Skip to content

Yahaya 17

1Da Yesu ya faɗi haka, sai ya ɗaga kai sama ya ce, “Ya Uba, lokaci ya yi. Ka ɗaukaka Ɗanka domin Ɗan ya ɗaukaka ka, 2tun da ka ba shi iko a kan dukkan ‘yan adam, yă ba da rai madawwami ga duk waɗanda ka ba shi. 3Rai madawwami kuwa, shi ne su san ka, Allah Makaɗaici na gaskiya, da kuma Yesu Almasihu da ka aiko. 4Na ɗaukaka ka a duniya da yake na cika aikin da ka ba ni in yi. 5Yanzu kuma, ya Uba, ka ɗaukaka ni zuwa ga zatinka da ɗaukakan nan da nake da ita tare da kai tun kafin duniya ta kasance.
6“Na bayyana sunanka ga mutanen da ka ba ni daga cikin duniya. Dā ma naka ne, ka kuwa ba ni su, sun kuma kiyaye maganarka. 7Yanzu kuwa sun san duk iyakar abin da ka ba ni daga gare ka yake. 8Domin kuwa maganar da ka faɗa mini na faɗa musu, sun kuwa karɓa, sun kuma san hakika na fito daga wurinka ne, sun kuma gaskata kai ne ka aiko ni. 9Ni, roƙo nake yi dominsu. Ba duniya nake roƙa wa ba, sai dai su waɗanda ka ba ni, domin su naka ne. 10Dukkan nawa naka ne, duk naka kuma nawa ne, an kuma ɗaukaka ni a zukatansu. 11Yanzu kuma ba sauran zamana a duniya, amma waɗannan a duniya suke, ni kuwa ina zuwa wurinka. Ya Uba Mai tsarki, ka kiyaye su da ikon sunanka da ka ba ni, su zama ɗaya kamar yadda muke. 12 Duk sa’ad da nake tare da su, na kiyaye su da ikon sunanka da ka ba ni. Na kāre su, ba kuwa waninsu da ya halaka, sai dai halakakken nan, domin Nassi ya cika. 13Amma yanzu ina zuwa wurinka. Ina faɗar wannan magana tun ina duniya, domin farin cikina ya zama cikakke a zukatansu. 14Na faɗa musu maganarka, duniya kuwa ta ƙi su, domin su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne. 15Ba na roƙonka ka ɗauke su daga duniya, sai dai ka kāre su daga Mugun nan. 16Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne. 17Ka tsarkake su cikin gaskiya. Maganarka ita ce gaskiya. 18Kamar yadda ka aiko ni duniya, haka ni ma na aike su duniya. 19Saboda su ne nake miƙa kaina, domin su ma a tsarkake su cikin gaskiya.
20“Ba kuwa waɗannan kaɗai nake roƙa wa ba, har ma masu gaskatawa da ni ta maganarsu, 21domin dukansu su zama ɗaya, kamar yadda kai, ya Uba, kake cikina, ni kuma nake cikinka, haka su ma su kasance cikinmu, domin duniya ta gaskata, cewa kai ne ka aiko ni. 22Ɗaukakar da ka yi mini, ita na yi musu, domin su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya, 23ni a cikinsu, kai kuma a cikina, domin su zama ɗaya sosai, duniya ta gane kai ne ka aiko ni, ta kuma gane ka ƙaunace su kamar yadda ka kaunace ni. 24Ya Uba, ina so waɗanda ka ba ni, su ma su kasance tare da ni inda nake, su dubi ɗaukakata da ka yi mini, domin ka ƙaunace ni tun ba a halicci duniya ba. 25Ya Uba mai adalci, duniya kam, ba ta san ka ba, amma ni na san ka, waɗannan kuma sun sani kai ne ka aiko ni. 26Na sanar da su sunanka, zan kuma sana, domin ƙaunar da ka yi mini tă kasance cikinsu, ni ma in kasance a cikinsu.”