1Ubangiji ya yi magana da Musa da Haruna, ya ce, 2“Wannan ita ce ka’ida wadda Ubangiji ya umarta. Ka faɗa wa Isra’ilawa su kawo maka jar karsana, marar lahani, wadda ba ta da wani aibi, wadda ba a taɓa aza mata karkiya ba. 3Sai ka ba Ele’azara firist ita, sa’an nan a kai ta bayan sansani, a yanka ta gabansa. 4Ele’azara, firist, kuwa zai ɗibi jininta da yatsansa, ya yayyafa sau bakwai a wajen alfarwar ta sujada. 5Sai a ƙone karsanar a idonsa, za a ƙone fatarta, da naman, da jinin, tare da tarosonta. 6Firist zai ɗauki itacen al’ul, da ɗaɗɗoya, da mulufi, ya jefa a wutar da take ƙone karsanar. 7Sai firist ɗin ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, sa’an nan ya shiga zangon. Firist ɗin zai ƙazantu har zuwa maraice. 8Shi kuma wanda ya ƙone karsanar, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, shi ma zai ƙazantu har zuwa maraice. 9Mutumin da yake da tsarki shi zai tara tokar karsanar, ya ajiye a wuri mai tsabta a bayan zangon. Za a adana tokar domin jama’ar Isra’ila, za a riƙa zubawa a ruwa don tsarkakewar zunubi. 10Shi kuma wanda ya tara tokar karsanar, sai ya wanke tufafinsa zai ƙazantu har maraice. Wannan ka’ida ce ta har abada ga Isra’ilawa da baƙin da yake zama tare da su.”
Taɓa Gawa
11“Duk wanda ya taɓa gawa zai ƙazantu har kwana bakwai. 12A rana ta uku da ta bakwai zai tsarkake kansa da ruwa, zai kuwa tsarkaka, amma in a rana ta uku da ta bakwai bai tsarkake kansa ba, to, ba zai tsarkaka ba. 13Duk wanda ya taɓa gawa, bai kuwa tsarkake kansa ba, ya ƙazantar da alfarwa ta sujada ta Ubangiji, ba za a lasafta shi cikin mutanen Allah ba, domin ba a yayyafa masa ruwan tsarkakewa ba.
14“Wannan ita ce ka’ida a kan wanda ya rasu a alfarwa, duk wanda ya shiga alfarwar, da duk wanda yake cikin alfarwar zai ƙazantu har kwana bakwai. 15Kowace buɗaɗɗiyarsa kuma wadda ba a rufe ba, za ta ƙazantu. 16Wanda duk yake cikin saura ya taɓa wanda aka kashe da tokobi, ko gawa, ko ƙashin mutum, ko kabari zai ƙazantu har kwana bakwai.
17“Don a tsarkake ƙazantar, sai a ɗiba daga cikin tokar hadaya don zunubi a cikinsa, sa’an nan a zuba ruwa mai gudu. 18Tsarkakakken mutum zai ɗauki ɗaɗɗoya ya tsoma a ruwan, ya yayyafa wa alfarwar, da bisa kan dukan kayayyakin da suke ciki, da a kan mutanen da suke a wurin, da kan wanda ya taɓa ƙashin, ko ya taɓa wanda aka kashe, ko ya taɓa gawa, ko kabari. 19A kan rana ta uku da ta bakwai kuma, wanda yake da tsarki zai yayyafa wa marar tsarkin ruwa, ya tsarkake shi. Sai mutumin ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, da maraice kuwa zai tsarkaka.
20“Amma mutumin da ba shi da tsarki, bai kuwa tsarkake kansa ba, ba za a lasafta shi cikin jama’ar Allah ba, tun da yake ya ƙazantar da alfarwa ta sujada ta Ubangiji, gama ba a yayyafa masa ruwan da akan yayyafa wa marasa tsarki ba. 21Wannan zai zama musu ka’ida har abada. Wanda ya yayyafa ruwan tsarkakewa, sai ya wanke tufafinsa, wanda kuma ya taɓa ruwan tsarkakewa zai zama marar tsarki har maraice. 22Duk abin da mutumin da ba shi da tsarki ya taɓa zai ƙazantu, duk wanda kuma ya taɓa abin da marar tsarkin ya taɓa zai ƙazantu har maraice.”
1Sai Ubangiji ya yi magana da Musa bayan rasuwar ‘ya’yan Haruna, maza biyu, sa’ad da suka hura wuta marar tsarki a gaban Ubangiji, suka mutu. 2 Ubangiji kuma ya ce wa Musa, “Faɗa wa ɗan’uwanka Haruna kada ya riƙa shiga Wuri Mafi Tsarki bayan labule ko yaushe, wato, a gaban murfi wanda yake bisa akwatin alkawari, domin kada ya mutu, gama zan bayyana a cikin girgije a kan murfin. 3 Amma sai Haruna ya shiga Wuri Mafi Tsarki bayan da ya kawo ɗan bijimi domin yin hadaya don zunubi, da rago don yin hadaya ta ƙonawa.”
4Sa’an nan Ubangiji ya ba Musa ka’idodin nan. Sai Haruna ya sa zilaika ta lilin tsattsarka, ya ɗaura mukuru na lilin, ya yi ɗamara da abin ɗamara na lilin, ya naɗa rawani na lilin, waɗannan su ne tsattsarkar sutura. Zai yi wanka da ruwa, sa’an nan ya sa su.
5Zai karɓi bunsuru biyu daga taron jama’ar Isra’ila domin yin hadaya don zunubi, da rago ɗaya don yin hadaya ta ƙonawa. 6Haruna zai miƙa bijimi na yin hadaya don zunubi saboda kansa. Zai yi kafara don kansa da gidansa. 7Zai kuma kawo bunsuran nan biyu a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada. 8Sa’an nan ya jefa kuri’a kan bunsuran nan biyu. Kuri’a ɗaya don Ubangiji, ɗaya kuma domin Azazel. 9A wanda kuri’ar Ubangiji ta faɗa a kansa, sai Haruna ya miƙa shi hadaya don zunubi ga Ubangiji. 10Amma a wanda kuri’ar Azazel ta faɗa a kansa, sai a miƙa shi da rai a gaban Ubangiji, a yi kafara da shi, a kora shi can cikin jeji domin Azazel.
11Haruna kuma zai miƙa bijimi na yin hadaya don zunubin kansa, ya yi kafara don kansa da gidansa. Zai yanka bijimi na yin hadaya don zunubin kansa. 12Zai ɗauki faranti cike da garwashin wuta daga bagaden da yake a gaban Ubangiji, ya kuma cika hannunsa biyu da turare mai ƙanshi, ya shigar da shi bayan labulen. 13Zai zuba turaren a wuta a gaban Ubangiji, domin hayaƙi ya tunnuke ya rufe murfi wanda yake a kan akwatin alkawari, don kada ya mutu. 14Sai ya ɗibi jinin bijimin, ya yayyafa da yatsansa a gefen gabas na murfin, zai kuma yayyafa jinin a gaban murfin sau bakwai.
15 Sai kuma ya yanka bunsuru na yin hadaya don zunubin jama’ar ya shigar da jinin bayan labulen. Zai sa jinin kamar yadda ya yi da jinin bijimin, ya yayyafa shi a kan murfin, da gaban murfin. 16Da haka zai yi kafara domin Wuri Mai Tsarki saboda ƙazantar mutanen Isra’ila, da laifofinsu, da dukan zunubansu. Haka kuma zai yi wa alfarwa ta sujada, wadda take a wurinsu, a tsakiyar ƙazantarsu. 17Kada kowa ya kasance cikin alfarwar sujada lokacin da Haruna ya shiga Wuri Mafi Tsarki domin ya yi kafara don kansa, da gidansa, da dukan taron jama’ar Isra’ila, sai lokacin da ya fita. 18Sa’an nan zai fita ya tafi wurin bagade wanda yake gaban Ubangiji don ya yi kafara dominsa. Zai ɗibi jinin bijimin da na bunsurun, ya shafa wa zankayen bagaden a kewaye. 19Zai kuma yayyafa jinin da yatsansa har sau bakwai a kan bagaden, ya tsabtace shi, ya tsarkake shi daga ƙazantar jama’ar Isra’ila.
20A sa’ad da ya gama yin kafara don Wuri Mai Tsarki, da alfarwa ta sujada, da bagaden, sai ya miƙa bunsuru ɗin mai rai. 21Haruna zai ɗibiya hannuwansa duka biyu a kan kan bunsurun mai rai, ya hurta muguntar Isra’ilawa duka a bisa bunsurun, da dukan laifofinsu, da dukan zunubansu. Zai ɗibiya su a kan kan bunsurun, ya kora shi cikin jeji ta hannun wanda aka shirya zai kora shi. 22Bunsurun zai ɗauki muguntarsu duka a kansa zuwa jeji. Mutumin kuwa zai sake shi can a jeji.
23 Sa’an nan Haruna zai shiga alfarwa ta sujada, ya tuɓe tufafinsa na lilin waɗanda ya sa sa’ad da ya shiga Wuri Mafi Tsarki, ya ajiye su a nan. 24Zai kuma yi wanka da ruwa a wuri mai tsarki, sa’an nan ya sa tufafinsa, ya je, ya miƙa hadayarsa ta ƙonawa, da hadaya ta ƙonawa don jama’a, domin ya yi kafara don kansa da jama’a. 25Zai ƙone kitsen hadaya don zunubi a bisa bagaden. 26Shi wanda ya kore bunsurun Azazel, sai ya wanke tufafinsa ya yi wanka da ruwa, bayan haka yana iya komawa cikin zango. 27 Bijimin da bunsurun da aka yi hadaya don zunubi da su, waɗanda aka yi kafara da jininsu a Wuri Mafi Tsarki, sai a kai su bayan zangon, a ƙone fatunsu, da namansu, da tarosonsu. 28Shi wanda ya ƙone su, zai wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, bayan haka ya iya komawa zangon.
29 Waɗannan za su zama farillai a gare su har abada. A rana ta goma ga watan bakwai za su ƙasƙantar da kansu, ba za su yi kowane irin aiki ba, ko ɗan ƙasa, ko baƙon da yake cikinsu. 30Gama a wannan rana za a yi kafara dominsu, domin a tsarkake su daga dukan zunubansu, su zama tsarkakakku a gaban Ubangiji. 31Wannan rana muhimmiya ce don hutawa a gare su. Za su ƙasƙantar da kansu, wannan farilla ce har abada. 32Firist kuma da aka naɗa ya zama firist a madadin mahaifinsa, zai yi kafara yana saye da tufafin lilin masu tsarki. 33Zai yi kafara domin Wuri Mai Tsarki, da alfarwa ta sujada, da bagaden. Sa’an nan kuma ya yi kafara domin firistocin, da dukan taron jama’ar. 34Wannan zai zama dawwamammiyar farilla a gare su. Za a riƙa yin kafara domin jama’ar Isra’ila saboda zunubansu duka sau ɗaya a shekara.
Sai Musa ya aikata kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.