce, “Bari ruwaye su fid da ɗumbun masu rai, bari tsuntsaye kuma su riƙa tashi bisa duniya ƙarƙashin sarari.” 21Allah kuwa ya halicci manya manyan dodani na teku da kowane irin mai rai da yake motsi, waɗanda suke a cikin ruwaye, da kuma kowane irin tsuntsu. Allah kuwa ya ga yana da kyau. 22Sai Allah ya sa musu albarka, yana cewa, “Ku hayayyafa, ku kuma riɓaɓɓanya, ku cika ruwayen tekuna, tsuntsaye kuma ku hayayyafa cikin duniya.” 23Ga maraice, ga safiya, kwana na biyar ke nan.
24Allah kuwa ya ce, “Bari duniya ta fid da masu rai bisa ga irinsu, shanu, da abubuwa masu rarrafe, da dabbobin duniya bisa ga irinsu.” 25Allah kuwa ya yi dabbobin gida bisa ga irinsu, da kuma na jeji, manya da ƙanana, da kowane irin mai rarrafe bisa ƙasa bisa ga irinsa. Allah kuwa ya ga yana da kyau.
26  Allah kuma ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, da kamanninmu, su mallaki kifayen da suke a cikin teku, da tsuntsayen sararin sama, da dabbobi, da dukan duniya, da kowane abu mai rarrafe da yake rarrafe bisa ƙasa.” 27 Haka nan fa, Allah ya halicci mutum cikin siffarsa, cikin siffar Allah, Allah ya halicci mutum, namiji da ta mace ya halicce su. 28Allah kuwa ya sa musu albarka, ya ce musu, “Ku hayayyafa ku riɓaɓɓanya, ku cika duniya, ku yi iko da ita, ku mallaki kifayen teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma dukan abin da yake da rai da yake kai da kawowa cikin duniya.” 29Allah kuwa ya ce, “Ga shi, na ba ku kowane tsiro mai ba da tsaba da yake bisa fuskar dukan duniya, da kowane itacen da yake da ƙwaya cikin ‘ya’yansa su zama abincinku. 30Na ba da kowane irin ɗanyen tsiro domin ci, ga kowace irin dabbar da take duniya, da kowane irin tsuntsun da yake sararin sama, da kowane irin abin da yake rarrafe bisa duniya, da dai iyakar abin da yake numfashi.” Haka nan ya kasance. 31Allah kuwa ya ga dukan abin da ya yi, ga shi kuwa yana da kyau ƙwarai. Ga maraice, ga safiya, kwana na shida kenan
Kukan Azaba da Waƙar Yabo
1  Ya Allahna, ya Allahna,
Don me ka yashe ni?
Na yi kuka mai tsanani, ina neman taimako,
Amma har yanzu ba ka zo ba!
2Da rana na yi kira a gare ka, ya Allahna,
Amma ba ka amsa ba.
Da dare kuma na yi kira,
Duk da haka ban sami hutawa ba.
3Amma an naɗa ka Mai Tsarki,
Wanda Isra’ila suke yabonsa.
4Kakanninmu suka dogara gare ka,
Sun dogara gare ka, ka kuwa cece su.
5Suka yi kira gare ka, suka tsira daga hatsari,
Suka dogara gare ka, ba su kuwa kunyata ba.
6A yanzu dai ni ba mutum ba ne, tsutsa ne kawai,
Rainanne, abin ba’a ga kowa da kowa!
7  Duk wanda ya gan ni
Sai yă maishe ni abin dariya,
Suna zunɗena da harshensu suna kaɗa kai.
8  Suka ce, “Ka dogara ga Ubangiji,
Me ya sa bai cece ka ba?
Idan Ubangiji na sonka,
Don me bai taimake ka ba?”
9Kai ne ka fito da ni lafiya a lokacin da aka haife ni,
A lokacin da nake jariri ka kiyaye ni.
10Tun daga lokacin da aka haife ni nake dogara gare ka,
Kai ne Allahna tun daga ran da aka haife ni.
11Kada ka yi nisa da ni!
Wahala ta gabato,
Ba kuwa mai taimako.
12Magabta da yawa sun kewaye ni kamar bijimai,
Dukansu suna kewaye da ni,
Kamar bijimai masu faɗa na ƙasar Bashan.
13Sun buɗe bakinsu kamar zakoki,
Suna ruri, suna ta bina a guje.
14Ƙarfina ya ƙare,
Ya rabu da ni kamar ruwan da ya zube ƙasa.
Dukan gaɓoɓina sun guggulle,
Zuciyata ta narke kamar narkakken kakin zuma.
15Maƙogwarona ya bushe kamar ƙura,
Harshena kuma na liƙe wa dasashina na sama.
Ka bar ni matacce cikin ƙura.
16Ƙungiyar mugaye na kewaye da ni,
Suka taso mini kamar garken karnuka,
Suka soke hannuwana da ƙafafuna.
17Ana iya ganin ƙasusuwana duka.
Magabtana suka dube ni, suka zura mini ido.
18  Suka rarraba tufafina a tsakaninsu,
Suka jefa kuri’a a kan babbar rigata.
19Kada ka yi nisa da ni, ya Ubangiji!
Ka gaggauta ka cece ni, ya Mai Cetona!
20Ka cece ni daga takobi,
Ka ceci raina daga waɗannan karnuka.
21Ka kuɓutar da ni daga waɗancan zakoki,
Ba ni da mataimaki a gaban bijimai masu mugun hali.
22  Zan faɗa wa mutanena abin da ka yi,
Zan yabe ka cikin taronsu.
23“Ku yabe shi, ku bayin Ubangiji!
Ku girmama shi, ku zuriyar Yakubu!
Ku yi masa sujada, ku jama’ar Isra’ila!
24Ba ya ƙyale matalauta,
Ko ya ƙi kulawa da wahalarsu,
Ba ya rabuwa da su,
Amma yakan amsa lokacin da suka nemi taimako.”
25Zan yabe ka a gaban babban taron jama’a
Saboda abin da ka yi,
A gaban dukan masu yi maka biyayya,
Zan miƙa sadakokin da na alkawarta.
26Matalauta za su ci yadda suke so,
Masu zuwa wurin Ubangiji za su yabe shi,
Su arzuta har abada!
27Dukan al’ummai za su tuna da Ubangiji,
Za su zo gare shi daga ko’ina a duniya,
Dukan kabilai za su yi masa sujada.
28Ubangiji Sarki ne,
Yana mulki a kan al’ummai.
29Masu girmankai duka za su rusuna masa,
‘Yan adam duka za su rusuna masa,
Dukan waɗanda aka ƙaddara musu mutuwa.
30Zuriya masu zuwa za su bauta masa,
Mutane za su ambaci Ubangiji ga zuriya mai zuwa.
31Mutanen da ba a haifa ba tukuna, za a faɗa musu,
“Ubangiji ya ceci jama’arsa!”