Suratut 2:67-73 (Shanu)
Kuma a lõkacin da Musa yace ga mutanensa: “Lalle ne, Allah Yana umurtar ku da ku yanka wata sãniya.” Suka ce: “Shin kana riƙon mu ne da izgili?” Ya ce: “Ina nẽman tsari daga Allah da in kasance daga jãhilai.”
Suka ce: “Ka rõƙa mana Ubangijinka, Ya bayyana mana, mecẽ ce ita?” Ya ce: “Lalle ne, Shi, Yana cewa: “Lalle ne ita sãniya ce; bã tsõfuwa ba, bã kuma budurwa ba, tsakãtsaki ce a tsakãnin wancan,’ sai ku aikata abin da ake umurninku.”
Suka ce: “Ka rõƙa mana Ubangijinka Ya bayyana mana abin da yake launinta.” Ya ce: “Lalle ne, Shi Yana cewa: “Ita wata saniya ce fatsa-fatsa, mai tsan-tsan launi, tana faranta ran mausu kallonta.”
Suka ce: “Ka rõƙa mana Ubangijinka, Ya bayyana mana abin da yake ita, lalle ne shãnu suna yi mana kamã da jũna, kuma mu, idan Allah Yã so, haƙĩƙa, shiryuwa ne.”
Ya ce: “Lalle ne Shi, Yana cẽwa: “Ita wata sãniya ce; ba horarra bã tana noman ƙasa, kuma ba ta shayar da shuka, lãfiyayya ce: bãbu wani sõfane a cikinta.” Suka ce: “Yanzu kã zo da gaskiya. Sai suka yanka ta, kamar ba zã su aikata ba.
Kuma a lõkacin da kuka yi kisan kai, kuka dinga tunkuɗa wa jũna laifĩ a cikinsa, kuma Allah Mai fitar da abin da kuka kasance kuna ɓõyẽwa ne.
Sai Muka ce: “Ku dõke shi da wani sãshenta.” Kamar wancan ne Allah Yake rãyar da matattu, kuma Ya nũna muku ayõyinSa, tsammãninku kuna hankalta.